YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Suna tsaye a gurin biyan kud’i ya ‘karaso gurin sai taga ana bashi girma duk ma’aikatan gurin na kiranshi da Sir tayi ‘kasa da kanta tana jinsa na magana cikin had’addan turancinsa da babu tangarda a ciki duk sai ta raina kanta gaskiya ilimi yayi addua takeyi Allah yasa kar ya waiwayo ya kallesu……….Ya kalli Manager gurin da Hausa yace.”Cikin wannan satin Salim zaije saudia wani na’uin turare da babu a gurin nan sa ka rubuta masa gudun mantuwa.”
Yace.”Insha Allahu.” Wucewa yayi ba tare da yayi kuskuran kallon inda suke tsaye ba, suna fita Uwani tace”Oh wannan turanci sai kace wani ba amuruke da alama dai shine shugaban gurin…..Manager da ba hausa yake ji sosai ba ya d’aga mata kai alamar Eh……Rashida tace”Gaskiya aunty Wasila mutumin nan yayi wallahi kun dace dake dashi dama yace yana sonki.” Wata harara ta watsa mata “Dallah kwaso kayayyakin mu wuce kin tsaya kina shashanci dare yayi.” Rashida ta dauki manya manya ledoji guda biyu Uwani ma ta dauka itama ta dauka haka suka fita hannunsu ni’ki ni’ki da kaya su ba mota ba, sai da suka fito ne ma suka fahimci dare yayi sosai dan goma ma ta gota…..Da kyar! suka samu mai babur ganinsu da kaya ya sanya ya lafta musu kudi wai dubu biyu Wasila tace”Muje zan baka.” aikuwa da sauri yaja babur din suka dauki hanya.
Sai da suka zo dai-dai titin makarantar legal tayar a dai-dai tar tayi faci!!! Tofa ga dare gashi babu masu faci a kurkusa ga gurin tsit! sai kukan tsintsaye….Uwani ta fito tana salati da sallami motocin gida jefi jefi ne suke wucewa suma kuma da gudu suke wucewa saboda sun samu arhar titi babu go solow, Wasila ta fito daga babur din tana fad’in”Yanzu ya za’ayi? kai innalilihi gaskiya banji dad’i ba wallahi.” Mai babur yace.”Ni wallahi na rasa ma ya zanyi dana sani nake wallahi dan idan ban samu wanda zaiyi min faci ba dole in bar babur din a gurin…….Wasila tace”To mu kuma muyi yaya kenan.”? Yace.”Hajiya dan Allah ki kyaleni naji da abunda ya dame ni ai kuna da kafafu ku karasa mana a kafa.”
Rashida tace”Ka duba tazarar dake tsakanin nan da dorayi fa akwai sauran tafiya gaskiya mu dai kasan yanda zakayi damu.”
Haushi yasa mai babur din fad’in”Ai sai ku kwana a gurin ni kunga tafiya ta.” Ya zare key dinsa daga jikin babur din ya dauki hanya ya barsu a tsaye a gurin…….Sai da suka daina hangoshi sannan suka tabbatar da cewar da gaske ya tafi din Wasila tace”Ai sai ku dauki kayan muma mu daura damarar tafiya da kafafunmu dan babu wani alamun babur a kan titin nan.”
Suka d’addauki ledoji suka saici hanya suna tafiya fakam fakam! ga nauyin kaya ga gajiya sunyi masifar galabaita……Sunyi nisa d a tafiya sosai suka hango ana haske su da touch Dukaninsu sun razana! ganin wasu tsagerun matasa sun durfafo inda suke “Kai! matanan daga ina kuke ne.”? Uwani tace” Ku bamu hanya mu wuce munyi dare zamu koma gid…..ai kafin ta rufe bakinta na kusa da ita ya wafci ledar hannunta yana zazzagewa…..Wasila tace”Kai meye haka kuk…..Ita taji ya fizgo jakarta dake rataye a kafad’a ya zazzage a kasa uban kudi suka watse a gurin….Ihu!! suka zumduma! suna fad’in Kai!! ashe yau mun fito a sa’a Kwashe mana su mana jeka bunciki jikinsu kaga ko da akwai sauran wasu idan da gold a jikinsu ka ciro.” Babban cikinsu ne ke wannan maganar…..”Kar ka kuskura ka ta’bani wallahi hannunka ya sauka a jikina sai nayi maka illah.”!! kamar mahaukaciya take maganar….babban cikinsu ya taso yana haskata da touch “Wow!! yafada yana lasar le’be.” Baby wannan jikinki naki ai bana banza bane ke kanki kin san sai an mora da har kike maganar zakiyi wa yarona illah to kafin kiyi masa ni bari nayi fara miki.”
Yana kai hannunsa jikinta ta gaura masa wani lafiyyan mari!!!! Ya kurma wani ihu! “Ni kika mara!? kanta yayi ta goce a guje tayi kan titi yabi ta hijab dinta ya take da kafafunsa tayi dubarar zare hijab din ta mike a sukwane ta sake ranta a na kare gashin kanta duk ya warware ya zubo mata a fuska da kafada……… tana tsallaka titi taga haske fitilar mota ta doso, tun kafin ta karaso take daga hannunta sama……Yace.” Garba rage gudun motar nan babu lafiya waccan kamar yarinya mace Allah yasa ba fyade za’ayi mata ba.” Garba yace.”Ai kuwa sir ga dukanin alamu hakad’in n…. ai kafin Garba ya rufe baki Goga ya iske inda Wasila take suka hargitse da kokawa……Da sauri yace.”Subahannahi Garba kashe mota.” Garba ya kashe mota da sauri ya bude motar ya fito wanda yayi dai-dai da lokacin da Wasila ta samu nasarar kwatar kanta daga Hannun Goga, a jigace! ta iske! inda yake tsaye ta afka kansa ba tare da ta sani ba, yayi saurin dafe bayanta da hannunshi guda yana kallon Goga ya dumfaro gurin……Yana isowa ya kai masa ‘kwakkwaran naushi! da hannunsa guda ba tare da ‘bata lokaci ba Goga ya zube a gurin hancinsa na zubar da jini
‘YAR BANGAR SIYASA!!
???? romantic love story????
NA:
BINTA UMAR ABBALE ????
????Manazarta Writes asso
‘Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*Free Pege 9*
Yaran Goga na hango ogansu a kwance a 'kas yana matagugu! sai suka ranta a ana kare ko wannesu na neman mafaka a tunaninsu jami'an tsaro ne sukayi basaja, a gurin......Uwani da Rashida suka iso gurin hankalinsu a tashe Uwani fadi take"Shegu tsinannu 'yan iska kawai mu samu kudinmu da 'kyar! su biyo dare su 'kwace ai gaskiya 'barawo baiyi ba."
Ahamad ya d'an ja jikinsa kadan ganin ta daina rawar jikin da takeyi ya dan tsira mata ido fuskatara na kallon 'kasa ta kasa dago kanta har yanzu da akwai furgice a tare da ita sosai ta tsorata da goga a duniya babu abunda takeji dashi kamar budurcinta
Rashida ta 'karaso inda take tsaye tana mika mata hijab dinta ta kar'ba ta zura Uwani tace"Amma dai babu abunda yayi miki ko." Daga kai kawai tayi tana goge fuskarta 'kamshin turaran da mutumin yake yi shine ya dabbeta tana ji kuma kamar tasan me irinshi
Muryarsa ce ta daki dodon kunnata wanda yasa tayi saurin dagowa sai taga ya juya yana tafiya bayanshi kawai ta kalla ta gane shi! *Ahamdu* ne Garba yace."Yallabai yace."Ku shigo motar sai mu aje ku a gida amma yana da kyau ku daina tafiya irin wannan ku kai dare kasancewarku mata akwai 'bata gari a ko ina zasu cutar daku."
Wasila ta dago kanta tana kallon Garba ya kalleta da mamaki! sai yanzu ya ganesu sune ashe!? to anya ma kuwa Yallabai din ya gane su.....Uwani ta hau daukar kaya ta nufi motar Garba yace."dan dakata tukkuna." Motar ya nufa ya tarar dashi a kishingide idanunsa a lumshe wata iriyar kasala ce ta dabaibaye shi sakamakon rungumar da yarinyar tayi masa duk ta gwaggoga nasa nonowanta a kirjinsa tsigar jikinsa sai wani irin mikewa takeyi sanyi sanyi ma yake ji burinsa ya isa gida ya kwanta ko samu sauki......"Sir." Garba ya kira sunanshi yana runkufar da kansa ya bude lumsassun idanunsa yana kallonsa yace." Shin ka gane ta kuwa? naji kace su shigo mota yarinyar nan ce fa mara kunya wacce ta zage ka dazu gurin kamfen." Ya tsirawa Garba ido yana kallonshi da mamaki a tare dashi.....Garba yace."ai da kana gurin kasa dago fuska tayi saboda itama tasan bata kyauta sai bayan ka bar gurin ne ta dago fuskarta nan na ganeta.......Jim! na minti biyu kafin yace."Kyaleta kawai shigo dasu muje dare nayi taci albarkacin abokanan tafiyarta."
Garba baiyi tsammanin hakaba saboda yasan halin Ogan nashi baya barin bashi babu shakka yarinyar nan na samu dama a gurinshi..........Wasila kam masifa ta hau yiwa su Uwani wai lallai sai sun shiga motar tunda Allah yasa zai tamaike su ita kuma kunya tasa tace dole su dauki kayansu su karasa da kafa ai sun kusa isa gida babu yanda zasuyi da ita suka dauki ledojin suka hau tafiya fakam! fakam!!! Garba ya cimmusu yana fad'in"Yallabai yace."Ku shigo muje ku kawo kayan." Ya hau kar'bar na hannun Rashida ta sakar masa dan dama ita ta riga ta gaji tsoron masifar wasila takeji Uwani ta kalli Wasila dake cigaba da tafiya tace"Haba Wasila ki tsaya mana a taimaka mana kinsan fa kafin muje gida mun galabaita gashi kin san inada ciwon kirji idan ya tayar min kamar zan mutu.
Tace"Tunda dai kun nace sai mun shiga muje amma meye saura anan mun kusa zuwa 'yan babura fa." Rashida tace"Eh duk da haka dai aunty Wasila ai ragi ragi ne." Shiru tayi musu suka kawai tabi bayansu a zahirin gaskiya bata son shiga motar dan dai kawai sun nace ne! Yana hango zuwansu gurin ya fito daga bayan motar ya bude gaban motar ya zauna gilashinsa ya gyara, ya tamke fuskarsa yayi dakacen hada jiki da ita ko da yake ai itace ta rungumeshi........Yana da tausayi sosai mussaman kan 'yaya mata shine dalilin ma da ya sanya ya tsaya amma da yasan yarinyar nan ce mara kunya babu abinda zai sanya ya tsaya ya 'bata lokacinsa Hanyar biri daban ta mota daban.
Suna shiga motar sanyi Ac da kamshi ya bakunce su, Uwani ce a farko sai Rashida Wasila ta zama karshen shiga motar sai dauke kai takeyi bata so su hada ido dashi gashi sun zauna a site daya tana kallon fuskarshi ta mirror ya hade rai! sai itama ta hade nata ran! tayi kasa da kanta, ita sam wannan taimakon baiyi mata ba saboda babban abun kunya ne guy nan yaje yaga makwancinta duk da haka dai ba zata bari su shiga ciki ba a bakin titi zasu sauka.
Jin surutun da su Rashida yayi yawa yana nema ya karasa wata damuwar bayan wacce yake ciki......Sai ya sanya hannunshi ya kunna redio karatun alkur'ani ya soma a tashi daga bakin *Ahamd Sulaiman* Duk da haka dai su Uwani basuyi shiru ba sai surutu suke suna ta zancan 'barayin da suka tare su.
Gyaran murya yayi sai suka yi shiru suna kallonsa....Wasila ta dan ja tsaki kadan tace"Dan Allah kuyi shiru idan munje gida kwayi maganar haba."
Shiru sukayi basu sake cewa komai ba motar ta cigaba da tafiya.
A hankali ya dago idanunsa dake sakaye da gilas yana kare mata kallo ko da wasa baza kace ita yake kallo ba saboda yanda yake wani basarwa.......Yarinyar nada kyau! sosai sai dai bata da kunya ko kad'an! shi kuwa baya shiri da mara kunya marasa ganin girman na gaba dashi.
Dai-dai bakin titin 'yan babura Wasila tace"Ajiye mu anan ba sai ka shiga damu zamu karasa da kafafunmu.
Uwani tace"Haba 'yar nan ki bari mana a karasa damu mana mutumin nan fa taimakon yake yi kar ki katse masa hanzari." Dan Allah aunty Wasila ki bari a karasa damu." Rashida ta fadi maganar tana karyar da kai.....Sai magiya take mata kamar zatayi kuka."
Yace."Garba shiga da motar nan ka kaisu har kofar gidansu kar ka dakata maganar ta." Yace."Angama Yallaba.'!
Uwani tace"Mungode sosai Allah yayi albarka alhaji Allah yasa a gama lafiya, Allah ya raya zuria." Ya amsa da "ameen." yana duba wayarshi....Wasila kam! sai shan kunu takeyi sam bata so haka ba dan dai kawai sunfi karfinta ne.
Wani tsukakken layin suka shiga motar ta dinga gwajab gwajab!! tana cijewa......Ya dan gyara zamanshi yana duba yanayin ungywar kai da gani kasan unguwace ta marasa galihu gidaje kananu babu tsayin katangar arziki ga kwatoci duk sunbi hanya abun babu kyan gani sam unguwar bata yi masa ba, bai shiga mamaki ba sai da yaji muryata na fad'in"Tsaya anan ga gidanan ai." Yabi gidan da kallo yana mamaki! wai sunan angyara ansa kofa da lokacin buhu ne abun sai ya bashi mamaki dan adam ke rayuwa cikin wannan gidan rubabbe lokacin damuna mutum na cike da fargaba da alhini kar ya rikito masa amma su haka suke kwanciya hankalinsu kwance......Tausayi suka bashi yanzu ya gane abunda ya sanya yarinyar famtsama harkar Jagaliya talauci masifa ne! da'alama kuma su kadai suke rayuwa a gidan.....Tunaninsa ne ya katse lokacin da ya hangota tana bude gidan...Uwani da Rashida sai faman godiya suke masa, Ya bude wani guri a cikin motar kudi ya dauko a daure a kyaure! ya mika ma Uwani ta karba hannunta na rawa gwiwa kasa ta zube tana godiya yace."Tashi dan Allah kamar hakan bai dace ba nayi niyya ne na baku amma akwai 'yar shawarar da zan baku idan babu damuwa." Tace"To Alhaji Yace."Ki hana 'kanwarki harkar Jagaliya sam bai dace da 'ya mace ba ni zan taimake ku sannan idan kun samu mijin aure kuyi aure ni zan dauki nauyin komai naku." Sai Uwani ta fashe da kuka tana fadin "Alhaji labarinmu mai tsayi ne Wasila kuma ba kanwata bace babbar 'yata ce sai Rashida su kadai na haifa marayu ne babansu ya mutu tun kafin suyi wayon haka sannan duk dangi sun guje mu saboda bamu dashi mune muke ciyar da kanmu kaga kuwa har jagajiya ai sana'a ce bazan iya hanata ba tunda gashi ta rufa mana asiri."
Yayi shiru yana sauraronta tausayinta yaji ashe itace mahaifiyar yaran shi ya dauka yarsu ce, Ganinta tana kuka ya sanya yace." amma al'amarin akwai hadari a ciki tunda kun daukeshi a matsayin sana'a Allah ya taimaka." Uwani ta amsa da "ameen tana sake godiyar kudin da ya basu....Ahamad ya bawa Garba Umarnin tafiya Garba yaja motar suka bar gurin Wasila kuwa ta jima da shiga gida sai haushin tsayuwar su Uwani takeyi a waje Allah yasa dai ba ro'konsa suka tsayi ba tasan halin masifar kwadayi da roko na mahaifiyar tata.
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
???? romantic love story????
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE ????*
*????Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
NA KUDI NE…….!
Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za’a tura kudin.0542382124…….Binta Umar gtbank….Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din….07084653262_08089965176 sai na fad’i yanda za’a biya kud’in…..Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars…….90899076_88137740 katin airtal ko oragne
Free Pege10
Suna shiga cikin gidan Wasila ta rufe su da masifa,”Haba Uwani nifa bana son ‘karanta bisabillahi yanzu minti na nawa da shigowa cikin gidanan kuna can kuna maula da zubda mutunci dama tunda naji shiru nace to kun tsaya roko wane irin rayuwa ce ban saka kaina ba a akanku amma duk da haka sai kun watsa min kasa a ido idan kuka ce haka zaku dinga yi to wallahi zan barku da halinku ko na samu kudi in boye kaya na.”
“Haba ‘Yar nan, mutumin nan ya cancani a tsaya ayi masa godiya ba don komai ba sai dan taimakon da yayi mana a wannan zamanin ba ko wane mai kudi ne zai tsaya ya taimaki talaka ba yanzu idan da badan yazo gurin ba da me kike tunani zai faru tsakanin da ‘barayin nan nasan wallahi sai sunyi mana tas! wannan budurcin naki da kike tattalawa su keta shi da wagari ya waya ai dole a tsaya ayi masa godiya ba abunda kike tunani ne ya tsayar damu a gurinsa shine dai yayi niyya ya bamu kudi kingasu ma.”
Ta mika mata daurarrun kudin dake hannunta, Wani banzan kallo tayi wa kudin kafin tace”Yanda ya baku kudin to ku ajiye ko lissafawa bance ayi ba ni ina da a’kida idan ina son mutum a siyasance ina sonsa idan bana son mutum bana sonsa dan haka banga abunda kudinsa zasuyi min ba tunda dai ina dasu.”
Uwani da Rashida suka saki baki suna kallonta da mamaki! wannan kudin masu tarin yawa zasu aje to akan me? ai su ba ‘yan siyasa bane kuma ai ba ita ya bawa kudin ba su ya baiwa ballanta tace.
Wasila tace”Ko kuna so dai inyi muku bayani dalla dallah akan mutumin nan domin naga kudinsa duk ya furgitaku.”
Uwani tace”To ai kece naji kina wata magana a wannan zamanin ayi maka kyautar kudi ka mayar gaskiya abin da kamar wahala.”
“Uwani wannan guy fa shine dan takarar Governor a yanzu dashi suke fafatawa da Governor mai ci a yanzu kuma duk kudin da kikaga na samu ta bangaran harkar siyasar nan to ta dalilinsa ne dan akanshi muke jagaliyarmu saboda haka duk ranar da mai girma governor yasan da cewar ina bangare biyu a wannan harkar to yan kudin da nake samu zai hanani dazu fa cewa yayi zai zauna dani na fada masa dukanin bukatuna sannan kuma ya sauke mukamin wani a dora ni a kai nan gaba kadan ina ganin zan zama ‘kusa a harkar dan haka banga amfanin da wad’annan ‘yan kudin zasuyi mana gobe insha Allah kafin mu isa government house zan kai masa kudinsa har gida bama bukata.”