NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE


Sun shirya tsaf tsaf! shida Hajja suka fito harbar gidan nashi, ya fito da wayarshi yana neman numbar Khalifa sai kiranshi ya shigo da sauri ya kara a kunnanshi Khalifa yace “Anya kuwa tafiyar nan dani za’ayi kuwa! Wallahi Hafsa ce ta tashi da zazzabi me zafi yanzu yanzu zan kaita a dubata muna zargin dai ko an samu ‘karuwa ne.”

Yace.”Ayya! Allah ya sawa’ke! babu matsala bari mu tafi kawai insha Allahu zamu shigo nida Hajjah sai mu dubata.” Khalifa yace.”Okey babu damuwa A mika min gaisuwa gurin aramma.” Yace.”Zaiji insha Allahu.” Yana kokarin kashe wayar ne Khalifa yace.”Allah yasa idan kaje kawai ga mutuniyar taka tana cire kafa da kyar! dan cikin nan yanzu nasan yayi kwari.” Ya d’anyi ya’ke wanda hausawa suke fad’in yafi kuka ciwo “Khalifa bana tunanin akwai cikin nan fa.” Khalifa yace.”Kar ka cire tsammani abokina.” Yace.”To Allah ya amshi adduarka.” Khalifa yace.”ameen ya rabbi sai kun dawo kenan.”? Yace.”Insha Allah.” Kashe wayar yayi ya mayar aljihu kana ya nufi

parking spece lokacin Garba nata ‘kokarin karkad’e mota Hajjah na gidan baya a zaune, kawai shima sai ya bude ya shiga ya zauna kusa da ita, Garba ya shiga ya zauna maxauninshi ya kunna motor a nutse suka fita daga gidan, Yayin da ma’aikatan shi ke faman yi mishi fatan alkairi da dawowa gida lafiya.

Littafin na kudine……!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biyaba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE‘Yr Bngr Sys
61
‘Katuwar tabarma ce shimfid’e a tsakar gidan, Wasila na kwance hannunta rike da mafici tana fifita zafi ake sosai a garin ga dukanin alamu ruwan sama na dab da sauka mai allo yana gefe kan buzunsa da wani ma dai-dai cin allo a hannunshi yana rubutu, Bitan da Rashida suna daga can gefe suna aikin gyara zabbi wanda malam ya sanya d’anshi Tanimu ya yanka su saboda Wasila wai ta dinga samun kuzari da karin jini da lafiya shiyasa ba’a daukar lokaci ake soya mata kaji da dafaffan kwai duk sanda ya fita kasuwar cikin gari kuwa sai ya siyo mata manya manya kifi masu kyau da kara lafiya………Ya d’an kalleta tana kwance tana aikin fifita sai gumi take Yace.”Da alama dai yau garin ruwa ne zai sauka shiyasa zafin ya tsananta da yawa.” mikewa tayi zaune tana gyara daurin dankwalinta tace” Kawu malam Allah zafin nan duk ya gigitani na rasa yanda zanyi.” Murmushi yay yace.”Bake kad’ai ba wasila nima Allah Allah nake in gama miki rubutunan in fita insha iska a waje duba dai dik girman gidanan babu iska ga rana ta game ko’ina.” Bitan dake sauraron hirar tasu tace”Ai idan kaga irin wannan ranar to tabbata ta ruwa ce dan haskenta yayi yawa, dubi gabas ka gani hadari ne sosai shiyasa nake sauri in gama ayyukana kafin ruwa ya sauka.” Wasila tace”Allah gwara ayi ruwan ko a samu sassauci ni akwana ma anayi.” Mai allo yasa dariya yana fad’in “Wato ke kanki kika sani ko? idan anyi an kwana ana ruwa ‘yan kasuwa suce me? wani fa sai ya fita zai samo abinda zai kaiwa iyali.” Tace”Allah Kawu malam zafin ne ya isa Allah na tuba.” Bitan tace”Aike Wasila dole ne kiji zafi saboda lalurar dake jikinki dama haka masu ciki suke da jin zafi.” Tace”Aikam dubi wuyana kuraje duk sun fito, ni ruwan sanyi ma nake so.” Mai allo yace.”Wannan ne kuma baki isa ba! za’ayi miki komai wanda kike so amma banda shan ‘kankanra.” Marairaicewa tayi tace”Kawu malam ba ‘kankanra zansha ba ruwan sanyi fa nace don Allah a taimaka asiyo min.” Shiru yay yana cigaba da rubutunsa, ta dinga magiya tana karyar da kai! Yace.”Bari Tanimu ya shigo.” Da sauri tace”Kawu ka bawa rashida kud’in ai tasan gurin.” Yace.”Bana son aiken rashida gurin nan akwai maza.” Shiru tayi tana had’iyar miyau da kyar ma’kogwaronta duk ya bushe! Kallonta yay ta bashi tausayi kwata kwata yanzu baya so yaga abinda zai ‘bata mata rai ko ya sata a damuwa, ya kalli Rashida dake wanke hannunta bayan sun gama aikin, yace.”Zo kar’bi maza jeki bakin gada gurin masu siyar da ruwan sanyi ki siyo mata kar a bada mai ‘kankara.” Rashida tace “To ta karaso da sauri ta ‘karbi kudin, hijab tasa ta kama hanya ta fita bayan ta dauki wani jug mai dan girma.

Tana fita dalleliyar motarshi ta karyo kwana zata shigo cikin layin……Yara yaran dake wasa a bakin hanya suka watse suna ihu da bin motar da kallo, Rashida na tsaye a bakin kofar gidan motar tayi parking a wani fili dake gefen gidan…..Wucewa take kokarin yi yay gaggawar bud’e motar ya fito gabanshi na wani irin fad’uwa, babu abinda yake fad’i cikin zuciyarshi sai alhamdullihi.”!!! Rashida tayi saurin dafe kirjinta tana kallonshi Sai kuma ta washe baki wanda kana ganinta kasan tana cikin farin ciki…….Garba ne ya bud’ewa Hajja mota ta fito tana mita da fad’in ” Zaman mota ai sai ya saka ciwo tafiya ba tafiya ba ‘kafafuna duk sunyi tsami.” Hannunta ya d’an ri’ke kana ta gyara sa takalminta da lullubin mayafin ta da ya sauka kafadarta……..Rashida ta karaso gurin cike da nauyi da jin kunya take musu barka da zuwa! Ya dinga amsawa da sakakkiyar fuska kamar bashi ba sai wani dariya yake yana godewa Allah lallai Khalifa Waliyi ne ashe dai da gaske a maganarshi , ya tabbata tunda yaga ‘yar uwarta itama tana ciki……..Ya kalleta a nutse yace.”Ina fata mai allo na nan.” Tace.”Eh yana nan yau bai fita da wuri ba ya tsaya yiwa anti Wasila rubuta.” Da jin maganarta sai yaji tamkar an tsiyaya mishi ruwan sanyi mai madara a ranshi yaji duk wani kunci da tashin hankalinsa ya kau! sai ya dinga zumud’in shiga gidan, yana fad’in “To kije ki shaida mishi cewar mune muke tafe.” Da sauri Rashida ta nufi cikin gidan cikin murna da farin ciki sai kace wacce akace ga mahaifinta ya dawo duniya……… Lokacin da shiga gidan Wasila ta tashi hakanan Bitan ma tana kicin tana gyara tukunya, ta zube a gabanshi da walwala a fuskarta tace”Kawu ga Alhaji Ahamdu mijin anti Wasila nan shida mahaifiyarshi yace a sanar maka da zuwansu.” Mai allo ya jinge allon dake hannunshi yana kallonta Yace.”To Masha Allah sune suke tafe cikin wannan ranar? maza karkade tabarmar nan ki gyara musu guri bari na shigo dasu Allah yasa ma ban fita ba da munyi sa’bani.” Rashida ta shiga karkad”e tabarma tana sake share gurin da marmatsar da abubuwan dake kan hanya…..Mai allo ya sanya takalmansa a nutse ya fita daga gidan………Tana ‘kokarin fitowa daga band’akin ne hancinta ya sha’ko mata masifaffen ‘kamshin turaransa da ba zata ta’ba mancewa dashi ba……Gabanta ya yanke ya fad’i lokacin da ta tsinkayi muryarshi yana sallama a gidan ta kuma tsinkayi muryar mai allo yana fad’in “Sannunku da zuwa Alhaji sannu kun d’auko rana Hajiya sannu da hanya, ku shigo ciki……’Kyauran band’akin ta ri’ke gam! jikinta na kyarma! ta dinga fad’in innalilihi wa’ina ilaihi raji’un! me ya kawo shi? me yazo yayi mana? me yake nema kuma? babu wanda zai bata amsa, ta cigaba da rike kyaure tana rawar jiki tana kuma juyo muryoyinsu a lokacin da suke gaisawa da juna. Jikinta ta duba daga ita sai zanin atamfa dan da zafi ya isheta bayan fitar rashida ruwa ta cika a bokiti taje ta kwara a jikinta wai ko ta samu sassauci babu abinda ke jikinta sai zanin atamfar da dankwalinshi, kamar za tayi kuka yanzu ni ya zanyi na fito ga mutane gashi ba suttura a jikina? tunanin da take kenan ta juyo muryar Mai allo na fad’in ” Rashida shiga ki kira ‘yar uwarki mana ni kaina a ‘kasa ina rubutu ban san sanda ta tashi daga gurin nan da tana kwance a gurin nan da kake zaune.” Yafad’a yana nuna masa inda yake zaune, sai ya shiga bin gurin da kallo kamar zai ganta a gurin……Rashida ta duba dakin bata ciki, Bitan dake kokarin fitowa daga d’aki tace”Ai inajin tana band’aki wanka take kasan dama yini take watsa ruwa bata son zafi ai.” Mai allo yace.”To to koda naji.” Ahmadu kuwa jin abinda Bitan tace sai kawai ya shiga rarraba idanunsa a cikin gidan yana laluben ta ina zata fito……Aikuwa sai yaji motsin ‘kyaure a wani ‘bangare da sauri ya mai da idanunshi gurin……Ta fito a hankali kamar wacce ‘kwai ya fashewa a ciki take tafiya, zanin jikinta ya d’angale saboda daurin kirji da tayi sai tayi amfani da dankwalin gurin kare kirjinta da fuskarta…….Gogon ya wani susuce a gurin ya dinga kallonta tin daga kafafunta har zuwa kanta, jikinsa yay wani bala’in sanyi lokacin da ya hango tudun cikinsa dake jikinta, rintse idonsa yayi yana tasbihi ga Allah ya sauke wata gawurtacciyar ajiyar zuciya, Ya bud’e idanunsa da sauri a dai-dai lokacin da take ‘kokarin shiga d’akinsu santsin takalmin dake kafarta ya kusa kayar da ita, tayi axamar rike kyauran d’akin tana salati zubewa tayi bakin kofar lokaci guda zanin jikinta ya kusa sa’bulewa dankwalin da ta rufe kanta da kirjinta tuni yayi nashi guri, wani irin ‘kullewa marar tayi tana murd’a mata………kawai ganinsa tayi tsaye a kanta ya wani gigice yana sa’be babbar riga dama manyan kaya ya saka tunda duk sanda zaije gurin mai allo baya zuwa da tazarce na shadda ko yadi riga da wando da malin malin yake sanya……..Shine yay bake bake a gurin yana fad’in “Subahanallahi! Kafin ta juyo miryar Bitan na fad’in ” Haba Wasila sai da fa na hanaki saka takalmin nan saboda santsin sa sau nawa yana kokarin kayar dake dan dai kawai Allah na kiyayewa ne, kinga ni dai yau ga abinda ya ja miki.” Bitan ta ‘karashe maganar tana kokarin mikar da ita! Rintse idonta tayi tana fad’in “Wayyo cikina mara ta ciwo Bitan Ya Allah.”!!!! Da sauri yay nufi shiga dakin zufa na karyo mishi Hajjah ta dakatar dashi tana hararshi, ita ta shiga dakin suka kama Wasilan suka janye ta daga bakin kofa! Shi kuma ya cire hularshi yana fifita da ita! Wannan wane irin tsautsayi ne? daga zuwanshi yana murna Allah dai ka taimake ni.”! Abinda yake fad’a kenan ya koma ya zauna yana cigaba da fifita da hularshi fargaba duk ta cika masa zuciya……Mai allo ya kalleshi cikin naxari sai kawai ya girgiza kanshi yana murmushi a cikin zuciyarshi ya cigaba da d’auraye rubutun dake jikin allon hannunshi, Yace.” Tuntuni naji Bitan nayi mata magana kan ta daina saka takalmin nan saboda rashin ji ta’ki dainawa, gashi yana so ya cutar da ita, tunda abin ya kasance da haka da kaina zan dauke takalman na fita dashi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button