YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Asabe mahaifiyar Camas! na zaune a kujera ‘yar tsuguno tana tsince shinkifa taji sallamarsu, ta amsa tana musu sannu da zuwa tabarma ta shimfida musu tana fad’in “Wasila yau kece a gidan
namu, Ina tace Hadiza zata rakani inga inda kuka koma Allah bai nufa ba sannunku da zuwa.” Suka shiga gaisawa, Asabe na tambayarsu Uwani sukace tananan lafiya lou. Wasila tace”Camas! kuwa tanan.”? Asabe tayi kasa da kanta ran nan a ‘bace tace”Yaushe rabon hadiza da kwana a gida ai tafi wata uku sai dai takanzo duk bayan sati biyu to wannan karon ma kinga satin ta uku bata zo ba.” Wasila tace”Ayya! mybe tananan tafe.” Asabe tace”To Allah yasa.” Shiru sukayi kafin su ta mike Asabe tace”Har zaku tafi bazaku tsaya kuci abinci ba.” Wasila tace”A’a Asabe mungode.” Har soro ta rakosu tana fadin su gaishe da Uwani da kyau kafin tazo.
Suna fitowa Wasila tace na fad’a miki dama kinga munyi asarar kudin motarmu ko? gashi bamu dana komawa gida tsakanin dorayi da tishima akwai nisa sosai dan da kyar ma aka kawo su a dari biyar kona pure watar basu dashi…..Rashida tace”Mu shiga gidanmu wanda muka bawa malam ‘Dayyabu nasan idan yananan zai bamu kudin mota da zamu koma gida.” Wasila taji dadin maganar Rashida sai suka nufi layinsu na da, suna shiga layin suka hango, gidansu ya koma katin sai da kayan provision! tsayawa sukayi suna mamaki! wani yaro da yazo wucewa ya shiga kallonsu yaso ya ganesu Wasila tace”Kai waye cikin provision din can.” Yaron yace.”Jazuli ne na gidanmu malam d’ayyabu ne ya siyar masa da gidan shi kuma ya ruge yayi kanti.” Wasila da rashida suka shiga mamaki! ashe malam dayyabu haka yake sun bashi gida domun ya zauna ya siyar ya kar’be kudin ya gwammace yayi ta yawon haya da yara da mata, cikin unguwar dama su Wasila da gidan malam dayyabu sune talakawa, gwara su wasila ma gidan kansu ne shi kuwa malam dayyabu gidan haya ne duk lokacin karbar kudi sai anyi rigima dashi masu unguwa sun taru a kanshi sannan zai bada kudin, shinda wasila ta tausaya masa suka bar mishi suna ganin tunda sun samu wani me zasuyi dashi ashe bayan tashin su da sati biyu malam dayyabu ya siyar da gidan ya kama haya ragowar kudin yasa a aljihu yana cin karansa babu babbaka dasu…….Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka kama hanya suka bar gurin zuciyarsu cike da wasi wasin yanda zasuyi.
Sosai suka dingi tafiya kan titi wanda tun suna magana suka daina tafiya kawai sukeyi suna yanke yanken hanya har Allah yasa suka fito titin gadon ‘kaya! Rashida ta sharce gumin dake goshinta tana haki! tace”anti wasila zama zanyi na huta na gaji wallahi.” Wasila tace”Mu samu guri mu zauna nima nagaji.” Suka sami guri dai-dai Gate din shiga Management suka zauna suna hutawa, sunanan zaune daliban dake makaranta suka soma fitowa ‘yan mata maza zawara da matan aure wasu na fitowa da motocin su wasu wasu kuma na tare abin hawa! Wasila ta dinga kallonsu suna bata sha’awa suna da gata suna da galihu sunyi dacen iyaye sun tsaya musu kan ilimi su kuwa fa! sune nan sune can! Sai taji zuciyarta ta karye hawaye ya tsinke mata! tayi gaggawar sunkuyar da kanta kasa tana sharewa bata so Rashida ta gani sannan kuma jama’ar dake gurun suma bata so su gani, tana dago kanta suka had’a ido da Suhairat ita da kawayenta bakin wata mota! Zasu shiga macace take driving din, da sauri ta kauda kanta gabanta na faduwa tace”Rashida tashi mu tafi.” Rashida tace”Anti wasila dan bari mu sake hutawa wallahi gurin akwai iska.” Tace.”Rashida hutun jaki da kaya kikeyi kawai ki tashi mu tafi mu samu mu fita babban titi na sabon titi.” Rashida ta mike tana yafa mayafinta sukayi gaba…….Motarsu Suhairat ce taci burki a gabansu, da sauri suka matsa baya Suhairat ce ta bude motar ta fito sauran suna ciki suna hangensu
Gabansu ta tsaya tana watsawa Wasila kallon banza tace”Ke matar babban mutum ina zuwa haka? ya naga kina yawo a kasa ko satar hanya kikayi kika fito yawon tazubar d’in da kika saba.”!? Wasila tayi shiru tana kallonta Rashida tace”Haba Suhairat wace irin magana ce wannan? kin manta anyi muku tsakani da anti wasila meye ruwanki da ita yanzu.” ? Suhairat tayi dariya tana gyara zaman glass din dake idanunta tace”Rashida daga tambaya sai cibi ya zama ‘kari! ai gani nayi bai dace ace kamar wasila matar Ahamadu Musa na yawo ‘kasa ba, ai kamata yay mu ganta cikin katuwar mota
wacce ta amsa sunanta, ko da yake dai ina jin satar hanya tayi ta fito, Okey karfa ku damu da maganata, ba wani abun nake nufi ba, saboda haka na barku lafiya.” Wasila da Rashida suka bita da kallo har ta shige motar tasu suna kallonta tana she’ka dariya tare da tafawa da ‘kawayenta tana nuna wasila da hannunta su kuma sai dariya sukeyi, kafin wacce take driving din ta figi motar a guje suka bar gurin.
Wasila ji tayi gwiwowinta sunyi bala’in sanyi ta inda har ta kasa motsa kafafunta da niyar tafiya sai kawai ta nemi gefan titi ta zauna rana na kwallare mata fuska zufa! ta shiga ketowa daga jikinta
Rashida itama ta zauna kusa da ita tana fad’in”Amma wallahi suhairat din nan bata da mutunci shegiya guzumar banza wacce ta rasa mashinshine anti wasila ki kyaleta don Allah mybe suna da labarin Ahamdu ya sake ki shiyasa suke murna da dariya amma babu komai ai duk abinda mutum yayi kanshi.
Ba tace komai ba tana dai sauraran Rashidan da duk rarrashin da take mata ita kuma sai nanata kalmar innalilihi wa’inna ilaihi raji’un takeyi a zuciyarta, ji tayi komai na rayuwa yayi mata zafi ta dinga nadamar kuskuran da tayi a baya, kanta ne ma ya soma yi mata ciwo, rana ce ko damuwa ce ko kuma rashin bacci ne? babu wanda ya sani sai Allah.
Kusan mintina ashirin suka dauka a zaune a gurin masu babur din a dai-dai ta sahu sai tayi suke musu wai ko zasu shiga kowa na ganin lamun ba shiga zasuyi ba sai ya buga babur dinshi yayi gaba!………………
Cikin ‘kwalleliyar ranar dake kan ganiyar ta, suka fita, titin sabon titin gidan ‘kankanra lokacin sunyi masifar galabaita mutuka gashi ko na pure watar babu Wasila taja hannun Rashida suka fake wata inuwa still dai a bakin titin suke zaune suna mai da numfashi suna kallon ababen hawan dake shige da fice a gurun…….”Wasila anti Wasila yunwa nakeji da shiru kinji ma’kogwarona kuwa kai anya ba zamu nemi taimako ba kuwa.”?
Wasila tace”Nima nagaji Rashida taimako a ina zamu nema.”? Anti wasila mu nemi left gurin masu motar gida sai sunfi sauki akan masu a dai-dai ta sahu tunda su kinga sana’a suka fito.” Wasila tace”anya kuwa Rashida.”
“Allah anti wasila ba zamu iya kai kanmu gida ba akwai fa nisa gashi ko rabi ba muyi ba.” Wasila tace”Akan muyi left din nan ai gwara mu tambayi wannan me shagon na tsalleke watakila ya taimaka mana.” Rashida tace”Bari naje ki zauna dan na lura kamar jiri ke d’ibanki.” Tace”Wallahi jiri nake rashida yi sauri kije Allah yasa ko dari biyu ya bamu.” Rashida ta tsallaka titi domin zuwa gurin me shago……..Mai shago najin bukatar Rashida yace “Duba daya ma zan baki amma shigo ciki na aunaki.” Rashida ta gane abinda yake nufi duba da irin yanayi kallon da yake mata na iskanci! sai kawai taja tsaki! ta fita daga shagon……Ba tayi shawara da Wasila ba kawai ta soma d’aga hannu tana tsaida motacin mutane…….. Khalifa dake driving yay saurin kallonshi hankalinsa na kan jaridar dake hannunshi yana dubawa yace.”Duba wacan yarinyar kamar Wasilan ka.” Yay gaggawar hanya nan ya hango rashida na d’agawa motarsu hannu, ya mai da kanshi kasa ya cigaba da abinda yake! Sai da suka kusa isa gurun rashida khalifa ya gane ba ita bace amma kuma gaskiya suna kama sai dai ita wannan tafi wasila haske! A hankali ya tsaida motar dai-dai inda Rashida take tayi gaggawar zuwa gurin………”Khalifa ya sauke gilashin motar a hankali yana kallonta, rashida ta marairace fuska muryarta na rawa tace”Dan Allah Yayana ka taimaka mana ka rage mana hanya nida ‘yar uwata wallahi tun daga d’orayi muka zo nan a ‘kafa kudin motarmu ya ‘kare.” Tunda rashida ta soma magana yake jin wani iri, maganarta sak! data Wasila, ta gefan ido ya dan kalleta, sai gabanshi ya fad’i! wannan fuskar ai kamar ya santa yarinyar nan ce kanwar Wasila, shiru yay bai ce komai ba, shi kuwa khalifa da bai san abinda ke faruwa ba yaji tausayin rashida yace.”Ina ‘yar uwar taki.” Rashida tayi saurin fad’in gata can tsallaken titi.” Yace.”Yi maza ki kirata.” Cikin farin ciki rashida ta tafi, dake hankalinta na kan khalifa sam! ba tayiwa Ahamdu cikkaken kallo ba ballanta ta gane shi.