NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
63
Jin yanda yake sake rintse hannunta dake cikin nashi ne ya sanya tayi saurin kallonshi, suka had’a ido tayi saurin saukar da nata ‘kasa tana motsi da bakinta, so take tayi magana amma saboda tsabar kwarjinsa ya sanya takasa, sai kawai ta cigaba da kallon gefe guda tana jin yanda yake shafa tafin hannunta a hankali a hankali, lokaci ‘kankani taji duk jikinta yayi sanyi idanunta suka soma lumshewa da alamun bacci a tare da ita, kanta ta dora jikin murfin motar tana takure jikinta hade da runtse idonta gam! wannan abin da yake mata sam bata so wani ya gani a cikinsu khalifa dake gabansu, Allah ma yasa hirar da sukeyi ta dauke musu hankali da yake rashida akwai saurin sabo duk garin da suka wuce sai ta tambayi khalifa sunan garin shi kuma ya fada mata tare da cikakken bayani…….Yana kallonta ta takure jikinta a jikin murfin mota idanunta a rufe, sai ya sake matsawa jikinta sosai ta bude lumsassun idanunta da suka soma sauyawa bacci ne ko meye oho! a hankali ya kamo ha’barta ya d’ora kanta kan kafad’arshi kana ya zura hannunsa ‘kar’kashinta ya ri’ke ‘kugunta sosai ya matso da ita jikinsa ya ri’ke da kyau!! Rintse idonta ta sakeyi tana sauke ajiyar zuciya gabanta na d’an fad’uwa kad’an-kad’an! Kamshin turaran jikinsa ne yayi masifar tafiya da imaninta abinda ya sanya ma kenan ta sakeyin luf a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, jikinta ya soma shikawa bacci na fizgarta mai dad’i……Jin shirun tayi yawa ne ya sanya Khalifa d’an juyowa yanayi masa magana, sai kawai idanunsa ya gane masa abinda ke faruwa, Abokin nashi ya gani ya wani yi la’kas! dashi hankalinsa kacokan na kan Wasilan da bacci me nauyi ya dauketa a jikinsa, shi kuma ya kurawa fuskarta ido fuskarshi dauke da wani munafikin murmushi…..Khalifa ya danyi gyaran murya yana fad’in “Kaga yanzu mun wuce gaidan! garinsu Alhaji Yunusa mutumin nan dake kawo mana shanun sallah.” Ya dago kanshi yana kallon khalifan yana ya mutsa fuska yace.”Nagane shi koba wannan madamfarin mutumin ba? kasan akwai sallahr da ta gabata nasa shi ya kawo min shanu irin wanda nake sadaka dasu, ya kawo marasa lafiya cikin guda goma uku ne suka rayu naji ciwon abinda yayi min shiyasa na daina siyan shanu a gurinshi.” Khalifa yace.” Nima tuntuni munyi hannun riga dashi dama ai nine na had’aku dashi ko?” Gyad’a kanshi kawai yayi ya sake gyara zamanshi wanda hakan ya sanya kanta ya sauka a kirjinsa a maimakon kafadarshi, gyara ta yay sosai ya tallafeta da hannunshi guda…..Khalifa ya kalleshi shima ya kalleshi sai yayi mishi nuni da Rashida da bakinshi, basarwa yayi ya nunawa Khalifa shi ina ruwanshi da wata rashida! Abinda basu sani ba kuwa shine ba rashida ba har su Garba sun d’an hango abinda ke faruwa basarwa kawai sukayi……Murmushi kawai Khalifa yayi ya juya yana mamakin abokin nashi, idan ance masa yana son yarinyar sai yace ba hakaba gashi lokaci ‘kan’kani duk ya wani susuce a cikin mota.

Kuluwa ta fito daga cikin d’akinta hannunta rike da wani ‘kullin kaya, wanda zanin da aka d’aure kayan yayi da’kal-da’kal da daud’a, ta nufi inda Uwani ke sunkuye da wata ‘katon baho a gabanta, wacce ta cika ta da kayan wanki ta zuba klin da sabulu a hannunta tana cud’awa! Kuluwa ta dire ‘kullin kayan dake hannunta tace”Uwani idan kin gama wankin dan Allah ki d’an sa’be wa ‘kananan yaran nan kayansu tuntuni nake so nayi wanki bani da sabulu kina dai kallo kwana biyu gidan sai a hankali yanzu Kawunki baya fita komai ya rinca’be mana.” Uwani ta d’ago kanta cikin tsananin wahala da gajiya tace”Kuluwa kinga dai sabulun nan banawa bane na mutane ne dan Allah ki bari a wankewa mutane kayansu ya fita wai me yasa duk sanda zanyi wanki sai ki kwaso min kayan yara kice na wanke alhalin kin san sabulu da omo ba nawa bane nima aikatau nakeyi a biyani.”
Da jin abinda Uwani ke fada sai Kuluwa ta fusata ta soma sirfa mata masifa da fad’in wallahi duk sanda ta sake yi mata musu kan abinda ta umarce ta dashi to sai ta bar mata gidanta.” Uwani dai ta cigaba da gurxar wankinta bakin ciki duniya kamar ya kasheta, tun safe take wankin jama’a har yanzu bata karya kummalo ba, ko da yake sai ta g

ama wankin ta kai sannan zata samu kudin da zata siyi abin karin dashi dan tuntuni Kuluwa ta daina bata abin kari a gidan, da daddare kawai take bata abinci shima d’an mitsitsi idan towo ne kuwa sai ta lakata mata ‘karshen kwasa cikin kwano wanda yaro ‘karami ma yaci ba zai isheshi ba.
Tana gurxar wanki hawaye na ‘kokarin su’bce mata, wannan wace iriyar masifa ce take cikinta? tayi dana sani tayi nadama tayi da ace abinda ya wuce zai dawo baya data yi gaggawar gyara kuskuranta, wannan wuya da take sha tasan duk itace ta jawowa kanta, Allah ya kawo musu dauki ita da ‘yarta ya had’ata aure da mai kudi mai mu’kami amma sabida hange da mummunar kaddara ta dinga zugar ‘yar tata ta kashe auranta, yanzu wa gari ya waya? wahalar da take ciki a yanzu ta wuce wacce taci a baya, a gidan Kawunta ana bata abinci taci ta koshi anan kuwa sai dai ta nema ta ciyar da kanta, Kawu Madu sallamamman namiji ne mijin tace sai abinda kuluwa tace ayi a gidan yake yi shiyasa duk abinda yake faruwa da rayuwarta baya tofawa, tun bayan tafiyarsu Wasila da kwana uku Kuluwa ta soma gallaza mata kyara! da hantara! da masifa! da kuma horan yunwa! ganin hakane ya sanya Ta nemi Inna Tabawa tana kuka take shaida mata halin da take ciki, itama Tabawar ta tausaya mata sosai sai da bata da yanda za tayi tunda itama talakace, sai kawai ta bata shawarar kan cewar ta kama sana’a sai ta rike kanta, saboda ba komai ne yake sanya Kuluwa nayi mata rashin mutunci ba saboda tana bata abinci ne.” Uwani tace”Dama can baya nayi sana’ar wanki indai zan samu anan to wallahi zanyi na rufawa kaina asiri.” Tabawa tace”Kada ki damu idan Allah ya kaimu gobe kizo gidana mu tafi cikin gari Unguwar amare zamu mubi gidajen mutane idan suna da wankau su bamu.” Uwani tace”To shikkenan.”

Aikuwa gari na waye wa Ta shirya ta tafi gidan tabawa, suka dauki hanyar cikin gari…….gida biyar suka samu wanki aikuwa Uwani ta zage ta wanke musu kayansu ta shanya musu tsaf suka biyata kudinta, ranar sai yamma suka dawo gida, Uwani ta bawa Tabawa kudi cikin kudin da samo ta ‘boye sauran a jikinta……Tun daga sannan Uwani ke zuwa unguwar amare tana musu wanki watarana kuma ta d’oro kayan saman kanta ta tawo dashi gida sai ta wanke su bushe tsaf sai ta kai musu su bata kudinta.

Da ‘kyar Rashida ta iya gane hanyar gidan ta dinga nunawa Garba hanya yana bu ta cikin kunyar gonakin mutane gwajab gwajab din da motar take ya sanya ta bud’e idanunta tana d’an motsawa, sai kawai taga duk rabin jikinta a jikinshi, yayin da shi kuma yayi wani irin zama a cikin motar kamar wanda zai kwanta yayi hakan ne domun taji dadin yin baccin a jikinsa……..Da sauri ta mike zaune tana gyara xamanta had’e da gyara mayafinta ta d’ora saman kanta…….Ya mi’ke zaune sosai yana ya mutsa fuskarsa, hakuri kawai yake yi amma wannan kwanciyar da tayi a jikinsa ta ya mutsa shi, sosai ya d’an saci kallonta sai yaga tana hamma! da alamun baccin bai isheta ba, sai kuma ya mutsa fuska takeyi cikinta ne ya soma ‘kullewa yunwa na sasakarta dama ‘ka’ida ne idan tayi bacci ko yayane ta farka sai taci abinci…….Jikinta ne ya soma rawa, ta dinga zare ido tana mutsu mutsu ta rasa ya za tayi a yaron dake cikinta yana mata wani irin motsi da zillo tare danno mararta kamar me shirin fitowa waje, cikin rawar murya tace”Rashida ina kayanmu suke.”? Rashida tayi saurin juyawa tana kallonta ganin yanda idanunta suka kad’a ne ya sanya ta gane yunwa takeji da sauri tace” Suna bayan mota.” Still murya na rawa tace”To sai kizo ki dauko min kin san dai cewa nayi ki rike min a hannunki saboda zan iya bukatarshi cikin ko wane irin yanayi me zai sanya kisa a cikin akwati.” Rashida tace.”Yi hakuri anti Wasila ai mun kusa sauka.” Tsaki taja tana motsa bakinta…..Ya kalli Rashida cike da kulawa yace.”Menene.”? Tace.” ‘kwai dafaffe ne Bitan ta bata shine tace na ri’ke mata a hannu na ni kuma wallahi na manta nasa a cikin jakar kayanmu gatacan a bayan motar.” Shiru yayi kawai ya juya bayanshi da kanshi ya kinkimo jakar kayan nasu ya d’ora saman cinyarshi ya zuge zif din jakar ya soma dubawa…..Nan ya d’auko daurin leda yaluwa da dafa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button