YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Ta fito hannunta rike da wani madai-daicib tire da goran ruwa da lemo a kai sai kananun cups ta ajiye kan teble din tana fadin ga ruwa sannuku.” Khalifa yace.”Yawwa sannu amaryamu.” Murmushi tayi kawai ta kama hannun Afnan suka nufi dakinta, ba tajin zata zauna in dai yana gurin a zaune……….Khalifa yace.”A’a ya zaki gudu kuma.” Karaf! yace.”Kunya takeji wai ita amarya.” Hafsa tasa dariya tace”Ai kunya halal ce! a gurin ‘ya mace gaskiya mungode da tar’bar da akayi mana amarya.” Ba tace komai ba ta bar suna ta surutu….Tana jin sanda yake fad’in”Ita wannan amarya bata da wata kunya dan ta ganku ne take sunkuyar da kai.” Hafsa kuwa sai tare mata takeyi tana fadin “Sam! ba haka bane.”
Afnan ta hau kan bed dinta tana tayi mata surutu da labarin skull dinsu ita dai jinta kawai takeyi, ta rasa wane tunani zatayi da ta sa’ka wancan sai ta kwance sam! wannan gidan ba gidan zama ba hankalinta har yanzu na kan harkokin siyarsar ta, taga sai wani gayyato mata mutane yake sai kace wata wacce tazo zama.”
Sun jima suna hira dan sai da suka dauki kusan awa biyu tukkuna sannan suka niyar tafiya, har lokacin Afnan na tare da Wasila suna hira dan tun tana biye mata da surutun ta har tayi mata shiru itama ta gaji ta kwanta bacci ya dauketa….Ya shigo dakin ya same su kwance kan bed a tare ita Afnan din baccinta yayi nisa sosai itace dai take ta kokarin gayyato baccin yazo yaki zuwa.
Mikewa tayi zaune tana daura dankwalinta, ya tsaya kusa da ita a nutse yace.”Yarinyar nan fa tun bata sanki ba, take zumudin ganinki gashi ta makale miki ya za’ayi ne momynta tace zata kwana biyu a gurinki kina ganin babu matsala ko.”?
Yafad’i wannan maganar ne saboda kawai baya son shiga hakkinta idan taga zata iya daukar yarinyar shi bai da matsala,
Jim! tayi itafa bata so ta sha’ku da kowa ballanta hakan yazo ya dameta wane irin zama za tayi a gidan! da har za’a na’nika mata yarinya,
Domin kar ta watsa wa maman yarinyar kasa a ido yasa tace.”Ni meye nawa a ciki gidanka ne fa, tayi zamanta.” Yace.”Eh ai nasan gidana ne ai kece matar gidan dole kina da hakki akai.’
Shiru tayi masa, yace.”alamu sun nuna kin amince kenan? Kallonsa tayi ya d’aga mata girarshi guda tayi saurin dauke kanta gabanta na faduwa, yace.”Ki fito zasu tafi sai kuyi sallama ko.”
Mikewa tayi, ya juya baya yana tafiya kallonshi kawai takeyi sai wani magana yake mata yana dage mata gira kamar wani dan saurayi mutum da girmanshi da komai sai iyayin tsiya,
Su Khalifa na tsaye suna jiran fitowarsu, dukaninsu basuyi tsammanin Afnan zata zauna ba sai suka gansu sun fito babu ita, cike da mamaki! Hafsa tace”Ina Afnan din.”? Ahamdu yace.”Ina ruwanki da ita kuma yanzu.” Rike baki tayi tace”Nifa duk wannan abin da nakeyi wallahi cikin wasa nakeyi ko kayanta daka gani saboda kar tayi min kuka ne yasa na had’o mata muzo dasu, amma ni nasan rigimar Afnan ba zata barku kusha ruwa ba a gidanan.”
Khalifa yace.”To nima dai haka nake gani amma dai shikkenan.” Wasila tace”Kai don Allah ku kyaleta mana ai babu wata matsala bacci ma takeyi ai ni nasan ba zatayi kuka ba.”
Khalifa yace.”Shikkenan ai dama bamu ce komai ba.” Murmushi kawai tayi tace”To ku gaida gida mungode.’ Hafsa tace”amarya yaushe zaki kawo min ziyara ne.”? Dan murmushi tayi takasa magana sai shine yace.”Idan ta kwana biyu zan kawo miki ita amma bana son gulma.” Hafsa tace”Kasan kuwa idan mun hadu sai munyi gulmarku.” Yace.”To na fasa kawo ta tunda d’abia mara amfani zakuyi.” Hafsa ta dinga dariya tana fadin”saboda rashin gaskiya ba, ai da kafarta nasan zata zo inda nake mu kashe mu binne.”
Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba, suka nufi kofar fita a tare, Wasila tana tsaye daga inda take tana musu fatan alkairi da sauka lafiya.
Sai da ya tabbatar motarsu ta fita daga gidan sannan ya koma cikin….Parlo yay zamansa yana kallo da tunanin yanda zai kai kansa gurin yarinar da daddare baya jin zai iya daga mata kafa a yau din nan.
Camas! kuwa lokacin da ta bar gidan Wasila kai tsaye gidanta dake tishama ta nufa, lokacin su Uwani da rashida abin duniya ya damesu sun tasa lafiyayyan abinci a gaba sun kasa ci sai tunini suke, Da jin labarin da Camas tazo musu dashi sai hankalinsu ya kwanta, jin cewar Wasilan na cikin koshin lafiya gashi har ta bada sallahun a fada musu cewar tanan kalau kuma su kwantar da hankalinsu tanan fitowa ta cigaba da rayuwa a tare dasu, Uwani ce kawai taji dadin wannan magana amma ita Rashida sam bata sha’awar wasila ta fito daga gidan Ahamdu tana ganin Allah ya gama yi mata suttura tunda ya gamata da miji nagari kamar wannan bawan Allahn.
Camas! bayan ta bar gidan su Uwani sai ta wuce can getshouse din As wato Alhaji Tasi’u lokacin yana tare da baki sai da tayi jira tukkuna ta shiga…..Yana ganinta yace.”Tuntuni nake saka ran zuwanki shiru da yanzu nake tunanin kiranki a waya.
Tace.”Wallahi kuwa ai ina tafe na dan tsaya wani guri ne.” As yace.”Okey bani labarin yanda kukayi kin samu ganin Wasila…..Tace.”Kwarai kuwa har mun shirya shawarar yanda za’ayi.” Tiryan tiryan! ta fada masa yanda sukayi da Wasila da irin alkawarin da tayi kan in ta fito daga gidan Ahamdu to ya saka ransa cewar ta zama mallakinsa.
As ya dinga washe baki yana shafa sumar kanshi tabbas idan hakane to ko nawa ne zai iya kashewa duk dan ta samu nasarar fitowa daga wannan gidan….Yace.”Yanzu abinda za’ayi shine ki bani accont numbar naki zan miki sending din kudi masu dan kwari, wanda zasu isa kuyi abinda zakuyi dasu, gaskiya naji dadin wannan labari naki dole ne ma nayi miki alkairi.”
Camas! dadi ya isheta tasan As bashi da kwauro mutum ne shi mai sauki da dogon hannu har yaso yafi governor mi’kawa, itana wasilan duk da bazarsa take rawa, ta bashi account numbar dinta a take ya tura mata dubu dari hudu yace nata duba dari dubu dari uku kuma taje tabawa masu gadin gidan Ahamdu idan sunki amincewa ta dawo zai kara wasu.
Godiya tayi sosai sukayi sallama da juna, tare da sharadin gobe zata fara aiwatar da aikinta…
Tun yamma Hadari ke had’owa daf da magariba gari ya turnuke sosai da kura iska na tashi da ledoji…..Dai-dai wannan lokaci Afnan ta tashi daga baccin da ya dauketa tun bayan tafiyar iyayenta, Wasila da ta fito daga toilet ta ganta zaune a kan bed tana mutsika ido, tace.”Afnan kin tashi.” Yarinyar ta kalleta tana gyada kai…Tace.”Kin sha bacci ko abinci baki ci ba tashi muje na rakaki kiyi brush baccin yamma bashi dadi ko kadan.” Afnan ta sauko daga bed din suka nufi toilet Wasila ta matsa mata man goge baki a sabon brush, ta karba tana fadin”Aunty Amarya ina momyna da Abbahna.”? Kai tsaye tace”Ai sun tafi tun dazu ke kina ta bacci.” ‘Dif! yarinyar tayi tana goge baki har ta gama wasila tace”To daura alwala muyi sallah sai kici abinci ko.”? Daga mata kai tayi, Wasila ta kalli fuskarta taga babu walwala sam! bata kawo komai ba, ta mika mata, mayafin abaya ta yafa kana tasa hijab suka tada sallah…….Sanye da jallabiya ruwan toka ya shigo kanshi sanye da hular labarawa fara tas da ita ya saje sak da balaraban saudia….Ganinsu suna sallah sai ya zauna kan Sofa yana cigaba da jar carbin dake hannunsa…..Suna idarwa, Afnan tace”Dadyna! ina Abbahna.” ? Ya kalleta da sauri yace.”Ke! haka ake daga idar da sallahr babu addua sai magana.” Rakykyakya’be fuska tayi sai hawaye shaaaa! ya bude baki cike da mamaki yana kallonta, hannu ya mika mata “Zo nan.! Taje ta tsaya tana goge fuska da bayan hannunta, Yace.” Me akayi miki kike kuka.”? Shiru tayi……”Ko auny Amarya ce ta dake ki.”? Wasila tayi saurin kallonshi jin abinda yace….Afnan ta girgiza kanta…”Ni dai a kaini gidaaaaa.”! Yarinyar tafada muryarta narawa still hawaye na zuba….Yace.”Ai kinyi kad’an yarinya ba zaki bani wahala ba wallahi sai kinyi iya adadin kwanakin da kikace zakiyi sannan zai mai dake.” Tsalle ta buga, ta hau kurma ihu! “Wayyo!! Abbana Momyna! ni gida zani ba zan zauna ba a kaini gidaa!!!! Hannunsa yasa ya toshe kunnansa, Afnan akwai lafiyar karadi sai kara take musu a kunne.