YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Bacci sukayi mai dadi ita dashi baccin da suka dade basuyi irin shi ba mussaman ita uwar gayyar da asuba da ‘kyar ya cireta daga jikinsa duk ta nannade shi fuskata dai-dai tashi numfashinsu na bugun juna….Rufe mata jiki yayi ya sauke daga bed din ya nufi toilet, wanda ya soma yi kana ya daura alwala ya fito….Dai-dai lokacin ta bude idonta ta ganshi yana goge jikinsa da karamin towel, a gurguje taga yana shiryawa har ya kammala ya juyo idonta tayi saurin rufewa, har sai da ta ya fita daga dakin, kana ta daddafa ta mike zaune, blanket din ta dan janye daga jikinta taganta sintir girgiza kanta kawai tayi, ta fara kokarin sauka hannunta ta dora kan wayarshi, tayi saurin dauka tana dubawa, ajiyar zuciya ta sauke a hankali ga dama ta samu, sai da kuma bata san meye security na wayar ba, Sunanshi ta rubuta da babban baki, ta’ki budewa, sai ta gwada rubuta sunan nashi da karamin ba’ki sai kuwa ta bud’e! Murmushi ta saki tana fadin”Alhmadullhi.” Numbar camas tasa da sauri ta fara kiranta….Camas nacan duniyar bacci taji shigowar kira cikin baccinta dake dama bata kashe wayarta sabida yanayin sana’arta wani dan iskan ma da asubah zai kiranta kuma taje…..Muryar Wasila ta daki dodon kunanta ta mike da sauri tana fadin”Wasila lafiya da asubah haka.”?
“Camas! ya fita sallah ne na samu na dauki wayarshi , wai shin ya akw cikine? guy nan fa naga da gaske yake wallahi, jiya sai da ya rabani da mutuncinta sannan sai wani karyar da wuya yake wai dole na zauna dashi yana so na da sauransu…..Kai tsaye Camas! tace” Wallahi kada ki yarda dashi yaudarace kawai yana so ki zauna ki cigaba da bashi dadi ne ya samu kankanuwar yarinya ai kawai kiyi takanki yana gama morarki zai sake ki.
“Ke har sai kin bani shawara ma! a she kin manta ra’ayina, ko nasha fada cewa ni ba zan auri mai shekaru ba yaro karami zan aura domin mu mori kuruciyarmu tare namijin da ya kwana biyu sai a hankali a lokacin da kake da kuruciya shi kuma a lokacin zai tsufa ya kasa biya maka bukatarka, wannan dalilin ne ya sanya naji sam bana sha’awar auranshi…..Camas! tace” Ato gwara dai kiyi da gaske dama yau nake cewa zanzo gidan naki jiya As ya bada kudi zan shigo muyi yanda zamuyi.” Tace”Shikkenan misalin karfe nawa zaki shigo.” ? Gaskiya da wuri zan shigo dan yau ma zamu zauna da governor wajejen goma da rabi ki saurari zuwa.” Wasila taji kamar tabi Camas! gidan gomnati, tace”Shikkenn sai kinzo din.” numbar Rashida ta kira a kashe ta Uwani ma a kashe, har tayi niyyar kiran As sai kuma ta fasa tana jin tsoron kar tana tsaka da kiranshi ya shigo ko kuma ya gane alama….Duk sai da ta goge numbobin mutanan da ta kira ta ajiye masa wayarsa.
Kafin tayi wanka sai da ta dade cikin ruwan zafi, kana tayi wanka da alwala ta fito daure da guntin towel…..Gashin kanta take kokarin busarwa ya shigo dakin…..Kai tsaye bed ya nufa ya kwanta rigingine yana kallonta har ta gama busar da gashin ta gyarashi tas ta daure shi cikin katon ribbon……Riga da wando ta dauko masu dan kauri tasa a jikinta ta daura dankwalin abaya kana ta hau kan dadduma ta tada sallah.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya dauke idonshi da kanta, yaji dadi sosai da ya dawo ya tadda ta tashi cikin kuzari da lafiya kuma ya lura jikin nata ya dan sake tinda ta daina cije bakinta da tafiya da kyar.
Tese message ne ya shigo wayarshi, ya mika hannu ya dauka yana dubawa, sabuwar numbar ce, ya bude yana dubawa
Kai Wawa! kayi gaggawar sakin wannan yarinyar da ka aura domin ba tsaranka bace idan ka’ki kuma wallahi rayuwarka na cikin had’ari
Daya message din ya bude yana karantawa cikin mamaki………
Za kayi tunanin ko daga abokanan hamayyar ka ne to ko daya kar kayi tunanin haka, mu daban muke kuma muna bibiyar lamarin wannan yarinyar dake tare da kai! saboda haka kwanciyar hankalin ka shine ka saketa idan ba haka ba to sai mun kashe kaaaa!
Zufa ce ta shiga ketowa daga ko wace kusurwa dake jikinsa test messages din yake maimaitawa yana mamaki har ta karaso inda yake bai sani ba, sai maganarta da yaji a tsakiyar kanshi…..”Ya muke ciki da kai? Ya dago kansa yana kallonta cikin tsananin mamaki! ta tsaya kanshi tana masa magana ga tsal ga tsal!!
D’an bata fuska yayi yace.”Wannan wane irin abu ne? ba tarbiya ce bace wannan babu gaisuwa kin tsaya min aka kina min magana babu d’a’a.”
‘Kasa tayi da kanta ganin kamar ranshi ya ‘baci! Wayar hannunsa ya mika mata yace.”Ko ina da masaniya kan wannan test din.” Ta kar’bi wayar tana dubawa…..D’an ta’be bakinta tayi ta mika masa wayar ba tare da tace komai ba…..Yace.”Kinyi shuru ko kin san masu numbar ne? ki fada min nayi wa tufkar hanci al’amarin ba ni kadai zai shafa har dake.”
Tura baki tayi tace”Ni ban san komai ba.” Ya mai da kanshi fuskar wayar yana sake duba test din….Kimanin minti biyar ya dago kansa yana kallonta, tana nan tsaye inda take, yace.”Koma dai su waye to kice musu basu isa su sanya ni na rabu dake ba komai sharrin su, zasuyi su bari, Ahamdu yanzu ya soma auran Wasila babu gudu babu ja da baya idan kuma mutum ya cika shi d’an iska ne to ya bayyana kanshi.” Yana gama maganarshi ya mike ya fita…..Zama tayi gefan bed tana nazari, ko dai Camas ce ta soma aikinta? babu shakka itace to ko dai As ne yasa sabuwar numbar don ya tsorata Ahamdu din to ko ma dai waye hakan yayi mata dadi gwara a tsoratar dashi, yaji baya bukatar zama da ita.
Yana fita ya nufi bakin gate, duk suna xazzaune suna ganinshi suka mike da sauri gaishe shi suke yana amsawa kafin ya mai da hankalinsa kansu, dik sun nutsu suna sauraransa, Yace.”Ina so ku sake sanya ido sosai a cikin gidan nan nasan dani daku amana ce ta hadamu to ku rike min amanata ku kula da akinku, zan sanya Cctv cemara a gidan nan saboda wani dalili ba wai dan kun gaza ba ko wani abu daban! No! ina da dalilina nayin hakan, walau mace ko namiji ban yarda ya shigo gidan nan ba sai kun shaida min a waya na tabbatar muku da ku barshi ya shiga, ina fatan kun fahinta.” Suka amsa da insha Allah zamu kula sosai Yallabai.” Sallama yayi musu ya koma cikin gidan.
Yana shiga parlor Rabe ba shirya daining kai tsaye daning din ya nufa, Rabe ya mika gaisuwar sa ya amsa a sake kana yace.”Ya hada mishi tea, da sauri Rabe ya sha masa tea mai kauri amma bai sanya masa sugar sosai ba kwara biyu kacal yasa saboda yasan ogan nashi baya son zaki da yawa, soyayyar doya da kwai ya zuba mishi a plete zai shafe biredi da buttur ya hanashi alamun baya son buttar din ya dauki cup din tea din yana kurba kadan kadan……..break fast dinshi yayi hankalinsa kwance sam! bai wani daga hankalinsa kan mutanan da sukayi mishi test messages ba yasan duk karya ne wai shi zasuyi wa barazana wannan messages din nada nasaba da government house zasu ninke shi baibai ne kuma ya tabbatar da cewar ita wasilan tasan duk abinda yake faruwa yana ganin ma kamar da hadin bakinta……yanzu ne ma yake jin wani karfin gwiwar xama da yarinyar tunda ya lura tana da rana a gurinsu.
Ta dauka zata ganshi a zaune ya zabga tagumi ko taga damuwa a tare dashi, sai taga cup din tea a hannunsa yana kur’ba da latsa wayarshi ga fuskarsa a sake kamar ma murmushi yake yi aikuwa dai murmushin yake yi, dan message Khalifa ya turo masa yana masa bangajiyar dukan ruwa, sannan wai Afnan tana gaishe su, kana kuma tace abawa amarya hakuri! Shine fa abin ya bashi dariya yake murmusawa, Jin motsin fitowarta yasa ya dago kanshi…Tayi saurin kauda nata kan kamar munafuka tayi nufin koma wa dakin….”Ki zo ga sa’ko Afnan tace a baki.” Yafada still da mirmushi a fuskarsa, ta dan juyo tana kallonshi, girarsa guda ya daga mata (sigina) yana sakar mata mirmushi…Ta tsani wannan halin da yake mata shi ba yaro ba ya dinga abun yara….da kamar kar ta je sai kuma ta nufe shi, tana tsayuwa kanshi ya jawo ta ya zaunar kan ciyarshi, wayar ya mika mata yace.”Khalifa ne ke baki hakuri tare da Afnan.”! Ta dan ya mutsa fuska tana duba message din…. ya mayar da hankalinshi wuyanta yana bala’in son gashi a rayuwarsa, zame dankwalin kanta yayi ya tusa hannunsa cikin gashin ribbon din ya cire gashin ya zubo a fuskarshi, sansanawa yake yi yana sauke ajiyar zuciya, da sauri! ya cire hannuwansa daga ‘Kungunta ya d’ara kan brest din ta yana……….