YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Hajara bata koma gidanta ba har sai da malam mai allo ya dawo suka gana da juna sannan tayi musu sallama ta tafi gidanta da al’kwarin dawowa gobe idan Allah ya kaimu.
Bayan sallahr isha’i mai allo ya samu nutsuwa duk suna zaune a tsakar gida bayan sun gama cin abinci, mai allo ya gyara zamanshi kan buzunsa yana kallonsu a nutse yace.”Naji da dadi kuma nayi farin ciki da har kuka gane mahimancinmu a gurinku, yanzu kun gane cewar baku da wani gata a duniya da wuce Allah da ma’aiki da kuma ni da ‘yan uwana, Mahaifiyarku ta dauke ku ta kai ku can cikin danginta, sun nuna muku cewar su basu da ala’ka daku , kamar yanda kuka fad’a min cewar da kyar ma suka bari kukayi kwana a guda a gurinsu, ni a ganina ba suyi lefi ba kamar yanda kuke tunani sun nuna muku mahimcin danginku ne, me yasa basu kori ita mahaifiyar taku ba? saboda sun san tasu ce kuma bata da wani guri da za taje idan ba gurinsu ba, naji dadi da faruwar hakan, na kuma tabbatar da cewar hakan zai sake sanyawa ku shiga cikin hankalinku ku gane meye rayuwa, alhamdullhi, Allah ne abin godiya a garun mu baki d’aya.” Shuru yayi yana sauke numfashi kafin ya cigaba da magana yana me kallon inda Wasila take zaune, Yace.”Jiya mijinki yazo garinan cikin tsananin rud’ani da tashin hankali yana shaida min cewar wai kina dauke da cikinsa a jikinki shin hakane ko ba haka bane? tunda dai ni kafin wannan zuwan nashi wattani uku da suka wuce yazo har nan ya shaida min cewar ya sake ki saki d’aya wanda a lokacin mukayi ta tsammanin zuwanki baki zo ba sai yanzu.
Tun lokacin da mai allo ya firta maganar mijinta yazo taji duk wani kuzari nata ya dauke yawun bakinta ya tsinke gabanta ya shiga fad’uwa da ‘karfi da ‘karfi sai kawai ta soma fad’in kalmar innalilihi cikin zuciyarta, muryar mai allo ce ta dawo da ita hayyacinta yace.”Ke nake sauraro Wasila.” Ta d’ago kanta idanunta cike da ‘kwalla tace”Eh Kawu in da ciki.” Yayi jim! kafin yace.”To masha Allahu, yanzu akwai aure a tsakaninku kenan? ko ku kuma bayan rabuwarku dashi cikin ya bayyana kanshi.”? Ta goge hawayen dake kuncinta tace”Bayan mun rabu cikin ya fito.” Shiru yayi yana girgiza kanshi kafin yace.”Gaskiya mana, yazo nan hankali a tashe a jiyan ni har na soma tunanin ko da akwai aure a tsakaninku ashe shi saboda cikinsa ya biyo bayanki, to babu lefi ai idan Allah yasa Habibu ya dawo daga tafiya, tunda shine yake da numbar wayarshi sai ya kirashi ya shaida masa abinda ke da akwai, amma maganar zai daukeki ya killace ki kiyi mishi rainon ciki duk bata taso ba, anan ma zaki raini ciki ki kuma haife lafiya ba tare da wata matsala ba insha Allahu, wannan dai hakkinsa ne dole a fad’a mishi halin da kike ciki duk saboda jininsa da kike dauke dashi a jikinki.” Kuka tasa tana fad’in “Dan Allah Kawu kar a fad’a masa bana so kawai a bari idan na haihu sai a bashi d’anshi Ni bana so yazo inda nake.” malam ya shiga kallonta yana mamakin gursheken kukan da take.
Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
60
Mai allo ya dan gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace.”Kiyi shiru ki kwantar da hankalinki ki daina kuma kuka, sanar dashi ba yana nufin cewa zaki koma gidanshi bane, A’a za sanar mishi ne domin fita hakkinshi, ba wai dan muna neman wani abu a gurinshi ba, yana da kyau ya san cewar har yanzu kina nan dauke da cikin nashi, kuma ya samu nutsuwar zuciyarshi, ni ba zanyi miki dole ba kamar yanda nayi a farko, ba zance tilas ki koma domin ki cigaba da zama dashi ba, zaki zauna ki samu nutsuwar zuciyarki ki haihu lafiya kana ki za’bi namijin da yayi dai-dai da rayuwarki ki aura.”
Bitan tace”Wannan magana da kayi itace mai kyau, saboda haka ki daina kuka kuma ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali ko dan saboda cikin jikinki insha Allah babu wanda zai miki tilas kan ki koma zama gidan shi tunda bakyaso to Allah ya za’ba miki abinda yafi alkairi.” Wasila ta shiga goge hawayenta tana sauke ajiyar zuciya, Bitan ta mike ta nufi wani daki minti biyu ta fito daga dakin hannunta rike da fitilar kwai ta gyara a nutse ta gyara fitilar ta kunna ta koma dakin…..Kimanin minti goma tayi a ciki ta fito tana fad’in “Na gyara muku shimfida sai ku kwanta ku huta mussaman ke Wasila naga alamun gajiya a tare dake kiyi bacci sosai sai ki samu sassauci da nutsuwar zuciya.” Suka mike a nutse suka shiga dakin……….Bitan ta zauna kusa da mijinta suka cigaba da tattaunawa dangane da al’amarinsu Wasilan.
Dakin na shimfide da lede sabuwa da lalubewa masu dan kauri sai katifa ma dai-dai ciya mai cin mutum biyu jakar kayanu ajiye a gefe, dakin dai ya ishesu su biyu ba tare da wani ya takurawa wani ba…..Wasila ta cire hijab din jikinta, ta janyo akwatin kayansu tana dubawa kaya mara sa nauyi zafi takeji idan da son samu ne ma ta watsa ruwa, saboda zafin da takeji, Da kyar ta samu wasu riga da wando irin marasa nauyi sosai ta saka a jikinta, ta nemi ta gyara tufkar gashinta, Rashida dake kokarin kwanciya kan katifar tace”Anti Wasila ni kuwa zan baki shawara.” Ta kalleta tana fad’in “Wace irin shawara.”? Rashida ta mi’ke zauna a hankali tace” Dan Allah ki koma gidan Ahamdu wallahi shine marufar asirinki yanzu idan kince wani auran zaki sakeyi to ai baki san wanda zaki aura ba, kin san yanzu auranan zamani nan sai a hankali, amma ni ba tun yau ba nake sha’awar auranki dashi wallahi, kuma idan kin duba kinyi tunani fa za kiga bashi da laifi dangane da abinda ya faru a tsakaninku, ke koma yana da laifi to naki laifin yafi nashi, saboda haka nake baki shawara kan dan Allah idan yazo da niyar mai dake gidanshi ki amince kawai ki koma zakiji dadi muma muji dadi.”
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon ‘yar uwar tata tace”Wato Rashida har yanzu kwadayi da hange ne cikin ranki ko? Rashida ta girgixa kanta alamun a’a…….Ta cigaba da cewa”Idan ba kwadayi ba me zai sanya kice min in koma gidanshi? Kince nafi shi laifi Eh na yarda na fishi laifi kuma na amsa laifina amma me yasa lokacin da nayi nadama na nemi afuwarshi bai yafe min ba? lokacin da nake kuka nake neman gafarar shi a lokacin ji nakeyi zan iya zama dashi cikin ko wane hali saboda yayi min hallaci ya kuma yi min abinda ba kowa ne zai iya ba, ni ba nufina a kasheshi ba ko a cutar dashi, amma na lura shi abinda yake zargi kenan……Kinga duk mutumin da yake zarginka hankalinsa ba zai ta’ba kwanciya dani ba, Ni nasan koda na koma gidanshi to koma mu ‘kan’kare za’ayi sabida yana zargina, sannan kuma ni bana jurar wulakancin da raini sam mutumin nan baya ganin mahaifiyarmu da daraja da mutunci ban san dalili ba ko dan yana da kudi ne oho! , naji ciwo sosai ranar da kuka zauna a gidanshi keda Uwani ya wulakanta ku, yana da kudi yana ganin babu wanda ya isa! sannan kice na koma gidanshi, ai ko zan koma auranshi sai ya mutunta mahaifiyata, ballanta ma bana sanyawa zuciyata cewar watarana zan koma gidanshi in cigaba da zama a matsayin matarshi, kawai Allah ya hada kowa da dai dai shi.”
Rashida tace”Wallahi ba Kwadayi bane ni kawai mutumin yake burgeni yana da kirki da tausayin talakawa kinsan dama ance dan adam tara yake bai cika goma ba, kuma ni a ganina ba wai baya ganin girman u



