NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

A babban soron gidan suka tsaya Kuluwa sai l’eken kofar gidan take dan Kawu cewa yayi su tsaya anan zai shigo dashi Kuluwa duk ta ‘kago sai d’aga kai takeyi tana lekawa…..Wasila taji tamkar ta gaura mata mari shin wai ita wannan matar wace irin mata ce mara kintsi da kamun kai.? ‘Kamshin turaranshi ne ya bakuncin hancinsu gabad’aya, Uwani ta gyarq lullubinta hade da sunkuyar da kanta ‘kasa kunyar hada ido take dashi sosai, Ita kam kuluwa fad’i take “Sannunku da zuwa Alhaji sannuku.” Ahmadu da Khalifa suka samu gefe suka tsuguna a nutse aka fara gaishe gaishe, Ahmadu ya kasa tantance mahaifiyar matar tashi duk da ya ta’ba ganinta sau d’aya amma dai baya tunanin Kuluwa itace saboda yanda ta za’ke da yawa sai banbad’anci takeyi tana musu hirarraki Mikewa sukayi a tare Khalifa ne ya fara yin gaba shi kuma ya tsaya yana gyara rigarshi, kuluwa ta tsura mishi ido Kudi ya fito dasu daure a kyaure ya mi’kawa Wasila dake gefanshi a hankali yace.”Ki bawa Momy ko.” ‘Kin ‘karba tayi Kuluwa tayi wuf ta kar’be kudin tana washe baki da fad’in “Ai kunya ba zata bari ta kar’ba Alhaji Mungode kwarai Allah ya tabbatar da alkairi ya baku xaman lafiya.” Uwani da Wasila ba suji dadin Abinda Kuluwa take ba, sai basu da yanda za suyi da ita……… Kuluwa da Kawu har bakin mota suka rakosu suna musu godiya da fatan alkairi, jama’ar garin sun taru suna mamakin irin bakin da Kawu Madu yayi, sai bayan motarsu ta ‘bace daga gurin ne Kawu ya shiga yi musu bayani cewar Ai sirikin sa ne mutumin dake auran ‘yar gidan Uwani ‘yar ‘kanwarshi…..
Uwani cikin gidan ta koma ta shiga daki ta had’a tagumi hawaye takeyi sosai takejin kewayar ‘yayan nata amma ko babu komai zamansu a gidan Ahmadun sai yafi mata kwanciyar hankali fiye da su zauna a wani guri itama ta yarda mutumin nason ‘yarta dan da baya sonta da bazai mayar da ita ba duk da tarin laifin da tayi masa.

Bayan azuhur suka sauka gajiya gami da jiri da zaman mota suka taru sukayi mata yawa, dan da kyar ma ta iya fitowa daga motar kafafunta duk sun sage sunyi tsami! Tana dan ya mutse fuska t

a rike hannun Rashida tana kokarin zama gefan shuke shuke! Ya fito daga cikin motar hannunshi rike da babbar rigarshi, Garba ya kar’bi rigar da wayoyinshi, hankalinshi na kansu yaga tana matse fuska cike da kulawa yace.”Lafiya menene.”? Shiru tayi mishi.” Ya kalli Rashida yace.”Ku shiga ciki mana karki bari ta zauna anan.” Rashida ta kama hannunta suka soma tafiya, ‘kafarta ta dama ce ta ri’ke ta kasa takuwa, ta rintse idanunta tana salati, dama tun a cikin mota takejin yanda cikin ke tattare mata yana dunkule mata guri guda, kwallah ta cika mata ido bakinta na rawa tace”Rashida ‘kafana d’aya ta ri’ke gefan marata ya daure.” Rashida tace”Ki daure anti wasila zaman mota ne yaja mu shiga ciki ka zauna sai in matsa miki kafafun naki.” Yana tsaye suna magana da Garba yaga sun tsaya sai ya sallami Garba ya nufi inda suke…….Rashida na ganinshi tace”Wai kafarta ciwo take.” Yace”Subahanallahi! to me ya jawo hakan.”? Rashida tace “Nima ban sani ba watakila kuma zaman mota ne.” Ya kalli Wasilan yaga tana kuka tana kokarin zama kasan gurin……Yace.”Kada ki zauna anan mana tashi mu shiga ciki ki samu kiyi wanka sai ki kwanta ki huta.”
Shiru tayi ta’ki tanka masa bala’in haushinsa takeji a ganinta ba kowa ne ya jawo mata wannan masifar ciwo ciwon ba sai shi…..Ganin tana had’a zufa a gurin rana na dukanta yasa ya sunkuya ba tare da yayi shawara da ita ba ya dauketa cak daukar jira jirai yayi mata ya nufi cikin gidan da ita……Duk da halin da take ciki sai da taji wani iri kunyar ma’aikatan gidan duk ta rufe ta tasan dai dole idan wasu ba sugani ba wasu zasu gani Uwa uba ga ‘Kanwarta Rashida, rufe idanunta kawai tayi ta ‘boye fuskarta cikin ‘kirjinshi…..Rashida tabi bayansu tana sinne kai fuskarta dauke da murmushi sosai mutumin yake burgeta saboda irin kulawar da yake bawa ‘yar uwarta.

Hajja tace”Subahanallahi! me ya faru haka.”? Yace”Zaman mota ya sanya kafafunta tsami ta kasa tafiya dasu.” Hajja tace”Aifa dama zaman mota ma ga mai lafiya babu dadi ballanta ga mai ciki sannu Wasila ka shiga da ita ciki tayi wanka sai suci abinci su huta.” Baice komai ba ya shige da ita bedroom dinshi, kai tsaye bad ya kwantar da ita ya nufi toliet.

Mikewa zaune tayi a hankali tana d’an mikar da kafafunta wacce tafi takura mata da ciwo ta dan tasa kad’an! ta rintse idonta tana kiran sunan Allah can taji zillo a cikinta ta bude idanunta da sauri tana sauke ajiyar zuciya, yanzu zai isheta da kusurkusur a ciki idan ba abinci taci ba babu zaman lafiya…..Fitowa yay daga toilet din yana tattare hannun rigar dake cikin shi tayi saurin dauke kanta ya ‘karaso inda take ba tayi aune ba taji ya dauketa, da sauri ta kalleshi ya d’aga mata girarshi guda, dauke kanta tayi tana zumbura baki kamar zatayi kuka itafa wannan za’kewar da yake a kanta sam baya burgeta taga sai wani rawar jiki yake mata tasan dai ba komai ya sanya shi yake mata hakan ba sai dan tana dauke da cikinshi…..A hankali ya dure ta tsakiyar bandakin yana mata wani munafikin kallo ya dora hannunshi a wuyanta, tureshi tayi ta jingina da bango (garu) gabanta ne ya soma faduwa, Ya sake matsowa kusa da ita, sai kawai ta saka kuka tana ture kirjinshi, cikin taushin murya yace”Wanka zanyi miki ba wani abu ba, ke kuka baya miki wuya ko.”? Cikin nauyin baki da yanayi na gajiya tace”To ka barni mana nayi da kaina da can kaine kake min?” Ya shiga kallonta yana girgiza kanshi, yace.” Daga yau nake so duk wata d’awainiya taki ta dawo hannuna ni mutum ne mai tausayin masu lalura irin taki, insha Allah mutukar ina gida zan dinga dauke miki dukanin laluranki har Allah ya saukeki lafiya.”
Shiru tayi tana kallonshi anya kuwa zata amince da wannan dad’in bakin nashi? itafa tafi tunanin saboda cikin sa da take dauke dashi ne yasa yake rawar jiki a kanta…….Saukar hannunsa taji a bayanta yana kokarin zuge zuf din rigarta, ta dinga tureshi tana hawaye hakan be dameshi ba sai da ya cire mata kayan jikinta tas, ya kurawa cikinta ido da yayi kurcici a mararta, wata kwallah ce ta ciko a idanunsa, ya tsuguna gwiwa bibbiyu ‘kasan toilet din ya dinga sumbatar cikin yana shafashi da hannunshi, Wann

an k’wallar dai da yake ta ‘boyewa sai da ta sauka, yay gaggawar gogewa, tana kallonshi taji ya dan bata tausayi, dan janye jikinta tayi ta matsa gefe tana zum’bura baki…..Ya sake binta yana rike hannunta duk jikinsa yayi sanyi wani irin masifaffan son yarinyar yaji yana bin dukanin ilahirin jikinsa……A hankali yaja hannunta suka isa inda kwamin wanka yake ya dauketa ya shiga da ita cikin ruwan da ya had’a, ido jawur yake kallonta yana jin wani masifaffan fleening na taso mishi, soso da sabulu ya dauka ya shiga cud’a mata jikinta yana sakin ajiyar zuciya, kamar kwai yake ta’bawa haka yake cud’ata sai da ya tabbatar ya wanke ta tas kana ya dauki towel mai kauri ya nad’eta a ciki……Daukar ta yayi ya fito da ita ya zaunar gefan gado…..Vasilin ya dauko ya nufi inda take zaune, warware towel din ya shiga yi ta rike towel din mirya na rawa tace”Ni ka bari shafa mai ai bai da wuya zan shafa da kaina.” Girgiza kansa yay saboda idan yace zaiyi magana cikin halin da yake ciki zai iya tona asirin kanshi, ya kar’be towel din daga hannunta ya aje gefe guda, a hankali ya haye bed din ya raba ‘kafafunshi ya sanyata a tsakiya ya shiga shafe mata jikinta da vasilin din, girman nonowanta da yanda suka sake kumburi da bun’kasa shine yake gigitashi yake d’imauta shi ya dinga kokarin daurewa duk dan kar ya nuna zulamarsa a fili al’amarin ya gagara bai san sanda ya jefar da vasilin din ba ya sanya hannuwanshi duka biyun kan nonowan ya shiga lailayasu yana jan nipples din tare da sauke masifaffiyar ajiyar zuciya…… Da sauri ta mi’ke zaune tana kuka tana kare jikinta da blanket ta dinga watsa masa harara tana share hawaye……Hannu ya d’aga mata yana so yayi magana sai kuma ya fasa, jiki a sanyaye ya sauka daga bed din ya bude wardorve ya dauko mata riga da zani na atamfa (vilsco) ya mika mata muryarshi a ‘kasa yace.”Kar’bi ki sanya.” Hannunta na rawa ta kar’ba saboda bata so tayi musu yace zai ‘kara kusantarta, yana mi’ka mata kayan ya kama hanya ya fice daga d’akin hankalinshi a masifar tashe.
Da ‘kyar tasa kayan tayi kwance a bed tana siyayyar da hawaye sam bata jin zata iya sakewa dashi kamar da a yanzu babban burinta bai wuce ta rabu da cikin dake jikinta lafiya ba…………Bacci ne ya fara fizgarta sam yanzu bacci bayayi mata wahala, mussaman yanzu da ta samu daki mai cike da ‘kamshi da sanyin na’urar sanyaya guri, bacci mai nauyi ya dauketa.
Jin shuru bata fito ba ya sanya Hajja tace Rashida ta shiga dakin ta gani ko lafiya? Rashida na shiga ta tadda ta kwance a bed tana bacci, murmushi kawai tayi ta fito tace “Hajja bacci takeyi.” Hajja tace tace”Koda naji ai shuru din tayi yawa, to ga abinci can ke sai ki zuba wanda zai miki kici idan ta tashi sai taci nata.” Rashida tace”Nagode hajja.” Daining din ta nufa domin cin abincin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button