NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Muje Zuwa
BINTA UMAR ABBALE
[7/12, 8:39 AM] Bintu: ‘YAR BANGAR SIYASA!!
???? romantic love story????
NA:
BINTA UMAR ABBALE ????
????Manazarta Writes asso
‘Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi

 *NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300   Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176  sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

 *Free Pege5*
Yana tsaye a inda yake Garba ya shigo ya sanya masa ido har ya 'karaso inda yake tsaye.....Kai a 'kasa Garba yace."Sir tayi nisa da layi sosai amma fa ina zargin wani dan gane da wannan yarinyar." Ido ya sanya masa a nutse yace."Kamar name kenan." Garba ya 'kara risinar da kanshi a kasa yace."Anya kuwa ba turo ta akayi ba kuwa kasan fa mutanan babu abunda ba zasu iya ba."

Murmushi yayi yace."Garba idan ma turo ta sukayi tayi min sharri ko abu makancin wannan to insha Allahu ba zasu samu nasara ba ni nafi karfinsu tunda bana nufin su da sharri sai alkairi harkata ta siyasa kuma yanzu na fara babu gudu babu ja da baya ni dasu Allah ya bawa mai rabo sa'a."
Garba yace."Ka gama magana Yallabai Allah ya baka nasara kan dukanin abunda kasa a gaba." Ya amsa da "ameeen.'' Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza, Garba ya take masa baya.

Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Ma'aruf a can tsallake a fake.....ranta duk a bace ta karasa bakin motar.....'Dan kwankwasa jikin motar tayi Camas! da Alhaji Ma'aruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur! ya bude mata motar yana fad'in" Ya akayi *'Yar gaske* Allah yasa kin aiwatar da komai." Rai a 'bace tace" Wallahi ya'ki bada had'in kai d'an iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba."

Alhaji Ma'aruf yace."Kai! wannan d'an iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji sha'awarki ba? anya ma kuwa yana da lafiya? duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji sha'awa ta kamashi." Ya 'karashe maganar yana bin jikinta da kallo.

Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas! take kwance a kai! Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka she'ke! Allah ya kyauta.

Hijab dinta ta sanya tace"Alhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku.

Alhaji Ma'aruf ya kunna motarshi yana goge gumi yace."Maganar ki gaskiya ce *'Yar gaske*  shiyasa muke 'kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin."

Suna tafiya suna zan can Ahamad dashi da taurinka kansa Alhaji Ma'aruf na fada musu yanda suke dauki ba dad'i a kan suga bayanshi amma abun yaci tura yace shi har jinin kad'angare ya sha duk saboda yaga bayan Ahamd amma asirin bai kar'beshi ba a lokacin ma so yayi ya dawo kansa sai da bokan da ya kulla asirin ya warware tukkuna ya samu lafiya.

Wasila tace"Ka rabu dashi Alhaji duk ku daina wahalar da kanku da kudinku da yawon bin malamai a kanshi sharrina ma kad'ai ya isheshi sai nayi fata-fata da rayuwarshi."

Alhaji Ma'aruf yaji dadi maganar ta yace.''Mu kuma munyi miki alkawarin baki dadin duniya *Yar gaske* zaki fantama sosai da kudi sai dai ki bawa wasu."

Da jin wannan magana tashi sai Wasila ta sake daukar aniyar babu gudu babu ja da baya a kan Ahmadu Musa *(Ba iyak ka)* har sai taga abunda ya turewa buzu nadi.


'Karfe goma sha biyu saura na dare ya ajiyesu a kofar gidansu Ledoji cike da kayan dadi ya bawa Wasila rafar kudi ta dubu dari camas ya bata dubu hamsin sukayi sallama da juna kan cewar zasu fito da wurwuri domi zuwa yawon kamfen........


'Yar 'kofar da suke karawa Wasila ta tura firgigit Uwani ta mike zaune dama ba baccin take ba tana zaune tana  dakon dawowar 'yar tata.

Wasila ta mayar da 'kofar ta kare gidan kana ta saki buhun dake sakale suka shiga cikin gidan suna ihu! kamar ba dare ba.

Uwani da Rashida suka fito a guje! Wasila ta farke rafar kudin dake hannunta ta soma mannawa Uwani a saman goshi.....Uwani na ganin Sabbin 'yan dubu-dubu na watsi a a tsakar gida sai ta fasa ihu! ta rungume! 'yar tata suka kama rawa wata lafiyayyar gud'a ta dinga rangadawa tana sakarwa 'yar tata kirari......Ita kuwa Rashida kudin take bi tana tsince tana ta faman kyalkyala Dariya sai kace mahaukaciya.


Sai da suka gama murnarsu sannan suka dauki ledojinsu suka shige ru'babbiyar rumfarsu da ta kusa ruftawa Rasida ta samo katon faranti suka baje wasu 'kosassan kaji guda shida wanda komai zulamar mutum bai iya cinye guda saboda girmansu ga had'ddaun lemuka masu sanyi nan suka baje suka dinga yagar kaza suna yi mata cin ala tsine uwar me karya, wai! yaushe rabon duniya da ayya raye."!! Uwani ta fada tana shigowa dakin bayan taje ta wanko hannunta........Wasila tace"Yanzu dai mu kwanta muyi bacci dare yayi sai gobe in yaso sai kuji labarin abunda yake faruwa.

Uwani tace"Ki d'an gutsira min wani abu mana na kwana dasu a karkashin filona anya ma kuwa yau zan iya bacci oh! duniya kenan."

Wasila tace"Uwani kwanta kiyi bacci harda munsharri ai insha Allahu mu da talauci munyi hannun riga."  Uwani ta dinga wata mahaukaciyar dariya tana fad'in"Ai dama ni nasan jari na haifa ke ba 'karamar mace bace idan ba'aso ki dan komai ba a so ki dan 'kirar jikinki ita kuma Rashida wannan farar fatar tata itace jarina."

Wasila tace"Uwani nifa ba karuwanci naje nayi ba sana'a muka fita mukayi ko ba haka ba Camas!." Tafada tana kallon Camas! dake irga kudinta.

Camas tace"Kwarai kuwa sana'ar mukaje mukayi ta siyasa gobe zamu fita da wurwuri shiyasa ma ban wuce gida ba."

Uwani tace"Kai amma wannan sana'a ta karbeku wallahi Allah ya bada sa'a ya taimake ku."

Suka amsa da "ameen." Sannan ko wacce ta gyara shimfida ta yada ha'karkari ta kwanta ana jira kuma gari ya waye a fita *Sana'a*







_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/13, 1:07 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
   ???? romantic love story????
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE ????*
*????Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE…….!
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za’a tura kudin.0542382124…….Binta Umar gtbank….Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din….07084653262_08089965176 sai na fad’i yanda za’a biya kud’in…..Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars…….90899076_88137740 katin airtal ko orange

Free Pege6
Da safe suka tashi da wurwuri sukayi wanka tsaf suka shirya tuni Uwani ta ta fasa musu shayi Rashida ta siyo su madara da milo da bread har da su kwai Uwani ta soya musu yau karin kullamo sukayi rigijib suka karasa cinye sauran kajinsu na jiya….Wasila ta kalli Camas! dake gyara daurin dankwali tace”Ya kamata kije gida mamanku ta ganki kafin mu tafi ko.” Camas! tace”Ke kin san idan na shiga gida yanzu babanmu nanan ba zai bari na sake fita ba kawai ki kyalesu idan na dawo ma had’u.”

Tace”Shikkenan ke Rashida zan bada dubu talatin ayi aikin gidanan a sanya kokafi data waje data bandaki saboda bana so in doso layin nan wallahi in hango ku kamar tumaki a akurki wai sunan kuna cikin gida a zaune amma jama’ar dake waje na ganinku wannan gidan ai sunansa kango ba gida ba.

Uwani tace”Naji kinyi maganar dubu talatin duk a aikin gidan anya kuwa basuyi yawa ba.” Tace”Na fiso ayi komai da inganci a sa kofofi masu kyau insha Allah yau ma idan mun fita zamu samo kudi.’ Uwani tace”To Allah yasa.” Wasila ta irga dubu talatin da biyar ta bawasu Uwani talatin na gyaran gida biyar kuma tace su dan auno kwanan shinkafa suyi cefane kafin ta dawo…….Haka sukayi musu sallama suka kama hanya suka tafi can guest house din Alhaji Ma’aruf dake a can yace su had’u.

Suna shiga harabar gurin suka wasu gugun matasa rukuni rukuni! amma ‘yan daba da shaye-shaye sunfi yawa…..Alhaji Ma’aruf da wani mutumi suna tsaye a kansu suna magana dasu.

Kai tsaye can suka nufa Alhaji Ma’aruf na ganinsu ya washe baki ya kalli Alhaji Tasi’u “Yawwa kaga ‘yan halak! ko yanzu yanzu mu ka gama zancensu ashe suna tafe.

Wasila tace” Aikuwa dai muna hanya wallahi kun san matsalar abun hawa sai a hankali.” Alhaji Tasi’u ya kalli abokinsa yana nuna Wasila da bakinsa yace”Ko baka fada mun ba na gane wannan ce Wasila ‘Yar gaske!” Yace.”Kwarai kuwa Alhaji kayi mamakin ganinta ‘yar karama ko.” Yace.”Dai-dai kenan duk da kankantar ta nasan zata bamu gudumawar da muke bukata daga gareta Wasila naji kina maganar abun hawa da sauransu ki kwantar da hankalinki zan siya miki mota ta kece raini ke dai kawai ki bamu goyon baya domin zamuyi amfani dake domin cimma manufarmu.”

A dake! tace”Kar ka damu Alhaji a shirye nake wallahi domin harkar na shigo gadan gadan duk inda nasan zan samu nan zan nufa in zaku sakar min kudi magana ta ‘kare.”

Alhaji Ma’aruf da Alhaji Tasi’u suka fashe da dariya suna tafawa, Sai bayan sun tsaigata da dariyar ne Alhaji Tasi’u yace.”Kunga wad’ancan mutanan dake zazzaune ko.”? Suka ce.”Eh.” yace.”To zaku fita dasu yawon kamfen saboda mun samu labarin Ahamadu (Ba iya ka) zai fita zagaye gari domin yad’a munufarsa a kan talakawa to muna so duk inda suka shiga suna yad’a manufarsu su shi ku soke! ku watsa jama’a akwai kayan aiki a tare dasu Lauje karkuji komai kuyi aiki sosai mune muke da mulki a hannunmu babu wani abu da zai same ku.”

Wasila tace”Kar ka damu alhaji nayi maka al’kawari bakin rai bakin fama.” Alhaji Ma’aruf ya kalli Camas yana lumshe mata ido yace.”Kefa baki ce komai ba.”

Tace”Haba karfa ku damu nima na dauki alkawari insha Allah sai mun rusa shirin Ba iya ka.”

Alhaji Tasiu ya nunawa matasan nan su Wasila yace sune abokanan tafiyarsu su kula dasu a matsayinsu na mata, har bakin mota suka rakasu suka shishhiga a’kalla sai da suka cika motaci hud’u irin na haya saboda yawansu sun kai su ashirin da wani abun….Kai tsaye suka dauki titin da zai futar da mutun cikin gari.

Cikin shadda fara kal ya fito yana daura agogon silvar a hannunshi hularshi ya kar’ba daga hannun Garba ya d’ora a kanshi Ba kano zallah yayi kyau har ya gaji ya zaune gefan gujera yana sanya safa Garba ya gama goge masa takalminsa sawu ciki ya mika masa ya sanya a kafafunsa yana mikewa Khalifa babban amininsa ya shigo shima yana sanya da manyan kaya shi harda babbar riga cikin kamala da mutumta juna suka gaisa kai kana ganin mu’amularsu zaka gane masu ilimi ne suna kuma aiki dashi……..suna fita harabar gidan suka tadda matasa sun kai su goma duk suna jiran fitowarsa….Aikuwa ya dinga amsa gaisuwarsu yana daga musu hannu su kuma sun rud’e da fad’in” Sai kayi Ko garin ba kowa mu muna tare da kai kane za’bin talakawa, Kano sai Dan Musa.”
Ahamad ya d’aga dukanin hannuwasa biyu sama da ‘karfi yace.” CPC.”! Suka amsa da “Sa’a!!!” Yace.”Sa’a ta mai rabo ce.” Sukace “Kaine kake da Sa’a mai Sa’a.” Ya saki murmushi da fad’in “Allah ya bawa mai rabo Sa’a.” Suka amsa da “ameeen.”!!!” Da sauri Garba ya bude masa bayan wata had’addiyar mota ya shiga Khalifa yabi bayanshi Garba da Dan uwanshi Hadi suka shiga sai direba ya shiga mazauninsa…..Kafin kice kwabo kin nemi jama’ar gurin nan kin rasa duk sun shisshige motocin dake fake a gurin domin su raka dan takararsu yad’a munufarshi…..Kai tsaye titin da zai sadaka da wata unguwa a cikin gari suka nufa mai suna Jakara nan yake so ya fara zuwa saboda yanda yake jin labarin unguwar babu kyau ga ta’bar’barewar al’amura da yawa tarbiyar yara matasa ta lalace babu sana’ar yi sai jagaliya da harkar gwan-gwan da sauransu yana so ya fara zuwa unguwar ya yad’a munfarashi kafin ya shiga sauran unguwanni.

A kan idonsu motocinsu suka dinga parking, dake duk rabin unguwar Jakara kasuwa ce kafin kice kwabo guri ya hargitse da kaya-kaya jin cewar ga d’an takarar gwamna nan yazo yad’a munufarshi masoya Ahamdu Musa Ba Iya ka suka dinga turereniya domin suje su daga masa hannu…..Matasan nan suka fito da tarin pastocinsa suka fara aikin mannawa a bango da shagunan mutane gefan titi suka dinga bi suna mannawa guri ya cika ma’kil! Khalifa ya bude masa samar mota ya fito da jikinsa ya daga hannuwansa biyu yana fad’in” CPC.”! Sai gurin ya rud’e! da fad’in” Sa’a!!!!! Su Wasila suka keto gurin da motocinsu a guje!!!! A take mutane suka watse kowa na ceton ransa…..Parking din motocin sukayi suka fito a fusace! ko wanne da makami a hannunsa…..A sai guri ya hargitse ihu!! kawai kakaji da gudu radadada!!!!!

Hankalin Ahamad ya tashi sosai gashi Police guda biyu kacal ya dauka kuma suma al’amarin yafi ‘karfinsu domin ‘yan daban gidan gwamnati suna da muggan makamai!! Ya ware murya sosai yana fad’in”Kowa yayi takansa ya tsira da rashi.”!!!! Wani Dan daba ya ‘bullo daga wata hanya dake da maraba da wata katuwar kwata hannunsa rike da wata shar’be’biyar addah! sai kartar ta yake a ‘kas! yana sakin wani uban ihu! da fad’in” Sai kayi ko garin ba kowa.” Eh! yane! mu za’a kawo wa raini a unguwar tamu! ashe yau sai an zubar da jini wallah!!!! Huhhhhhh! ya kurma wani uban ihu! yayi kan ‘Yan daban Gidan gwamnati yana sararsu ta ko’ina!!!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button