NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Saboda yanayin yanda takejin rashin ‘karfi a jikinta ya sanya ta nemi guri ta tsuguna Rashida tabi layin kar’bar kati ta kar’bo mata kana ta mike suka kama layin ganin likita………….Dr nayi mata kallon farko ya gane tana jin jiki saboda ya hango rashin wadataccen jini a tare da ita da damuwa da kuma rashin bacci! Ya tambayeta abinda ke damunta, nan ta shaida masa cikinta ne ke mata ciwo sosai sai kuma zazzabi da jiri! Dr yace.”Kina da ciki ko.”? Daga kanta tayi hawaye na kokarin zubo mata…..Rubuce rubuce yay jikin wata farar takardar yace.”Maza kije kiyi scanning yanzu ki kawo min.” Ta kar’ba ta mike a hankali ta fita…..Rashida na tsaye jikin wata bishiya ta hango fitowarta ta karasa tana tambayar ta tace”Rashida muje lamco de yace sai nayi scanning! Rashida taji kwallah na kokarin zubo mata a idonta tace”Anti Wasila Allah ya rabaki da wannan cikin lafiya yana baki wuya Wallahi.” Girgiza kanta tayi ta sanya hannu ta d’auke hawayen da ya sauka kan kuncinta cikin zuciyarta tace”Ameen.” suka kama hanya suka fita wajen asibitin inda gurin Scanning din yake…….Allah yaso ta sako dubu biyu da dari biyar cikin jakarta shiyasa komai yazo da sauki…..Suka shiga gurin suka kama layi….Mai siyar da pure water ya kawo mata keda hufu ta siya a take ta shanye uku ta bawa rashida daya tasha….Kamar jira ake tasha ruwan mararta ta shiga wani irin juyi tana murd’a mata sosai takeji zafi zufa! sai yanko mata takeyi, cije bakinta take tana kiran sunan Allah har layi yazo kanta ta mike da kyar ta shiga dakin scanning din da kyar ta hau gadon……tana cijewa da daurewa gami da kiran sunan Allah aka ga mai mata ta sauko, a hankali ta gyara zaninta ta karbi sakamakon ta fita tana cire ‘kafafu da kyar……Rashida ta rike hannunta suka fita, a hankali a hankali suke tafiya har suka isa gate din shiga cikin asibitin…..dai-dai lokacin kafafunta suka ri’ke gabakid’aya ta kasa d’agasu! Salati ta soma sai ta tsugune! a gurin tana kiran sunan Allah, Rashida ta tsuguna kusa da ita tana kuka hannunta gam! gam! da nata fad’i take “Anti Wasila sannu tashi mu shiga ciki dan Allah kiyi hakuri kinga mutane na wucewa.” Jirkitattun idanunta ta d’ago tana kallonta dasu gumi duk saman goshinta hannunta na rawa tace”Rashida mutuwa zanyiiiii ni ka d’ai nasan irin ciwon da nake ji a marata.” Rashida ta goge hawayen fuskarta hankali a tashe ta soma waige waige a gurin tana neman wanda zai taimaka musu.

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasp numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
BINTA UMAR ABBALE????????????
[14/08, 12:04 pm] Farida Books: ‘Yr Bngr Sys
55
Wata matace ke ‘kokarin shigowa asibitin hannunta rike da kati ta kusa yin tuntu’be da Wasila dake durkushe tana rike cikinta……Da sauri tace”A’a ya kuke zaune anan ko ba haihuwa za tayi ba.”? Rashida ta goge hawaye tace”Ba haihuwa zatayi ba Daga scanning muke shine ta kasa tafiya cikinta ne ke ciwo.” matar tace”To maza kamata muje wancan rumfar ai nan kan hanya ce.”Rashida ta kama hannunta ta dora kafadarta matar ta riko kugunta suka mikar da ita tsaye…….Horn din da ake zabgawa ne ya sanya matar juyawa a fusace tace”Mutane babu uziri shikkenan dan kana cikin abin hawa na ‘kasa bai da ‘yanci sai ai ta zabga masa horn mtsss! ta karashe maganar tana tsaki hade da dan matsawa motar ta kunno kai cikin asibitin………Hafsa dake draving ta dan juyo tana kallonsu, sai kawai idanunta suka saukan Wasila tana sunkuyar da kai hade da rintse idonta…..Da sauri ta samu guri tayi parking ta fito…..Zeey dake kusa da tace”Ki shiga ki fito ni inanan.” Tace”Zeey fito dan Allah Wasila ce matar governor ina tsammanin bata da lafiya fito da sauri.” Zeey tai saurin bude motar ta fito……Suna karasa inda suke Hafsa tace”Sannu Wasila baki da lafiya ne.”? Jin muryar Hafsa yasa tayi gaggawar dago kanta tana kallonta, a hankali ta lumshe ido bakinta ya bushe ‘kamas! ta d’aga mata kai…..Hankali a tashe Hafsa ta kalli Rashida dake share kwalla tace”Kunga likita? kuma meke damunta dan da kagani tana cikin matsala sosai.” Rashida tace”Munga likita har yace taje tai scanning to daga dawowarmu ne sai kuma jikin ya rikice.” Hafsa tace”Muga scanning din.” Ta mika mata da sauri ta bude tana dubawa….Da sauri ta dago tana kallon wasilan Ciki! mamaki takeyi sosai lallai babu yanda Allah baya tsara lamarinshi……Tace”Zeey dan Allah ku kamo ta keda Kanwarta ta muje.” Wayarta tayi gaggawar fito dashi ta soma kiran ‘kawarta dake asibin mai suna Aliya likita ce ta mata, tace”Aliya ganin nan na shigo asibitin ku amma ina tare da mara lafiya.” Aliya tace”Okey ku shigo ofis dinmu ina shirye shiryn tashi ma dan dai kawai kince zaki shigo ne.” Tace”Gamunan.” Har da ita gurin rirrike Wasilan suka mikar da ita tsaye…….Sai me suna fara tafiya jini ya soma zirarowa daga kafafunta…..Salati suka sa Rashida ta dinga kuka tana rirrike wasilan da fadin”Innalilihi wa’ina ilaihi raji’un.” A gaggauce Aliya ta karaso gurin, a take sukayi gaggawar dora wasila kan wani keke kai tsaye dakin ‘yan ‘bari Aliya tace a nufa da ita…..Hafsa Rashida hankalinsu yayi masifar tashi…..Hannu na kyarma ta kira wayar Khalifa ta shiga shaida masa halin da ake ciki….Lokacin ma yana hanyar zuwa gidan abokin nashi dan haka kawai sai ya juya akalar motarsho zuwa asibitin

Kasancewar sun tari al’amarin da gaggawa ya sanya suka samu nasarar tsayar da zubar jinin dake barazana ga d’an tayin dake kwance a mahaifarta…..Sistar Aliya ta fito daga room din tana cire safar hannunta, ofis dinta ta nufa nan ta tarar dasu sunyi jugum! ta zauna tare da zare glass din idonta, Hafsa tace”Allah yasa dai cikin nan bai zube ba dan wallahi zubar jinin nan ya tsoratani.” Sistar Aliya tace”Ciki nan daram! ammafa Allah ne kawai ya kare wallahi dan saura kadan ya zube dan dai munyi gaggawar tarar abun ne da tuni sai da labari.” Hafsa da Rashida suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala….Sistar Aliya tace” Ammafa samun kwanciyar hankali shine dole sai anyi mata daurin mahaifa domin mahaifarta na saurin budewa, ko tana aiki karfi ne.”? Da sauri Rashida ta girgiza kanta, Sistar Aliya tace”Tun bayan sati uku da suka gabata mahaifarta ta bude sakamakon aiki ko duguwar tafiya mai tsayi Allah ne kawai ya tsare wannan cikin ni nayi mamaki wallahi.” Hafsa tace”Naji dadi sosai kawata babu damuwa za’ayi komai indai cikin zai zauna ka kira Abban Afnan yanzu zan shigo.

Aliya tace”Wai ya kuke da itane naga duk kin tashi hankalinki.” Tace”Matar Abokin Abban Afnan ce muna shiri da ita sosai.” Aliya tace”Okey naji kince Khalifa zai zo ina mijinta.” Tayi saurin fad’in “Yayi tafiya ai kuma amanarta na hannun khalifa kinga dole ya kula da ita.” Aliya tace”Dole kuwa tunda shi aka bawa amanarta….Scanning din take dubawa tana girgiza kanta tace” Gashi cikin yayi kwari wata uku da sati biyu.” Hafsa ta shiga tunani, Eh tabbas hakan zata iya faruwa tunda satittikan cikin yayi dai-dai da lokacin auransu.

Khalifa ne ya shigo cikin asibitin, ya kira wayar matarshi, ta fito daga ofis din Aliya ta masa jagora har dakin da Wasila ke kwance ita kadai ce ba a dakin babu kowa tayi zuru zuru da ita sai nadamar rayuwa takeyi lallai ‘yaya mata na cikin hadarin rayuwa idan suna da ciki, wahalar da ta shiga dazu ta bata tsoro tayi tunanin ma mutuwa zatayi dan lokacin da taga jini ya soma zuba daga jikinta hankalinta yayi masifar tashi……Shigowar khalifa dakin ya sanya ta sunkuyar da kanta kwalla na taruwa a idonta….Khalifa ya karasa bakin gadon zuciyarsa duk ta karye tausayi kawai yaran suke bashi, A nutse sistar Aliya tayi mishi bayani tace” Tana jiran Dr Alfindiki ya fito zasu shiga da ita teatar room domin ayi mata aiki, bai wani tsaya dogon tunani ba ya sanya hannunshi ya kuma bada umarin a daure mata mahaifar duk domin samun zaman lafiyar cikin dake kokarin zubewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button