YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

“Anti Wasila taso ga mota can zat
a daukemu Allah sarki wallahi me motar nada kirki.” Wasila na daga inda take zaune ta dinga kallon had’addiyar motar tana mamaki! anya kuwa, wata zuciyar tace wasila idan baku shiga motar nan fa babu wanda zai taimakeku gwara ku shiga ko bakin asibiti ne sai ya saukeku in yaso sai ki siyar da zoben hannunki.” Sai ta yarda da shawarar da zuciyarta ta bata, ta mike tana karkad’e jikinta suka nufi motar.
Khalifa tun kafin su karaso yake mamaki! Fuskar wasila ba bakuwa bace a gurinshi itace wallahi.” Ya furta ba tare da ya sani ba, kalmar ta sanya shi dago kanshi yana kallon inda yake kallo, kawai sukayi ido hudu da ita, sai dai ita bata ganinshi shike ganinta kasancewar gilashin motar me duhu ne.
Yace.”Mutukar zaka dauki yaran nan cikin motar ka ka saukeni dan Na rantse ba zan had’a nuffashina dana wannan yarinyar ba.” Khalifa ya dinga kallonshi cikin tsananin mamaki! yace.”Haba! taimako ne fa shin bakaji abinda ‘yar uwarta ta fad’a ba, tun daga dorayi zuwa nan a ‘kafa akwai wahala, kayi hakuri kawai a daukesu ai ba wani abun bane.” Sai kawai ya hau kokarin bude mota zai fita…..Khalifa yace.” A’a me yayi zafi! bari kawai na basu kudin abun hawa ba sai ka fita ba.” Yace.”Hakan shi yafi maka alkairi.” Khalifa ya bude ma’adanar kudinshi dake cikin motar dubu ashirin ya ‘kirga ya zuge gilashin motar, suka had’a ido da Wasila sai tay saurin matsawa baya gabanta na faduwa, dan ta hango gefan fuskar mutumin nata kanshi a kasa yana kallon jarida……Khalifa shima bai nuna ya ganeta ba, sai ya mikawa Rashida kudin yace.”Kanwata ‘karbi kudin nan ku hau abun hawa, kinji ko abokina nada uziri shiyasa amma da da kaina zan dauke ku na kaiku har gida.” Hannu na rawa Rashida tasa ta kar’bi kudin tana godiya ta kalli Ahamdu tana fadin”Mungode sosai Allah ya saka da alkairi.” A nutse ya dago kanshi yana kallonta, itama ta shiga shock ganin fuskarshi, Yace.”Ki godewa Allah.” Sai ya mai da kanshi ‘kasa, Khalifa ya kunna motar yana fadin”A gai da gida ko.” cikin nauyin baki tace”Mungode.” ta bar jikin motar, sai da motar ta bar gurin sannan ta wuce cikin sanyin jiki ta nufi inda Wasila ke tsugune kusa da wata bishiyar darbejiya kanta na kasa gabanta sai faman faduwa yake tana fadin”Innalilihi wa’ina ilaihi raji’un a zuciyarta.
Ba cinye wa bace ba kuma burgewa bace ki dinga cushe cushen maganin matsi a matantakarki, ruwan d’umi kawai ya isa ya sanya gabanki ya matse ko da kuwa kinyi haihuwa goma ne, yana da kyau idan kin haihu a gida kije asibiti domin a duba matantakar ki ko kin samu matsala a gyara miki in kika zauna a gida bakije asibiti ba, akwai matsala idan kin ‘karu guri ya had’e a haka mijinki ya shiga yaji kwararo! shikkenan kuma matsala ta afku a tsakaninku????????♀️
Littafin na kudi ne……![13/08, 6:37 pm] +234 906 803 2427: ‘Yr Bngr Sys
53
Malam mai allo na shirye shiryen tafiya tsangayarshi, su Ahamdu suka sauka a garin……Tanimu d’anshi na biyu shine ya shaida masa zuwan ba’kin, Ya fito cikin babbar riga da koren rawani a nannade a kanshi, ganin su Ahamdu tsaye jikin motarsu ya sanya ya washe bakinsa, ya shiga yi musu barka da zuwa yana fad’in”Gwara da Allah bai sa na fita ba, dama yanzu nake shirin fita gurin karatu da sai da muyi sa’bani sannuku da zuwa sannuku.” Cikin gidan suka nufa akwai wani babban zaure a soro wanda yake saukar baki a ciki dama kullum sai Bitan ta shiga ta gyara ta kunna turaran wuta dan haka ma yanzu dakin sai kamshi yake yi, Ahmadu da khalifa suka zauna……Malam mai allo ya zauna kan buzunsa yana fad’in”Wallahi ko jiya sai da nayi zancen ku nake cewa Hajara da Bittan su shirya suje suga dakin yarinyar nan akwai kuma ‘kwan zabi dana aje mata sunanan da yawa nace su tafi mata dashi ta soya tunda nasan in tazo nan garin tana yawon soyawa taci.”
mirmushi kawai Ahamdu yay yana tausayawa mutumin bai ce komai ba ya shiga gaisheshi ya amsa cikin walwala da farin ciki kai kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki….suka gaisa da khalifa cikin farin ciki da barkwanci kafin ya tashi da sauri yana fad’in”Bari nasa bitan ta kawo muku abinci da ruwa.”
Yana fita dakin yay shiru Khalifa yayi gyaran murya yana kallonshi yace.”Yanzu baka tausayawa wannan mutumin ba! ya kake tsammanin zaiji idan ka sanar dashi abinda ka aikata dan Allah ka janye kudirinka ka kudurta a ranka ka mayar da ita, kar ma ka fada masa komai kawai kace kazo gaisheshi ne.”
Shiru kawai yay baice komai ba, a zahirin gaskiya mutumin ya bashi tausayi sosai yasan zai shiga tashin hankali mutukar yaji da abinda yake tafe dashi, ammafa duk da hakan baya tunanin yanje kudirinshi shi kanshi a yanzu ya rasa wace irin ‘kiyayya yake wa yarinyar sam yanzu baya ma so a dangantashi da ita, dan haka gwara kawai ya sanar mishi da abinda ke faruwa hausawa nacewa ta inda aka hau tanan ake sauka.
Malam mai allo ya shiga dakin yana gyara babbar rigarshi, sai fara’a yake yace.” Kamar na sani yau na tashi Tanimu da sassafe ya tatso nono ashe ina da baki kai masha Allah naji dadin zuwanku Ahamdu.” Yafada yana gyara zamanshi kan buzunsa…..Bitan ce ta shigo hannunta rike da wata kwarya me zane zane da fefe a samanta da ludai guda biyu tana fadin”Sannunku da zuwa.”Khalifa yay saurin kar’bar kwaryar furar yana amsawa, ta dan tsuguna gefe tana gyara lullu’binta suka fara gaisawa, Ahamdu duk nauyi da kunya ya isheshi ganin yanda mutanan ke rawar jiki a kansu, Bitan na kokarin fita Kawu Habibu da Haraja suka shigo suma suna cike da murna da farin ciki, Mai allo ne ta tura danshi, Tanimu yaje ya sanar musu da zuwan su…..Suka gaggaisa cikin mutunci da mutuntawa Ahamdu duk jikinsa yayi sanyi da karamancin mutanan, Mutanan nada kirki da mutunci da kara babu shakka da karamcinsu Wasila ta dauko to da taji dadi, wannan mugun halin mybe daga can dangin uwarta ta daukoshi, abinda yake ta fada kenan a zuciyarsa……Khalifa ne ya iya shan furar shi kam ko ludai daya bai sha ba, tun daga sannan mai allo yasha jinin jikinshi dan bai san Ahamdu da irin wannan fuskarba babu walwala babu sakewa tun dazu suke hira da khalifa yayi shiru abinshi sam ba’ayin doguwar magana dashi zaiyi shiru mai allo jikinsa yay sanyi sosai,
Gyaran murya yay ya mai da hankalinsa kan Ahamadu yace.”Jikina na bani akwai babban al’amarin dake tafe daku dan hauwasa sukance labarin zuciya a tambayi fuska hakikanin gaskiya alhaji Ahamdu ba haka nasan fuskarka ba, a sanin da nayi maka kai mutum ne mai walwala da sakakkiyar fuska ina fatan ba wani laifin wannan yarinya tayi maka ba, dan dama kullum cikin addua nake ubangiji Allah ya zaunar da ita dakinta ya kareta daga rudin duniya dana mahaifiyarta.”
Khalifa dai ‘kas yay da kanshi kunyar had’a ido yake da mai allo din da kaninshi Habibu, dan yanzu da ya sani ma yake da bai rako ahamdun ba sam baya son abinda zai daga hankalin mutane……’Dan numfashi ya sauke a hankali kafin yay gyaran murya yace.”To Alhamudullihi arrama! naji dadi da ka dan fuskanci wani abu daga kallon yanayi na, Da farko dai kaine ka bani auran wannan yarinyar ni kuma biya sadaki na kar’ba bisa amana, to wani babban dalili ya sanya na yanke hukunci a kanta wanda nasan ba zai maka dadi ba, kayi hakuri haka Allah ya kadarta bazan boye maka ba Allah ya gafarta malam naso na rike amanar da ka bani amma zuciyata ta’ki aminta, da hakan…….Wannan yarinya tayi min abun da ya sanya naji na tsaneta gabakidaya bani son ganinta cikin gidana, ba kuma na son cigaba da zama da ita a matsayin matata, dalili kenan da ya sanya ni na saketa saki day……..Kafin ya ‘karasa mai allo yayi saurin fadin kalmar “Innalilhi wa’ina ilaihi raji’un!!!! Ahamdu yayi kasa da kanshi, mai allo ya shiga goge zufa da babbar rigarshi gumi ne kawai yake karyo masa,