NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book! keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE

Littafin na kudi ne…….!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! WhatsApp numbar
07084653262alliya:
‘Yr Bngr Sys
48
Shashshekar kukunta ne ya dameshi yana draving yana jan tsaki ya rasa ma wane irin mataki zai dauka kanta, domin tayi mutukar bashi mamaki! sam! bai ta’ba tsammanin za’a iya had’a baki da ita a cutar dashi ba, ashe dama ita da akwai abinda take shiryawa shiyasa tun jiya yaga ta saki jikinta tana ta zumud’i, to wai idan ta bi As din ina zai kaita? shi da kansa yake tambayar kanshi da kanshi, tabbas yarinyar ba ‘karamar mara hankali bace wato ita tafi so tayi ta yawo a gari tana shiga cikin maza tana cakuduwa dasu! da auransa a kanta zata bi As suje inaaaa? Sitiyarin motar ya daka da karfi har sai da ya kufce daga hannunshi motar tayi wani irin abu!! Jikinta na bala’in rawa tace”Kay….hakuri dan Allah.”! Ko kallonta bai ba ya kunna motar a guje yake janta yanayi kamar ma yace ta fice masa daga mota saboda tsabar haushi da takaici…….Lokacin da suka isa gida ruwa ya dauke ma’aikatan sa na katuwar rumfar da suka saba zama suna jiran dawowarshi. kafin ma yay parking din motar sun isa inda yake suna masa barka da zuwa, ba tare da ya bude motar ba ya amsa musu, kana kowa ya koma inda yake. Ya bude motar tashi ya fito itama ta bude ta fito jikinta na wani irin d’ari da karkarwa….Bin bayansa take simi simi har yanzu bata daina zubda hawaye ba.

Bai wani saurareta ba ya shige bedroom dinshi domin yay wanka ya sauya kayan jikinshi zazzabi zazzabi ma yake ji a jikinsa kasancewar dama shi tunfil-azal ba mutum ne me son ruwan sama ya dake shi ba……Ta jima tsaye a parlon tana kuka kafin ta lalla’ba ta shige nata bedroom ta hau cire kayan jikinta ta daura towel ta nufi bandakin, to kafin tayi wankan ma sai da taci kuka ta koshi kana ta fito kanta nayi mata wani irin bala’in ciwo mara misali, tana kuka taje ta kudundune jikinta da bargo, tana rufe idonta……Shigowarsa dakin ya sanya ta mike zaune da sauri tana matsawa lokon gado dan tana ganin kamar zai daketa ne ko yayi mata wata illar mugun tsoronsa takeji tunda ta lura idan ranshi ya ‘baci bai iya hukunci ba.

Kayan sanyi ya sanya a jikinsa masu kauri kanshi sanye da hular sanyi ya rufe har kunnanshi mugun sanyi yake ji mai shiga jiki ga zazza’bi na damunshi haka kawai ta janyo masa lalura.

Kafin yace komai ta soma kuka tana d’ad’daga hannuwanta sama da fad’in”Don Allah kayi hakuri wallahi ni babu ruwana, dama shin……Kasa karasa maganar tayi ta hau inda inda tana rawar baki.” Ya zuba mata idanunsa yana kallonta fuskarshi babu walwala ko ta kwabo, yace.”Ki nitsu ki daina wannam firgice firgicen da kikeyi.” Hannunta tasa ta rufe bakinta hawaye na ambaliya a fuskarta, ya zauna gefan gadon yana kallonta har sanda ta dan samu nutsuwa, Kawai taji sautin muryarshi yana fad’in”Me kuka shirya akaina ke da mutanan naki? Kuna so ku kasheni ko.’!? Tayi saurin kallonshi tana girgixa kanta……Yace.”Hakane mana.” ” Wallahi ba haka bane.” Yace.”To naji, Ina zaki bi As kike gudu.”? Sai hawaye ya soma shatata! yace.”Ba kuka nace kiyi min ba.” Tayi shiru tana kallonshi, yace.”Kiyi min bayani dallah dallah kan a’lamarin.” Tayi shiru tana me sunkuyar da kanta kasa! Tsawa ya buga mata yace.”Zazzabi nakeji a jikina yi min bayani abinda nace ba kuka nace ki min ba.” bakinta na rawa ta shiga wassafa masa yanda suka tsara ita da As da yanda in ta kufce daga hannunsa zasu gudu fataskum sannan kuma ta kaishi kotu shi da mai allo kana idan al’kali ya raba auransu ta dawo ta cigaba da harkokinta, Ya dinga kallonta yana girgiza kanshi, Mahaifiyarta bata da hankali ko d’an! abinda yake ayyanawa kenan cikin ranshi, to idan ba rashin hankali ba me zai sanya ki zauna kina tsarawa ‘yarki shirme da abinda zai cuceta har ta dinga kokarin kashe mata aure, amma babu komai shi ya san abinda zaiyi musu.

“Na yarda babu abinda ke damunki sai jahilci da da’kikanci! Allah yayi miki suttura kina nema ki butulce masa, me nayi miki? me kuma me allo yayi miki da har kike nufin tozarta mu ki kaimu gaban al’kali! kan anyi miki alkairi ke zaki mayar da sharri! ko da yake tarbiyace baki samu ba tun farko ku kusa ko alama ni bana ganin laifin Kawunki saboda yayi iya bakin kokarinshi a kanku, k

eda ‘yar uwarki da ita kanta ‘Yar uwar taki! amma dake keda da maman taki duk taron mahaukatane kuna adawa dashi Okey ni Ahamdu mutukar na cika d’an halak! sai nayi muku abinda kuke bukata, kafin ki tozartani ni zan tozartaki! Ni Ahamdu ba’ayi min na bari! idan kinga na bar abu nine nayi niyyar bari, Yau zaki gane asalin waye ni.”!!!!

Kuka take sosai tana fad’in”Don Allah dan annabi kayi hakuri wallahi kuskure nayi kuma bazan ‘kara ba nayi nadama ni na hakura ma da komai zan zauna da kai nasan kai mai kaunata ne tunda har ka ceto ni lokacin dana fad’a ruwa nagane rayuwa ba’a bakin komai take ba.”

Yace.”Tubanki na banxa ne Siyasar banga da Jagaliya kike so kiyi to zan baki lasisi a hannunki.” Yana gama maganarshi yasa kai ya fice daga dakin.” Ta kwanta tare da takure jikinta tana ta kuka da makyayatar jiki.

A daran ya kira dr Nasir yazo ya danyi mishi treatment ya bashi maganguna dan zazzabi da mura mai karfi ce ta kamashi, abinci yaci yasha magani kana ya shige bedroom dinshi ya rufe yayi kwanciyarshi akwai bacci me nauyi ya daukeshi.

Yanda taga dare haka taga rana, lokaci zuwa lokaci gabanta na wata irin faduwa, idanununta sun kada sunyi jawur tsabar kuka da damuwa da kuma tsananin zazzabi da ciwon kan dake damunta………..Asubah nayi taje tayo alwala ta fito ta duba doguwar riga mai hula mai dan nauyi tasa a jikinta kana ta tayar da sallah……Kwanciya tayi kan dadduma tana lumshe ido bacci mai dad’i yana fuzgarta, ya turo kofar dakin ya shigo, a zabure! ta mi’ke zaune tana gyara zaman hijab dinta da ya karkace…….Yana sanye da jallabiya fara tas da ita har yanzu kanshi na sunkufe da hular sanyi har kunnanshi kafafunshi ma safuna ne farare ya iske inda take zaune kanta a kasa tana watsa da ‘yan yatsunta! Hannunsa guda dake cikin aljuhunsa ya zaro ya fito da wata takarda fara a nannad’e ya mi’ka mata……Dake kanta a ‘kas! yake bata ankara ba sai da yace.”‘Kar’ba.” tayi saurin d’agowa tana kallon hannunshi, gabanta yayi wani irin bugu! Innallihi wa’ina ilahi raji’un! Sai le’bubanta suka soma rawa suna had’uwa!!! “M….me zan kar’ba.” Tafada tana kallonsa da gwala gwala idanunta da suka gaji da kuka.” Kai tsaye yace.”Abinda kike bukata ne nayi miki.”! Sai hawaye ya wanke mata fuska! ta sa hannunta dake karkarwa ta kar’bi takardar! Shi kuma ya kama hanya ya fice daga d’akin……Kasa bude takadar tayi ta ajiyeta a gabanta ta ‘kura mata ido le’banta sai rawa yake had’e da jikinta cikin ranta take fad’in “Ubangiji Allah yasa mutumin nan ba sakina yayi ba a lokacin da nayi nadama nake sha’awar zama dashi.” Ihu! ta kurma bayan ta warware takardar ta karanta abinda ke ciki.

Ni Ahmadu Musa Na saki matata Wasila saki d’aya idan ta samu miji tayi aure

A sukwane ta bud’e ‘kofar dakin ta fice palor hannunta rike da takardar tana gurshen kuka ta nufi dakin shi, lokacin yana ‘balle magani zai sha kawai ta afko dakin……Kafafunshi taje ta rirrike tana kuka da shashsheka! “Dan girman Allah kada kayi mun haka! Wallahi nayi nadama bazan sake ba, zan zauna da kai bisa amana, ka mai dani dakina kar muyi haka da kai.”!!! Baice mata uffan ba ya afa maganin abakinshi ya kora da ruwa ya aje goran ruwan kan bedside kana ya kalleta duk tayi wujiga wujiga! har wata ‘yar rama tayi tsakanin jiya da yau d’in ga kuma alamun tashin hankali da fargaba da nadama nan a tare da ita, Yace.” Lokaci ya ‘kure miki ai bakiji abinda nace bane ? Idan kin samu miji kiyi aure Ahmadu ya barki har abadah.”! Sai ta sake shi tana masa wani irin kallo! kamar zauntacciya tace”Wallahi babu inda zanje ina cikin gidana ni bana son saki ai kaine ka kar’be min budurcina kuma sannan zaka mayar dani ‘karamar bazawara da ‘kananun shekaruna, ni babu inda xanje dan ni ba bazawara bace kuma ni bani da wani miji idan ba kai ba………Yayi bala’in shan kunu yana sake tamke fuska yace.”Tun wuri ki kwashe duk wani abu da kika san naki ne a gidanan ki fice min a gida minti talatin na baki wallahi idan ba haka zan sanya su Garba suyi miki rashin mutunci sai kin fita da kwayayyar fata kamar yanda ‘kawarki ta fita dashi.”
Bubbuga ‘kafafunta ta shiga a ‘kasan dakin ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button