YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Camas! na tsaye a bakin gate din gidan Ahamdu suna fafatawa da masu Gadi! Magiya take musu suna sake botsarewa “Kinga Hajiya Wanzu Mai gidan ya fita kuma bai sanar damu zuwanki ba, a ‘ka’idar shiga wannan gida sai kana da shaida idan kina so mu barki ki shiga to ki nuna mana shaidarki.”
Daya daga cikin masu gadin ne yake wannan maganar.
“Ni bani da wata shaida da zan nuna muku amma nace ku shiga ku shaidawa matar gidan cewar ‘kawarta tazo Mai suna Hadiza ‘Yar Camas! nasan kuka sanar mata da cewa nice zata baku Umarnin kan ku bude min kofa na shiga.
Wanda yayi magana da farko shine ya sake magana da fadi’n ” Kinga Hajiya ita kanta matar gidan da kike magana a kanta bata da wannan power din Itama cikin tsaro take babu wanda ya isa ya bamu umarni mu bi idan ba mai gidan ba.”
Camas! ta saki murmushi tana girgiza kanta, jakarta dake rataye a kafadarta ta fito da ita ta zuge zif din kudi ta dauko daure cikin kyaure ta lissafa dubu ashirin ta mikawa mai maganar…..”Kar’ba na lura toshiyar hanci kake bukata babu damuwa idan kun kwantar da hankalinku ma yanzu zan fito.”
Shiru yayi yana kallon kudin hannunta, Sai ya juya yana kallon sauran ‘Yan uwanshi, Sundu’ki! ne ya d’aga masa gira alamun ya ‘karbi kudin….Sai ya sanya hannu ya karba da fad’in”To ki shiga amma minti ashirin kacal muka baki kiyi ki fito domin yallabai na iya dawowa da ko wane lokaci.” Camas! tace”To babu damuwa yanzu zan fito.”
Suka bude mata ‘karamar kofa ta shiga….Sundu’ki! ne ya tashi da kyar! dake irin mutanan ne masu masifar ki’bar tsiya shiyasa ma ake kiransa da suna Sundu’ki!!! Yace.”Dan tsaya anan.” Tsayawa tayi ya tafi tinkis tinkis yana duddubawa, Abdulmumini yake nema bai ganshi yaji dadin hakan yasan yaron munafiki ne zai iya fadawa Mai gidan abinda ke da akwai…..Ya dawo inda take tsaye yace muje na raka ki kofar da zata sadaki da cikin gidan….Tare suka jera ya nuna mata kofar daga can nesa godiya tayi ta ‘kara gaba da sauri…….Wani abu ta dinga matsawa a jikin kofar……Wasila na takure kujerar palon ta mike zumbur!! bakin kofar ta nufa, “Waye.”!? Tafada Camas! Tace” Yi sauri ki bude min Wasila.” Jin muryar Camas! ya sanya da sauri ta bude mata kofar!! Tana shigowa suka rungume juna Wasila ta fashe da kuka ta jata suka nufi cikin palon
Camas! sai bin ta take da kallo tana bin palon da kallo……..A cikin wannan daular Wasila take ita nacan tana yawon bid’id’i! da maza! Tab!!! ai kam ba zatayi yawo ita kadai ba duk yanda za tayi sai tayi ta turgud’e mata wannan auran sun taru sun zama d’aya. Shawarwarin da take tayi kenan da zuciyarta
A zahiri kuwa cewa tayi “Wasila ban ta’ba ganin yan iskan mutane ba kamar masu gadin gidanan shegu tsinannu zuwana uku sun hanani shigowa sai da na basu dubu ashirin tukkuna shima da sharadi kan minti ashirin kacal suka yarda nayi na fito…….” Rabu da ‘yan iska nima ranar sai na mari daya daga cikinsu ai ba laifinsu bane na ubangidansu ne babu babban mara mutunci irinsa.”
Camas! ta cire karamin gyalan dake jikinta tana kallon Wasilan tace”Wai dan Allah da gaske kike aure ne tsakanin ki da Ahamdu.”? Wasila tace.”Wannan wace irin magana ce Hadiza? ko zanyi miki karya ai ba zanyi miki irin wannan ba Yau tsayin kwanaki biyar kenan da daurin auren inda yaje jan garinmu aka dauro.”
Camas! tayi kwata’kes! itafa duk ta susuce! komai na gidan Ahamdu ya tafi da imaninta kai shi kanshi ma so take taji yanayin Jijiyarsa a jikinta sha’awarsa takeyi sosai da sosai.
“Tabdijam! amma mutumin nan ya karya miki alkadari sai da aski yazo gaban goshi sannan zai miki haka wallahi ki san yanda zakiyi ki fece! daga hannun wannan mugun mugunta zai miki Jiya da muka zauna metteng Governor yake cewa mutukar ya sake samun hawa kujerar mulki ke zai baiwa mukamin mai bashi shawarwari! saboda ya yaba da kokarin ki a wannan tafiyar shine dalilin da yasa ma nayi duk yanda zanyi na shigo gidanan domin in shaida miki abinda ke faruwa Governor da sauran ‘kososhin gomnati hankalinsu ya tashi da faruwan wannan al’mari sunce kuyi kokari ku kufce daga hannun Ahamdu ya aure ki ne ba kyakkyawar manufa ba, kuma kema ki zauna kiyi nazari da kyau ki gani sai da dadin yazo sannan zai miki wannan wulakancin ai wallahi ki nemi mafita tun kafin dare yayi miki.
Wata zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tace” Camas! na rasa yanda zanyi da mutumin nan Ahamdu! duk inda kike tubaninshi ya wuce nan wallahi! mugu ne! duk wata kafar mugunta da kika sani ya santa, tsakankanin kwanaki biyar din nan ni kadai nasan irin wuyar dana sha a hannunsa sau biyu yana sumar dani…….Har jinya na kwanta, yau ne kawai na dan samu sauki in kin lura zaki gani, babban tashin Hankalina Uwani da Rashida duk da nasan akwai kayan abinci a gidana babu wannan matsalar to amma nasan suna can hankalinsu a tashe saboda rashina.”
Camas! tace”Gaskiya kam hankalin Uwani ya tashi sau biyu muna zuwa gidanan dasu bamu samu damar shigowa ba to amma jiya naje can gidan naki na kwantar musu da hankali nace yau zanyi duk yanda zanyi na samu ganinki, A nan take shaida min cewar itama taje Can garinku Garko tayi wa mai allo wankin babban bargo sam! itama bata maraba da wannan auran naki.”
“Ai ki bari kawai Camas! babu babban wanda ya cuce ni irin mutumin nan ni nafi zargin kudi ya kuza masa shiyasa yayi min wannan wulakancin……Wai kamar ni budurwa a bani sadaki na dubu biyar wulakancin yayi tsanani.”
Camas! tasa dariya tana fadin”Ta’b! amma gaskiya tsohon nan bai da M Yo ko ni da nake a fanko ai ba zanyi arha irin taki ba, Wallahi naci alwashin sadakin aurena sisin gold ne da katuwar mota da katon gida……hahahaha kina nan kina ‘boye budurci an bada shi kan mafi karancin kudin hahahaha.”! Camas! ta dinga shaka mata dariya har da kwanciya.
‘Bata rai tayi tace”Kin ga Hadiza bana son iskanci da rashin mutunci! Ki bar dariya Budurcina nan yanda yake dubu biyar din sadaki nan a ajiye ai na fada masa da auran da babu duk daya suke a gurina kar ma yayi tunanin zai samu budurcina shi kuma mai allo duk sanda na kufce daga wannan gidan to ya kwana da shirin garin Garko sai anjimu dashi.”
Camas! tace”Da kyau! kawata yanzu wane mataki kike dauka na kubutar da kanki daga hannun Ahamadu Musa.”?
Yawo babu takalmi a cikin ruwa yakan jawowa mace babbar illah! ‘Yar uwa ki lura da kyau! Sanyi na saurin shiga ta kafafu ba zaki gane haka ba sai ranar da ya soma yi miki illah! ki tsare jikinki idan zakiyi aikin ruwa kina kokarin sanya silifas domin kare kanki da lafiyarki
Littafin na kud’i ne…..!
Kika futar min da book ke da Allah kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar.
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: ‘Yr Bngr Sys
29
”Kin san Allah Camas! na rasa wane mataki zan dauka na rasa wane tunani zanyi duk kaina ya kulle dana sa’ka wancan tunanin sai na warware yanzu ni ban san yanda zanyi na gudu daga gidanan ba, Ke da kanki kinga irin matakan tsaron daya zuba a gidanan da kyar suka barki kika shigo kuma ina jin sanda yake ce musu mutukar suka bari na fita daga gidan to a bakin aikinsu kuma sai ya dauresu…..Shiyasa jikina yayi sanyi na rasa wane mataki zan dauka a kanshi.
Camas! tace”Kina da kudi a accont dinki ko.”? “Sosai kuwa ni ban san ma a dadin su ba.” Shikkenan ai magana ta kare kud’inki zasu share miki hawaye…..Kin san abinda zamuyi yanzu.”? Girgiza kai tayi, Ki bani Atm d’nki a ciro kudi masu kauri muzo mu yaudari masu tsaron kofar gidan na lura suna da bala’in son kudin tsiya tunda dubu ashirin kacal na basu suka amince su cuci ubangidansu ina mai tabbatar miki da cewar kika basu dubu dari ko dari biyu zasu san yanda za’ayi bi futa daga cikin gidanan ba tare da kowa yaji ya gani ba sai yasu yasu.”