NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Girgixa kanshi ya shiga yi yace.”Ban san a ina zanga ‘kawarta ba mybe a samu wani labari a gurinta.” Khalifa yace.”Eh to ai kuma inda za’a sameta ne aiki.” Yace.”Zan duba wayarta baza’a rasa numbar ta ba.” Khalifa yace.”Yawwa hakan yayi kyau Allah yasa a dace yanzu dai ka kwantar da hankalinka mu shiga ciki kaci abinci ka huta tukkuna insha Allahu komai zaizo da sauki.”

Girgiza kai kawai yay yace.”Khalifa hankalina ba zai ta’ba kwanciya ba sai naga yarinyar nan, na ‘kwallafa raina kan cikin jikinta burina kawai in ganta kuma in tabbatar lafiyar abinda ke cikinta.” Khalifa yace.” Shine ai nace damuwa da tashin hankali bashi ne mafita ba addua itace mafita kawai ka kwntar da hankalinka ka cigaba da addua.”
Murmushi mai ciwo yay khalifa bai san yanda yake ji a zuciyarsa ba shiyasa yake cewa ya kwantar da hankalinsa a maganar kwanciyar hankali ta ‘kare a gurinsa yanzu mutukar ba ganin yarinyar nan yayi ba. A
Tare suka fito daga motar tamkar wanda ‘kwai ya fashe musu a ciki suka nufi cikin gidan. ga gajiya ga rashin samun nasara.


Dake akwai tafiyar ‘kafa tsakanin bakin titi da cikin ‘kauye yasa suka samu babur irin na (kafu-kafu) ya shiga dasu ciki har ‘kofar gidan Mai allo aka ajesu, kana suka biyasu hakkinsu…..Suna kokarin shiga gidan ya fito da cazbaha a hannunshi, kawai sai yay tozali dasu. Ya bude baki yana kallonsu cike da mamaki.
Idanun Wasila ya kawo ruwa rau-rau! ranar naka sai naka! Wai itace tazo garin Garko da ‘kafafunta! Hawaye suka zubo mata a kumatu, kai a ‘kasa suka isa inda yake suka zube gwiwa bibbiyu suna kuka! Tausayinsu ya kamashi da sauri yace.”Ku tashi mu shiga ciki.” Jikinsu a sanyaye suka mi’ke rashida taja akwatin kayan nasu suka bi bayansa.

Kamar dai koda yaushe Bitan na zaune a tsakar gida tsaf da ita jikinta sai kyallin mai yake da alama bata jima da yin wanka ba tana sanye da wani leshi ruwan ganye(kore) irin nada ta d’aure kanta tamau! da dankwalin leshin, cinyar ta farantin shinkafa ne tana tsincewa sai kawai ta tsinkayi muryar mijin nata yayi sallama, Da sauri ta d’ago kanta tana kallon bakin ‘kofa, Yanzu yanzu ya fita ko mantuwa yay abinda take ayyana cikin ranta, sai kuma taga su Wasila a bayanshi.

Tace”A’a malam su wa nake gani a bayanka yau.”? Yace.”Gasunan nima fita ta na hango zuwan su Wasila ce da Rashida.” Bitan! ta ri’ke ha’ba babu yabo babu fallasa a fuskarta tace”To masha Allah sannunku kuzo ku zauna ga gurin zama.” Mai allo yace.”Kuje ku zauna.” Sukaje suka zauna kusa da ita sai sunkuyar da kai suke mussaman Wasila dama itace akuyarta tayi kuka a garin…..Mirya na rawa tace”Kawu ina wu

ni mun sameku lafiya.” ? Yana daga tsaye yake amsawa yana nazarinsu….Rashida ma ta gaishi ya amsa, kana suka shiga gaishe da bitan itama ta amsa cikin kulawa kafin ta mike a nutse ta nufi kicin….Mai allo ya dinga kallonsu zuciyarsa na karyewa ‘yayan Yahuxa tamkar ‘yayan cikinsa suke, duk yanayin da ya gansu na dad’i ko na rashin d’ad’i dole ya shiga damuwa, kallon farko da yay musu ya fahimci akwai damuwa da firgici a tartare dasu mussaman Wasilan da tayi firgai firgai da ita kamar ma mara ‘koshin lafiya. Bitan ta fito daga kicin hannunta rike da samira mai hannun roba, ta aje a gabansu ta koma kicin din da sauri ta fito hannunta rike da wani farin jug ta bude randa ta debo musu ruwa ta aje a gabansu ta zauna tana fad’in” Kuci abinci kunji ko ku daina kuka da damuwa rayuwar nan kowa hakuri yake da ita.”

Malam yay gyara murya yana kallon matar tashi yace.”Zan fita kamar yanda na niyyata idan Allah yasa na dawo sai na zauna dasu, Insha Allah.” Bitan tace”To malam ubangiji Allah ya tsare a dawo lafiya.” ya amsa yana kokarin fita, Wasila da Rashida har rige rige suke gurin yi masa adduar dawowa lafiya ya amsa musu a lokacin da yake kokarin fita daga gidan.

Bitan taga sun kasa cin abincin tace”Ku saki jikinku fa kuci abinci insha Allahu ba zaku samu wata matsala dani ba, ni dama tuntuni ina tausayawa rayuwarku mutukar kun gane gaskiya kuma kun gana mahimacin Kawunan ku a gurin ku , ai magana ta wuce suma kansu Kawunan naku hankalinsu a tashe yake, amma nasan yanzu hankalinsu zai kwanta tunda kun dawo garesu.”

Sai suka sake jin kwarin gwiwa a tare dasu, Rashida ta bude samirar abincin dake gabansu, burabusko ne (biski) yayi shar shar dashi sai kamshin man’kuli zuryan yake, ga maggi star guda biyu a gefe da yaji….Wasila taji yawunta ya tsinke sosai taji sha’awar cin burabuskon ta mike a nutse ta wanko hannunta, ta dawo ta zauna Rashida ma mikewa tayi taje ta wanke hannunta sukayi bisimillah tare da fara cin abincin.

Bitan ta mike a nutse ta shiga kicin ta kunna wuta, Girgi zata dora musu na mussaman, sabida yaran sun bata tausayi sosai da sosai sam basuyi sa’ar uwa ba duk wata wahala da suka shiga mahaifiyarsu itace sila shiyasa kwata kwata basa shiri da ita sabida munanan haleyenta gashi tayi ta zagin mijinta a gabanta, duk abinda za tayi wa yaran za tayi musu ne saboda Allah da kuma maraicinsu, ba dan halin Uwarsu ba..
Tas suka cinye burabuskon basu rage komai ba, Wasila tafi rashida ci dan daga karshe ma rashidan cire hannunta tayi ta bar mata ta ‘karasa cinye tayi gatsa tana hamdala hankalinta ya kwanta sosai da tsabtar Bitan shiyasa kome ta girka ta bata zata iya ci……Bitan ta fito daga kicin hannunta rike da wani ma dai-dai cin kwando dafaffan ‘kwai ne a ciki da yawa ta aje a gabansu tace ku ‘kara da wannan yanzu zansa yara sunyi min cefene na sake dafa muku abinci. “Wasila tayi murmushi tana fad’in ” Bitan mungode Allah ya saka miki da alkairi.” Murmushi kawai tayi ta koma kicin tana cigaba da aike aikenta.

Hajara ce tayi sallama ta shigo gidan tare da d’an autanta Lamir yana biye a bayanta…….Tsayawa tayi bakin kofa tana kallonsu, Sunkuyar da kai sukayi kamar munafukai. Bitan ta fito daga kicin taganta tsaye a bakin kofa tace”Ki shigo mana ai ba abin mamaki bane addua bata fad’uwa ‘kasa banza.” Hajara tace”Ai dole nayi mamaki Bitan! Yaushe suka zo kuma.”? Bitan tace”Ke dai shigo ki zauna.” Hajara ta karasa kan tabarmar ta samu guri ta zauna idanunta a kansu Wasila ta dinga tunano rigimarsu da Hajaran tana shan duka a gurinta a duk lokacin da sukazo garin, dan kwata kwata basa shiri sunfi shiri da Rashida……Cikin jin nauyi suka gaisheta ta amsa tana fad’in “Kunga uwar bari kenan.”!? Sukayi ‘kus! kansu a ‘kasa, Hajara zata fara sababi! Bitan ta dakatar da ita da fad’in ” Haba Hajara wannan ba kana bane! Kullum fa addua kuke kan Allah ya karkato da hankalin yaran nan gareku Allah kuma ya amsa adduarku sannan kice wani abu, don Allah kar ki fad’i wata mummunar magana kan yaran nan ki kyalesu ma suji da abinda ya damesu.

Hajara ta fashe da kuka tana fad’in “Haba Bitan! al’amarin nan fa akwai dam

uwa da ba’cin rai wallahi yaran nan sun sanya mu a fargaba da tashin hankali mussaman waccan mai ‘katon kan tana sunkuyar da kai munafuka kawai Ai dama nace duk sanda kika kwaso kafafunki kika zo sai na ci miki mutunc…….Bitan tace” Ashe bakiji maganata ba kenan haba hajara.”? Hajara ta kwance bakin zaninta ta goge hawayen fuskarta tana fad’in “Allah ya ji’kan ka Yahuza.” Ai sai Wasila da Rashida suka sa kuka! Suna bata hakuri! Takaicin duniya ya ishi bitan Hajara tazo ta dagula al’amari ta tayarwa da yara hankali sai koke koke sukeyi……To itama hajaran da taga sun ki su daina kukan sai ta shiga rarrashinmu itama ba yin kanta bane tunawa tayi da d’an uwanta….Rashida da Wasila suka dinga bata hakuri da fad’in “Insha Allahu baxa su sake guje musu ba tunda sun gane basu da kowa a duniya da wuce su……Hajara taji dad’in wannan magana tasu sai tace ” Komai ya wuce insha Allahu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button