YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Malam mai allo yayi shiru yana jimanta al’amarin, to har yausha hakan ta faru basu sani basu sani ba ko da yake hakan zata iya kasancewa tunda bayan rasuwar Yahuza rigima suka dinga tafkawa da Uwani mahaifiyar yaran kan dole sai an raba gado an bata na yaranta shi kuma yace ko za’a raba gado to ba za’a bata na yara saboda ita mace ce su kuma yaran lokacin suna yara kananu za dai a siyar da gona a raba kudi kaso biyu shi ya dauki kashi daya sauran kuma ya zama magada wato Wasila da Rashida kenan in yaso ita sai a fitar da ita na tuminin takaba kamar yanda addini ya shara’anta…..Nan ma sai ta tada ballin masifa taje ‘yan uwanta suka zugota tazo tana yiwa su malam rashin kunya wanda hakan ya janyo sukayi mata fatata fatata! sannan suka kwace su Wasila daga hannunta, kwana biyu da faruwan lamarin Wasila dake tana da wayo a lokacin ta kai kimanin shekaru goma sha biyu sai ta fakaici malam din ya tafi tsangaya ra rike hannun kanwarta suka gudu da malam ya dawo ya samu labari yace.”Suje idan shine sai sun tako da kafafunsa sun neme shi, to hakance ta kasance koda su Wasila suka koma gaban mahaifiyarsu sai wahala tayi tsanani a garesu da kyar suke ci daya a rana Wasila itace yawon bin gidajen amare tana musu wanke wanke da raino da share share su bata kudi da abinci ita kuma Uwani itace aikin wankau da dakau da sauransu…..Wasila ta yanke shawarar tun karar wan mahaifin nasu domin su bashi hakuri suka shirya tsaf suka nufi Garin nasu Garko!! Malam ya dinga musu fad’a sosai yace.”Duk tsiya dai nine mahaifinku tunda babu ubanku kuna bin shawarar mahaifiyarku kuna bijere ma dangin ubanku to ko auranku ake nema gurinmu zaku zo gwara ku nutsu kuyi hankali ku zauna tare damu zaman ku cikin wannan gida ku kadai bai dace ba saboda haka na yanke shawarar zan baku daki daga ku zauna har Allah yasa ku samu mijin aure ita kuma Uwani ta tafi gidansu itama bata wuce aure ba idan ta samu miji tayi aure….Da jin wannan magana ta malam mai allo sai su Wasila suka yanke sgawarar guduwa domin a ganinsu yanda suka saba da zaman birni zasu cutu a kauye….Washe gari Uwani ta tasa kan ‘Yayanta da asuba suka gudu….Wannan abu da sukayi ya batawa malam mai allo rai tun daga lokacin ya dauke hannunsa daga kansu idan ma sauran ‘yan uwa suka kawo masa maganarsu sai ya koresu yace kar wanda ya sake kawo masa maganar wadannan yaran marasa kunya suje duniya ce zata koya musu hankali.
Wannan kenan
Malam mai allo ya kalli Hajara yana girgiza kansa yace.”Hakika naji dadi da kukayi gaggawa zuwa ku sanar dani wannan al’amari dake faruwa, wannan rashin tarbiyar ne yasa tuntuni na hana Yahuza tafiya maraya da zama saboda nasan tilas a haifi da mara ido a lokacin ya rufe ido yaki sauraran kowa shi dai kawai ya tafi burni ya nemi kudi karin abun kuma ya hadu da mata mara kamun kai ya aure ai asalin lalacewar yaran daga mahaifiyarsu ne da ta basu tarbiya da duk haka bata faruwa ba mu kanmu Uwani bata ganin girmanmu ballanta tana nuna musu muhimancimu a gurinmu, amma babu komai insha Allahu gobe tare zamu tafi kome za’ayi kafata kafar yaran nan dan bazan bari su lalace ba ace muna kallo nan zan kawo su duk in aurar dasu kowa ya huta.”
Hajara tace”Wannan shawara taka itace abun dubawa Allah ya tabbatar mana da alkairi.” suka amsa da “ameen” gaba d’ayansu.
To kamar dai yanda malam mai allo ya fad’a hakane ya kasance da wurwuri yayi sallama da ‘yan uwa ya fad’a musu abunda ke faruwa suma suka bada goyon bayan kan hukumcin da ya yanke, kana suka hadawa Haraja sha tara ta arziki suka bita da godiya da fatan sauka gida lafiya.
Uwani da Rashida kadai ne a gidan sunci kwalliya har sun gaji kamar wanda zasuje gidan buki ga cefane nan kayan miya da nama cikin takarda za’ayi miya gida sai kamshi yake yi….Amina na kwance a tabarma tana danna katuwar waya Uwani na kicin tana aiki Malam mai allo yayi sallama a kofar gidan…..Gaba d’ayansu sai da gabansu ya fadi! Uwani ta fito daga kicin da ludayi a hannunta tana fad’in”Ke Rashida muryar wa nakeji kamar ta wannan masifaffan tsohon.”! Rashida tace”Wallahi nima irib muryarshi naj……Kafin ta karasa muryarsa ta sake karad’e gidan “Salamu alaikum.”!! Uwani ta amsa da karfi tana fad’in” Waye wai yake rangwada mana sallama kamar munci bashi.”
Malam mai allo ya girgiza kansa jin muryar Uwani radau! yasan zata aika tunda dama ba kunya gareta ba……”Nine malam mai allo na Garko.”!
Yafada yana dafe kyauran kofar gidan.
“Ayyo koda naji wannan sallama haka to ana zuwa.” Uwani tafada tana jan karamin tsaki.” Ta kalli Hajara “Ai sai ki tashi kije kece tilas dinsa ni kuwa yace zai min wannan wa’azin sai dai mu kwashi ‘yan kallo ni dashi a unguwar nan.”
Jiki a sanyaye Rashida ta mike ta dauki yalolon mayafinta dake kan igiya ta yafa, duk rashin kunyarsu suna shakkar malam mai allo dan baya musu da sauki………Tana fitowa ta durkusa tana gaisheshi bai amsa ba sai kare mata kallo yake ganin irin dinki dake jikinta atamfa ce duk an kacalcalata saman nonowanta duk a waje……Girgiza kansa yayi yace”Rashida kece kika dawo kamar ba d’iyan musulmai ba wannan shigar ta jikinki ta sabawa sharia meye abun burgewa anan.? to babu komai duk magana ta kare kiyi maza ki kirawo min daya marakunyar yanzu yanzu zan tasa ku a gaba mu wuce garko saboda na samu labarin ashararanci da kukeyi a gari mahaifiyarku na daure muku gindi kuna yiwa manya mutane rashin kunya wai Wasila ce take siyasa tana gogayya da maza saboda kasa ta rufe idon ubanku shiyasa annabi yace ka zabawa ‘yayanka mace tagari duk dan gudun faruwar irin wannan, mu ba’a son ranmu dan uwanmu ya auri mahaifiyarku ba saboda sam bata da tarbiya gashi kuma kun dauko irin nata halin to kome zakuyi sai da kuyi amma tilas ku koma can Garko da zama idan Allah ya kawo muku miji kuyi aur……”Babu wanda ya isa ya rabani da ‘yayana wallahi akan wannan sai in maka mutum a kotu.”!!!!Uwani ce ke fadar wannan maganar ashe tana la’be tana jinsu……”Haka kawai zaka zo har gida kana zagina malam ka rike mutuncinka da girman ka ada can ma ban yarda ba ballanta yanzu da nasan ina da ‘kumbar susa a hannuna dan haka ni banga wanda ya isa ya rabani da ‘yayana ba.”
Malam mai allo yace.”Uwani rashin kunya za kiyi min.”? Wannan ba rashin kunya bace gaskiya ce, sai da yarana suka girma suka zama mutane inacin ganiyarsu sannan za’a lalla’bo kawai saboda an samu labarin mun faso gari ace ga zance ga magana kafad’i idan kana bukatae wani abu yanzu yanzu sai na kira Wasila tayi maka hasafi ba wai kace zaka tafar min da ‘yaya kauye ba.”
Malam mai allo ‘kwalla ta taru a kwarmin idonsa yace.”Baku da kudin da zaku bani Uwani kuma kinyi min abunda yafi haka dan kin zageni a yanzu ba wani abun bane ni dai na gama yanke hukunci ke Rashida idan na isa daku maza jeki had’o kayanku muka kama hanya mu tafi.”.
Rashida ta mike ta shiga cikin gidan tana kuka wayarta ta dauka ta kira Wasila ta fada mata abunda ke faruwa…..Wasila tace”Kome zaiyi kar ku sake ku bishi ku kyaleshi a soro idan ya gaji da tsayuwa ya gaji ya tafi masifaffan tsoho kawai.” Uwani kuwa taja tunga ta tare bakin kofa ta rantse babu inda zai tafar mata da ‘yaya……Suka dinga tafka rigima da Malam mai allo Uwani ta dinga yi masa rashin kunya kamar ba wan mijinta ba har hankulan mutane ya fara dawowa kansu mutane suka fara taruwa a’lamarin yayi wa malam ciwo a ranshi sai ya fito waje ya tsaya yana tsumayin fitowar Rashida ganin ya fita daga gidan sau kawai Uwani ta rufe kofar gidan ta zura sakata ta koma ciki tana surutai “Idan ka kaji da tsayuwa ka tafi tsoho mai nacin tsiya kawai……….Garba dake can gefe suna magana da wani mutumi ya nuna masa malam mai allo dake bin kofar gidan da kallo yana mamakin rashin kirkin Uwani wato shi suka rufewa kofa, sai ya sanya gefan babbar rigarsa yana goge gumin saman goshinsa…..Garba ya karaso inda yake hannu ya mika masa suka gaisa yace.” Aramma idan ba zaka damu ba ina so mu tattauna wata magana da kai.” Malam mai allo dake neman wanda zai rarrashe shi kan abunda su Uwani sukayi masa yace.”Babu komai yaro ina sauraranka.” Garba yace.”Muje mota arrama.” Malam mai allo baiyi shakkun bin Garba ba saboda lokaci guda yaji ya aminta dashi suka nufi inda yayi parking din motar a tare.