YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Uwani ta kalleta ranta ya ‘baci da maganarta amma saboda sanin halinta yasa tace”Eh kuluwa ki daina shakka ko kokwanto Wasila na da ciki amma kuma da Ubanshi.”
Kuluwa ta ta’be bakinta tana fad’in “To yanzu naji zance Allah ya rabasu lafiya sai ki kira su kuci abinci gashinan babu yawa dai aci da hakuri tunda ban san da zuwanku ba.” Uwani tace”To mungode.” Kuluwa ta fita daga dakin, tana gyara daurin zaninta wanda yayi da’kal! da’kal da daud’a!
Uwani ta le’ko tana kiransu Wasila dake zaune jikin bishiyar darbejiya dake gidan………Rashida da kyar ta lalla’bata suka koma dakin….suna shiga ta fito da sauri tana fad’in “Rashida ba zan iya ba wallahi mutuwa zanyi zuciyata tashi takeyi.” Karaf a kunnan Kuluwa cikin fusata tace”Ke! buhun ubanki nace! Buhun ubanki kaji min shegiyar yarinya ciki haukane da zaki zo min gida kina min iskanci! har ki dinga cewa zuciyarki tashi takeyi to bari malam ya shigo wallahi kinji na rantse ba zaki zauna min a gida ni ba’a kawo min iskanci ehe! dama ai baku bane tilashin mu ita Uwanin itace tilas dinmu dan haka sai ku koma inda kuka fito abin arziki baya zama na tsiya.” Takarashe maganar tana kumfar baki kai daka ganinta a fusace take! Uwani ta fito daga daki tana bata hakuri saboda tasan halin ta zata iya cewa su Wasilan baza su zauna a gidan ba kamar yanda ta fad’a, Hakuri take bata tana karyar dai muryarta sai rawa take! Kuluwa ta cigaba da aikinta tana sababi! da zagin Wasila
Uwani ta dauko langar abinci ta dire a gabansu tana fad’in ” Ku kiyaye da wannan matar idan kuna son zaman lafiya bana son abinda kikeyi Wasila kinga bamu da gatan da yafi nan, Kuluwa macace mara hakuri zata iya sa Kawu yace ku bar mishi gida kamar yanda ta fad’a saboda haka duk abinda zakiji na tashin zuciya ki dinga daurewa kina hakuri haka take muguwar kazama ce tun tana da kuruciyarta gashi har girmanta……Wasila bata iya magana ba rashida ce mai magana tace”Gaskiya Uwani gidan nan baiyi wallahi duba fa ki gani ko ina kazanta da kashin dabbobi dubi bandaki babu kofa sai buhu kiji warin masai dake tasowa har nan kawai mu zamu tafi Garko ke kiyi zamanki nan tunda kece tasu.”
Uwani ta marairaice fuskarta muryarta na rawa tace”Rashida kin san yanda nake son ku kuwa ? bana so kuyi nesa dani shiyasa na’ki aure na ‘kare rayuwata tare daku, ina ‘kaunarku saboda nasan bani da kowa sama daku, Uwata ta mutu Ubana ya mutu mijina ya mutu sai ku kawai nake kallo naji dadi idan kuka tafi Garko kuka barni wace irin rayuwa kuke tunanin zanyi a cikin garin nan.”!?
Tausayin mahaifiyar tasu ne ya kama su, sai suka hau goge hawaye, suna adduar Allah ya kawo musu dauki da gaggawa amma hak’ikanin gaskiya mahaifiyar tasu tasha wuyar rayuwa ta kuma yi wahala dasu bai kamata su guje mata ba,
Zama tayi kusa dasu tana bud’e langar abincin aikuwa sai wani irin towon dawa ba’ki’kikirin yayi musu sallama! towon sai shaining yake ga wata uwar miya kamar fitsarin jaka, sai wake guda guda a cikin miyar tana ta warin daddawa……A guje Wasila ta mike ta nufi bakin rariya ta dinga kakarin amai tana zubar da kwalla! Kuluwa tayi azamar fitowa daga kicin da ludayi a hannunta….Wannan karon Uwani da kanta taje ta rirrik’e ‘yar tata tana mata sannu ita kuwa sai rike ciki take tana mur’kususu da kiran sunan Allah! Kuluwa ta dinga kallonsu bakin cikin duniya kamar ya kasheta ‘Kwafa tayi ta koma kicin din! Yau ba gobe ba zasu bar mata gidanta dan bata ciki da iskanci da wulakanci……Kawu Madu ya shigo gidan yana sa’be babbar riga sai kawai ya gansu cirko cirko Uwani da Rashida kan Wasila dake durkushe tana kakari……Yace.”A’a Uwani meke faruwa ne Me yasa me ta take amai haka.”? Kafin Uwani tace wani abu Kuluwa tayi zuruf ta fito daga kicin fuskarta a murtuke tace” ‘Kyankyamina takeyi shine take amai tunda suka shigo gidanan basu shiga dakina ba can bakin bishiya suka zauna saboda suna kyankyamina saboda haka yau ba gobe ba zasu bar min gidana dan wallahi ba zan dauki wannan iskancin ba.” A take Kawu Madu ya sha kunnu yana kallonsu rai a bace yace.”Ashe baku da tarbiya dama? matar tawa kuke ‘kyankyami!? to shikkenan dama ai baku ne tilas dina ba Mahaifitarku ce saboda haka zaku bar min gidana tunda baku da mutunci.” Uwani ta shiga share hawaye tana fad’in “Kawu ba haka bane wallahi yarinyar nan nada ciki mai laulayi yana bata wuya dama tun a mota take amai har yanzu ba wai suna ‘kyankyamin Kuluwa bane.”
Yace.”Uwani.”! ta amsa yace.”Shin yaushe kikayi wa yarinyar ki aure babu labari gashi nace tana da ciki.”! Kuluwa tace”Nifa malam ban yarda ba wallahi wannan yarinya cikin shege tayi shine suka kwaso jiki suka gudo nan sabida gudun abin kunya dan haka wallahi ba’a gidan nan ba idan kuma kace tilas sai sun zauna to ni zan fice na baku guri.”
Hankalin Kawu Madu ya tashi, Yace.”A’a ba za’ayi hakaba Kuluwa ai duk wannan magana ma bata taso ba, ke Uwani zo ki zauna kiyi min bayanin abinda ke faruwa.”
Uwani ta bishi kan tabarma suka zauna tare Kuluwa ta ‘karaso gurin hannunta rike da ludayi ta zauna kujera ‘yar tsugo tana fad’in “Eh ai gwara muji bayanin komai domin mu samu kwanciyar hankali.” Uwani ta share hawaye a hankali ta soma warwarewa masa abubuwan da suka faru da rayuwarta ita da ‘yayanta komai bata rage masa ba sai da ta fad’a mishi……Kuluwa tace”Duniya kenan yanzu ke Uwani bakiji kunya ba, wato lokacin da kuka samu kudi kuka samu dad’in duniya baki tuna damu ba sai da wahala ta taso ki sannan zaki tuna damu ki kwaso jiki ra’be ra’be da ‘yaya kizo ki d’ora mana nauyi to ba zata ta sa’bu ba! Mu ba zamu dauki nauyin ki kuma mu d’auki nauyin ‘yayanko ba, Dan haka gobe gobe yaran nan zasu bar gidanan suje can dangin mahaifinsu tunda suna raye, kema abinda yasa ba zamu kore ki ba saboda mun san ko kinje can gidan Kawunki ba zai kar’be ki ba saboda haka ke kad’ai zamu ri’ke saboda kece tamu.”
Kawu Madu yace.”Kwarai kuwa Kuluwa wannan magana taki gaskiya ce, Yaran nan baxa su zauna mana a gida ba sabida bamu da hakki a kansu dan haka kamar yanda kika fada hakane kwana guda zasuyi su bar mana gida suje can cibiyarsu………Uwani ta dinga kuka tana fad’in “Haba Kawu ku duba al’amarin fa kada kuyi min haka bani da kowa sai ‘yayana bani da uwa da uba bani da miji sai ‘yayana su nake gani naji sanyi a raina.” Kuluwa tace”To ai tunda hukuncin da muka yanke bai miki ba to sai ki bi ‘yayan naki haba! wannan ‘kulafucin son ‘yaya dame yayi kama.” Ta mike tana jan tsaki ta shiga dakinta…..Kawu Madu ma ya mike yana fad’in “Na fad’a miki Uwani na yanke hukunci Kuluwa ta yanke hukunci saboda haka shawara ta rage gareki.” Ya buge babbar rigarsa ya ‘kara gaba.
Wasila da Rashida kam! basu ciwo ba dalili dama sunfi son su tafi can garkon shiyasa sukaji dadin hukuncin da Kawu madu ya yanke a kansu amma basu nunawa mahaifiyar tasu ba, sai suka shiga kwantar mata da hankali da fad’in ko sun tafi insha Allahu zasu dinga zuwa a kai akai suna dubata…..Uwani dai jinsu kawai takeyi abin duniya ya taru yayi mata yawa bata ta’ba nadamar rayuwa ba irin yau.
Kuluwa ta dinga shige da fice a tsakar gidan tana sakin ‘ba’kaken maganganu wanda ya sanya jikin Uwani yi sanyi taji a zuciyarta gwara kawai su Wasila su bar gidan dan ba zata iya jurar rashin mutuncin kulawa tana aibata mata yara da kiransu karuwai watarana tana ganin zata iya mayar mata da martani kan maganar da takeyi, ta dinga jin wani irin d’aci! da bakin ciki a raina ashe haka abun yake da ciwo a duk sanda aka danganta d’anka da wannan suna (karuwai) gaskiya ta gode Allah da ya bata ‘yaya masu hankali da hange nesa tasan da bada hakan ba da tuni sunanan da kuluwa ke kiransu dashi ya tabbata tunda ita da kanta ta dinga turasu karuwancin, tagode Allah da yasa wannan cikin dake jikin Wasila ta sameshi ta hanyar halak ba haram ba.