NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Ahmadu kuwa kai tsaye ke’bantaccan gurin hutawarshi ya nufa dake bayan gidanshi, yayi kwance kan wani irin gado mai kamar lilo yana lilashi idanunshi a rufe abin duniya yayi mishi yawa, ada da bata kusa dashi yana daurewa amma kuma yau din nan da ya kusance ta yaji hankalinshi ya tashi sosai wanda har baya so ya sake shiga gidan ya ganta gudun aikata abinda baiyi niyya ba, ya kuma lura da yarinyar kamar tana tsoranshi yanda take zabura idan ya kusanci jikinta tilas dama hakan ta faru a tsakaninsu tunda rabuwa ce sukayi ita dashi mara dad’i! amma dai shi yanzu babu sauran wani ‘kulli a cikin ranshi ya amince da tubanta kuma yana so suyi zama na kwarai zaman da kowane ma’aurata keyi, ammafa ya zauna yayi tunani da nazari hakan ba zata kasance ba har sai yayi kokarin dauke idonshi daga kanta, ba zai yuwu ba ace daga dawowarta ya fito da zulamarshi a fili dole ya dinga dauke kansa yana kuma nuna mata ba wannan ne ma’kusudin abinda ya sanya ya dawo da ita gidanshi ba, da wannan shawarar ya mike ya nufi cikin gidan dai-dai lokacin da ake kiran sallah la’asar…..Hajja da Rashida ne zaune a palon suna kallo suna hira ya shigo sannu yay musu ya nufi bedroom dinshi hajja tace”Yana da kyau idan ka shiga ka tasheta tayi sallah barcin yamma bashi da dadi ko kad’an Mafi akasarin masu ciki kuma sunfi s

on irinshi.” Yace.”Kwarai kuwa Hajja annabi ma ya hanemu da yin bacci tsakanin azuhur da la’asar bari na tasheta yanzu.”
Yana shiga dakin ya tarar da ita ta tashi idanunta na kallon rufin dakin….Ya karaso kusa da ita cike da kulawa yace.”Ki tashi kiyi sallah ina fatan ‘kafar naki ya daina ciwo.”? Daga masa kanta tayi yace.”To alhmdullhi.” Toilet ya nufa ta bishi da kallo tana ayyana abubuwa da yawa a kanshi ya fito daure da alwala ya fice daga dakin, a hankali ta sauko daga bed din ta nufi toliet din bakinta ta wanke sannan ta d’aura alwala ta fito, sallahr ma da kyar tayi saboda yana take jin wata shegiyar yunwa idanunta har rufewa sukeyi saboda rawar jiki wuyanta da hijab din da tayi sallah ta fito tana rarraba ido a palon……Hajja da Rashida na daki suna sallah sai shi kad’ai ne kan kujerar daining yana had’a abinci ya hangi fitowarta, had’a ido sukayi ta dauke kanta jikinta babu kwari ta nemi kujera ta zauna, ya gama had’a abincin cikin plate ya dauko a nutse ya kawo mata inda take, ba tayi musu ba ta ‘karba ta dora saman cinyarta ta fara ci da bisimillah a bakinta ya kawo mata ruwa da lemo ya aje gabanta ya juya domin komawa daining din ta bishi da kallo tana mamakin yanda ya zama wani silent babban mutum mai kudi da shekaru gami da tarin ilimi na boka dana isilma shine ya mayar da kanshi bawa a gurinta, mamaki take sosai sai kuma wani sashen zuciyarta ke fad’a mata cewar “Duk wani abu da zai miki shi a yanzu yanayi miki shine saboda d’anshi ko ‘yarshi da kike dauke dashi amma da babu cikinsa a tare dake kallo baki isheshi ba sai dai idan jarabarshi ce ta kawo shi. Girgixa kanta tayi kawai tana adduar Allah yasa ta sauka lafiya tagani zai cigaba da hidima da ita ko kuwa.

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book na barki da Allah! Kema kika karanta baki biya ba na barki da Allah! Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
65
Koda ya kammala cin abincinshi sai ya mike a nutse ya nufi bedroom dinshi yana tafiya tamkar wanda ‘kwai ya fashewa a ciki, shi kad’ai yasan abinda ke damunshi, hakika dawowarta gidan nashi na barazana da lafiyarshi dan tun suna cikin mota yake ta fama da joystick dinshi yana hanata aikata abinda takeso dan duk abinda yake daurewa yake yi a yanzu dai idan ba samu yayi ya rage damuwa ba to tabbas dai ya san yau da ‘kyar idan zai iya rintsawa……..Wanka yayi ya shirya cikin yadin kashmir d’an gasken milk colour mafi akasari kayanshi farare ne bai fiye sanya abu mai duhu ba duk da ya kasance farin mutum, ya tsaya gaban mudubi yana gyara wuyan rigarshi kana kuma ya dan gyara saisayayyar sumarshi ya daura agogo a hannunshi, turaranshi mai dadin kamshi ya fesa ya fito palo hannunshi rike da hularshi yana gyarawa, Tunda ta daga kanta sau daya suka hada ido dashi ta mai da kanta ‘kasa gabanta na fad’uwa, ganinshi tayi tamkar sabuwar hallita kamar wanda aka ‘bareshi a akwali (sabo) yayi wani fresh dashi fatarshi tayi luwai luwai annuri sai sauka yake kan kyakykyawar fuskarshi…..Hajjah tace”Au na d’auka yau d’aya zaka zauna a gida tunda matar gidan ta dawo sai ku tattauna a tsakaninku amma naga ka shirya zaka fita.” Ya danyi gyaran murya yana d’ora hular a kanshi yace.”Ba zan jima ba zan dawo insha Allah akwai ba’kin da zanyi zamu had’u dasu can gest house d’ina dan already ma yanzu suna can suna zaman jirana.” Hajja tace”To Allah ya kiyaye a dawo lafiya.” Rashida tace”Yayana Allah ya tsare.” Ya amsa cike da kulawa. Ya d’an saci kallonta dai-dai lokacin data d’ago kanta suka had’a ido dashi, murmushin sa mai tsada ya sakar mata yana d’an d’aga mata girarashi guda kamar dai yanda ya saba, tayi gaggawar mayar da kanta ‘kasa kamar bata so tace”Adawo lafiya.” Bai tsammanin hakan ba sai yaji dad’i sosai yace.”Amin amin.” Ya nufi kofar fita, tsintar kanta tayi da binshi da kallo har sai da ya fita sannan ta mai dauke kanta tafiyarshi ma abar kallo ce komai nashi a nutse yake ya cika namijin da ko wace mace zatayi sha’awar aure amma ita har yanzu tana shakku a kansa dan tana jin tsoron ta sake sakin jikinta dashi wani abun ya had’asu na kuskure yazo ya saketa ko yaci mata mutunci amma itama tana hango tsantsar son da yake mata a ‘kwayar idonsa.

A can gest house din nashi Khalifa ne tare da Alhaji Muktari daura dan takarar governor jahar katsina ya kawo masa ziyara tare da dashi da mu’karrabansa, dake jam’iyarsu daya shiyasa suke zumunci kuma kusan halinsu yazo d’aya da juna, Alhaji Muktari ya ta’ba zama governor a jahar katsina yanzu yana so ya maimaitane yana kuma so ya karya al’kadarin governor dake ci a jahar tasu mai suna Engineer Haruna Haruni mutum ne mugu wanda yake mulki bisa zalinci halinsu d’aya da mai girma governor Lawan Rabo governor dake ci a jahar kano, duk wani ‘kulla ‘kulla gami da cuta da zalinci tare sukeyi dan duk abinda Lawan Rabo yayi a jahar sa to lashakka Haruna haruni shima sai yayi a tashi jahar, Wannan dalilin ne ya sanya Alhaji Muktari zuwa gurin abokin nashi domin su shawarta abubuwan da zai amfane su ya kuma amfanin al’ummar jahohinsu……………Tunda Governor Lawan Rabo ya samu labarin zuwan Alhaji Muktari garin sai ya dami kanshi, sosai ya kira Abokin nashi ya shaida mishi abinda ke faruwa, Haruna Haruni yace.” Nasan ba zai bar garin ba tilas sai shigo ku gaisa kada ka nuna masa komai kamar yanda suke abunsu a lullube muma zamu bisu a haka, ai yanzu ya’ki d’an zamba ne muke kan kujearar mulki sai munso wani zai hau ka daina tayar da hankalinka kan komai kuma Amadu ya daina firgitaka, komai fa na hannuka a yanzu koda Amadu ne ya cika za’be sai munyi juyin mulki ballantana kuma muna da mai matacciya wannan maimai d’in ko sun so ko sun’ki sai munyi idan zaka shigo katsina ka shigo a shirye domin tilas ma a wannan karon mu kauce hanya mubi matasan yaran nan a sannu su samo mana ‘kananun yaran da zamu bawa mai matacciya yayi mana aiki a kansu, tabbas dai nasan baka mance abinda ya faru ba a shekaru uku da suka gabata.” Lawan Rabo ya sauke ajiyar zuciya yace.”Tilas shawararka ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button