NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

na yayyaga takardar sakin tana kuka wiwi da majina da hawaye sun had’e a fuskarta tana fad’in”Ni ban saku ba, babu inda zanje wallahi ba zaka mayar dani bazawara ba.” Sosai ya shiga mamakinta da maganar ta wai ba zai mayar da ita bazawara ba ashe tana kishin kanta haka? amma kuma take neman saki da kanta har da ikirarin shiga kuto gashi kuma an saketa anyi mata yanda take so tana nadama! Tabbas bakin al’kalami ya riga ya bushe yanda yayi rantsuwa a kan ya gama zama da ita har abada ya gama taje ta ‘karata da ba’kin halinta.

Da ta dameshi da kuka ya mike a zafafe! yana zare mata ido! bata tsorata ba sai ma sake gyara zamanta da tayi a dakin tana takurewa, yaje ya hau janta domin ta fice masa daga dakin kukanta na damun ‘kwalkwarshi! Nan fa d’aya! labule ta kama ta rik’e tsam! tana turjewa wai ba zata fita ba……Ya kwad’a mata lafiyayyan marin da yasa taga gilmawar taurari a idanunta! Shouting dinsa taji a kunnenta yana fad’in” Kin fi son muyi irin wannan rabuwar ko okey……Janta ya so mayi ta rike ‘kafar gado tana kuka da fad’in “Nayi nadama ba zan sake ba ni babu inda zani nan ne gidan mijina.”! Sosai ta rike kafar gadon ta’ki saki! Kawai ya tattaro ta gabadaya ya dauketa bai dire ta ko ina ba sai palo, yana kokarin juyawa ta rike masa kafafu! Yau yaga jaraba da naci da ‘kulafuci!! Fuzge kafarshi yayi yana jan tsaki! ya koma dakinshi, Ranshi idan yayi dubu ya ‘baci…..Ita kuwa bayan shigewar sa dakin kwanciya tayi kasan carpet tana wani irin kuka da kiran mutuwa tazo ta dauketa ta huta da wannan kad’arar data afka mata.

Littafin na kudi ne….!
Kika fitar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
alliya:
‘Yr Bngr Sys
49
Kofar dakin nashi ta tsirawa ido tana daga inda take kwance hawaye sai zurara yake daga idanunta, shikkenan ta cuci kanta! shikkenan ta tashi daga budurwa ta koma bazawara! abinda ke tayi mata yawo kenan a kwakwalwarta! Wani sashe na zuciyarta yake kara tunasar da ita abinda ta manta, itace fa take so a saketa kuma yanzu murna ya kamata tayi ba kuka ba, da ba tayi wannan tunanin ba sai yanzu? Hawaye ya sake kece mata, sam ba tayi wannan tunanin ba sai yanzu da Allah ya jarrabeta da son auran take tunanin zawarci! mikewa tayi xaune tana goge hawayen fuskarta palon take bi da kallo tana ‘kissima abubuwa da yawa, Dole ne ta nemawa kanta mafita, dan daga yanzu ta daina daukar hud’ubar mahaifiyarta a ganinta duk itace ta ingizata fadawa wannan halin, zawarci da kuruciyarta, yanzu ta daina ganin laifin Rashida gashinan Allah ya nuna mata gaskiya tun kafin ayi nisa, Hotonshi dake manne a wata kusurwa ta dakin ta zubawa ido! hawaye masu zafi suka sake yanke mata, wani irin bala’in sonsa taji sabo na ratsa zuciyarta, ta mike ta isa inda hoton yake tana kallonsa, yana zaune kan wata had’addiyar kujera sanye da farar shadda! sai murmushi yake yi! tsayin ta ba zai kai inda hoton yake ba tana so ta dauko ta kasa, sai ta kura mishi ido tana fad’in “Tunda ka sakeni dole na tafi na bar maka gidanka! nayi nadamar abinda nayi maka! ba’a hada baki dani ba akan a cutar da kai kamar yanda kake zargina! kawai nima shaidan ne ya zugani amma yanzu nagane abunda kake so ka gane! zan tafi in bar maka gidan ka tunda ka saken…….! sai ta kasa karasawa ta zube a gurin tana dukan kujera hade da wani irin kuka mai cin rai!!! kimanin minti goma tana cikin wannan halin kafin ta mike zumbur! ta nufi dakinta, Wani tunani tayi a yanzu dai babu mai sasanta al’amarin nan sai mai allo shine zai shiga cikin maganar yasa Ahamadu ya mai da ita.
Ta dauki karamar jaka ta zuba kayanta, wayoyin da ya siya mata tun jiya ta mantasu a motarshi, hakan bai dame ta ba a yanzu, hijab din da take sallah ta zura ta fito tana goge hawaye, kofar dakin shi ta kalla har yanzu tananan a kulle, taji zuciyarta ta sake karyawa, tabbas ya nuna mata shi din dan halak ne! sam bata ta’ba tsammanin zai saketa kaitsaye ba sai gashi tun bata dangana shi da al’kali ba ya yanka mata ticket, ta bude kofar palon ta fita zuciyarta na tsananin harbawa, shikkenan duk wannan daula da jin dad’in sun zama labari Shikkenan duk uwar soyayyar da yake mata lokacin da suke marking love ta yanke, ta sanya hannu ta share hawaye tana tuno irin rayuwar jin dadin da suka dingayi yanda suke soyayya suna jiyar da kansu dadi! kuka tasa tana girgiza kanta haka nufi bakin gate ta kasa tsaida hawayen fuskarta yanzu idan Ahmdu bai mai da ita ba wace irin rayuwa za tayi……..Dukaninsu sunyi mamakin ganinta da jakar kaya tana kuka, Garba ya hana abude mata kofa ta fita yace dole sai ya sanar da mai gida….Ta tsaya gefe tana goge fuska tana addua Allah yasa idan yazo ya tausaya mata yace ta koma gidan……Ya kirahi a waya lokacin baccinsa baiyi nisa ba sosai ya daga wayar Garba yay masa bayanin abinda ke faruwa. Kai tsaye yace.”Ku bude mata kofa kuma kabi bayanta kaga ina ta nufa.” Garba yace.”Shikkenan yallabai.” Kashe wayar yay yace su bude mata kofar, Jikinta a sanyaye taja jakarta ta fita daga gidan……Garba sai da ya dai-daici ta fita babban titi kana yabi bayanta, aikuwa yaga tana tare abin hawa! shima ya tare ya shiga yace da direban ya bi bayan babur din dake gabanshi duk inda yayi, haka kuwa akaiyi, Wasila ta sauka a bakin titi ta biya me babur kudinshi ta ganganra domun shiga Estete din da gidanta ke ciki, Garba na biye da bayanta bata sani ba. Sai bayan yaga shigarta gidan ne ya kira wayar Ahamdu ya sanar mishi da cewar ga inda taje Yace.”shikkenan kyaleta kawai ka dawo gida.” Garba ya mai da wayarshi aljihu ya bar bakin gate din.
[8/8, 12:03 PM] .: Uwani Camas! Rashida na zaune suna karyawa Wasila ta tura kofa ta shiga, dukaninsu suka maida hankalinsu kofar shigowa, kawai suka ga Wasila ta shigo fuskarta a jeme idanunta yayi wani irin ja! sun kara girma ga fuskarta ta nuna al

amun tashin hankali da nadama gami da dana sani! Da sauri Uwani ta mike tsaye tana fad’in” Yaya na ganki haka? Cikin damuwa yanzu dama muke maganarki ina cewa kiyi maza maza kizo mu taf…….Kafin ta ‘karasa maganar dake bakinta taga Wasilan ta zube tsakiyar dakin tana kuka hade da dafe kanta tare da fad’in”Na shiga uku na lalace.”!!! Uwani gabanta ya yanke ya fad’i sai ta dur’kushe gaban ‘yar tata tana karkarwar jiki ta rirri’kota jikinta tana tambayar ta abinda ya faru!!! Wasila ta shiga tutture ta tana shashshekar kuka da fad’in “Kece kika jawo min wannan masifar duk wani wahala da zan shiga a rayuwa ta kece!!!!! Uwani taji wani gumi ya tsinke mata! Wai shine meke faruwa ne? Rashida da Camas! suka iso inda take durkushe tana kuka! Kawai sai ta kama Rashida ta rungume ‘kam!’kam! tana wani irin kuka.! Rashida taji zuciyarta ta karye itama sai ta soma kuka tana tambayar ta abinda ya faru!! Cikin hard’addiyar magana tace”Rashida ya sakeni! Ahmadu ya sakeni!! ya sakeni Rashida na gane abinda kike ta so nagane yanzu Uwani ta cuceni na cuci kaina innalilihi wa’ina ilaihi raji’un”! Da jin wannan maganar dake fitowa daga bakin Wasila sai kawai Uwani taja tsaki tana fad’in” To sai me? dan ya sakeki? dama ai haka muke bukata bai wahalar da kanshi ba bai wahalar damu da sharia ba, dan haka sai muji dadin yin harkokinmu cikin kwanciyar hankali, ni wallahi na dauka ma ko wani abun yayi miki ko kuma zakice kina da ciki shiyasa ma hankalina ya tashi.” Wasila ta d’ago kanta tana kallon Uwani sai ta hau girgiza kanta takaici da bakin ciki fal ranta, Wai Mahaifiyarta ce ke murna da mutuwar auranta dan dai bata san yanda takejin bakin ciki bane cikin zuciyarta……Bakinta na kyarma! tace”Uwani murna kikeyi da mutuwar aurana.”? Uwani ta kalleta cike da mamaki tace”To ai abun murna ne abinda muke nema ne fa ya samu to meye zaki damu kanki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button