NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE


Camas! tare da Usaini dillali

Malam Usaini dillali yayi nasarar damfarar Camas kudin manya manyan filaye guda uku kud’in sun kai kimanin miliyan shida da rabi dan bayan kudin Wasila har da nata tasa a ciki kusam miliyan biyu usaini yayi mata roman baka inda yake cewa kafin shekara kudin filayen zasu kai miliyan goma ko fiye da haka, duk ya bata dakardun gaibu ya gudu ya bar gari dama ba’asan daga inda yazo ba……….Camas ta zama tamkar mahaukaciya lokacin da taje taga filayenta wani attajiri yana aikin gina gidan gona dashi, ihu! ta dinga kurmawa tana zagin masu aikin gurun wai filayenta ne waye ya basu damar ta’ba mata…..Tana wani irin huci! ta d’auko musu takardun filayen tana nuna musu, duk suka kar’ba suna dubawa, sai suka kwashe da dariya sunayi mata kallon mahaukaciya, babban cikinsu yace.”Amma ke jahila ce wallahi wane shegen ne ya fada miki wannan takardar fili ce? hahaha! takardun wuta da ruwa ne saboda dakikiya ce ke baki fahimci abinda aka rubuta a jiki ba.” suka dinga dariya suna kallonta……..Wayarta ta dauko a fusace! take neman numbar husaini sai dai kiran duniya sai ace mata layin ma baya aiki kwata kwata, ta sharce gumin dake goshinta ta kallesu daya bayan daya tace”Idan kun san wata baku san wata ba, ‘yan sanda zan kira muku sune zasu rabani daku shegu tsinannu barayi.” Daya daga cikinsu yace.”Zaki ci ubanki yanzu.” Waya ya ciro ya kira mutumin da ya sanyasu aikin……Minti goma sai gashi cikin wata arniyar mota, ya karaso gurin yana me neman karin bayani, kawai tsaurin ido na Camas! sai ta hau kund’uma masa ashar har tana ‘kiransa ‘barawo mutumin ranshi ya baci da sauri ya kira Anti daba yace suje da ita su tuhumeta a inda yay sata idan ta’ki fada musu su ragargajeta! Tun a gurin suka dinga kwada mata mari suna haurinta da kafafunsu, sosai ta tsorata ta dinga kuka tana bawa mutumin hakuri yace.”Ai sai kin fada musu inda naje nayi sata.” Camas hankalinta yay masifar tashi ta dinga kuka tana data sani, haka dai Anti Daba suka tasa kyeyarta har ofis dinsu.


Cikin kaya marasa nauyi ya fito palo yay bacci har ya gaji, baccin da ya jima bai yi irinshi ba…….Kai tsaye daining ya nufa dan da wata irin yunwa ya tashi daurewa yayi yayi wanka gami da sallah sannan ya fito palon , hankalinta a kanshi lokacin da ya fito palon sai ta fara yunkurin mikewa Rashida tace”Anti Wasila ki koma ki zauna ki fada min abinda kike so sai nayi miki.” Girgiza kanta tayi tace”Aikin lada zanyi Rashida.” Hajja da rashidan suka bita da kallo lokacin da ta nufi inda yake wanda su sai lokacin ma suka san ya fito palon
Har ta’karaso inda yake idanunsa na ka

nta, ya dan sassauta fuskarsa yana yi mata wani irin kallo wanda kana ganinsa kasan na tausayi ne.
A hankali tace”Ya jikin.”? Sai ya tafi tunani shaf ya manta plan dinshi, da sauri ya dan ya mutsa fuska yace.”Yanzu kam alhmadullhi.” tace”Ka jima kana bacci dan har nayi tunanin tashinka kaci abinci kasha magani gashi lokacin shan maganin ya ‘kure biyar ta kusa.”

Ya aje cokalin hannunshi yana kallonta a nutse yace.”Gwara ma da baki tasheni ba dan da kin tasheni mybe ki ‘kara min wani ciwon ne tunda kin san bana so a tasheni ina bacci.’
Tace.”Eh nima tunanin da nayi kenan.”
Ya cigaba da kokarin zuba abincin, cikin nutsuwa ta kar’bi plate din tana kokarin zuba mishi ta hada masa komai ta tura gabanshi.

Yace.”Allah yay miki albarka.” Cikin zucci ta amsa, tana goge hannunta da tissue yace.”Sai ki ‘karasa ladanki ko.” Ta kalleshi tana son karin bayani.

Girarsa ya daga mata fuskarsa da murmushi me kayatarwa, tayi kasa da kanta tana dan murmushi ta gane abinda yake nufi sai kawai tayi niyyar barin gurin, yace.”Idan baki bani da hannuki ba to ba zanci ba.”

Ta juyo tana kallonshi cikin shagwaba tace”Bafa mu kadai bane a palon.” Yace.”Eh nasani tunda kina jin kunya dauko abincin muje daki.'” Makale kafada tayi tace”ka bari idan anjima sai na baka yanzu dai kaci wannnan da kanka.”

Ya wani lumshe idonsa yana mata shu’umin kallo yace.”Idan anjima ba abinci nake so ki bani a baki ba, wani abu nakeso ki bani.” Tace”Koma meye nayi alkawari kai dai kaci kasa magani.” Yace.”Kince Kinyi alkawari ko.”? Daga kanta tayi alamun E yace.”To zo ki zauna gabana naci abincin ina kallon fuskarki.” Dariya tasa tana kallonshi, tace”Idan na zauna kusa da kai ba zakaci abinci sosai ba idan ka gama ci na dawo.” Da murmushi a fuskarsa yace.”A ganinki idan kina kusa dani zan kasa cin abinci ko? baki sani ba xaman ki a kusa dani shine zai sanya na cinye abincin ba tare da nasani ba.” Kujerar daning din ta gyara ta zauna tayi tagumi tare da tsira masa ido tace”Shikkenan gani na zauna amma minti biyar na baka ka cinye abincin gabanka.” Yanda ta fad’i maganar ya bashi dariya yace.”ki dai ‘kara minti biyar su zama goma abincin fa nada yawa.” Murmushi tayi tace”Tom na kara minti uku.” Yace.” Okey.” Agogon hannunshi ya d’an duba biyar da minti da minti biyu……Sai yay bisimillah ya fara cin abincin da sauri da sauri yana had’awa da lemo Dariya take kunshewa ganin yanda yake cin abincin hannu baka hannu kwarya wai baya so lokacin ya cika bai cinye abincin ba………..Ya d’ago kanshi suka had’a ido lokacin ya cika bakinshi da abinci me cike da ganyayyaki ga nama dariya take tana nuna bakinsa da hannunta ‘kasan ha’barshi kan gemunsa duk miya! ta dinga kyalkyala dariya tana kallonshi……’Bata fuska yay da sauri ya kalli agogon hannunsa yaga biyar da kwata….Kallonta yay da sauri! itama tayi saurin kallon agogon hannunta, biyar da minti goma sha shida, Still dai da mirmushi a fuskarta ta d’aga masa hannunta mai daure da agogo tana nuna masa lokaci,
‘Bata rai yay yace.”Agogonki na latti.” tace.”Agogona dai-dai yake tafiya kai ka ‘kara minti hud’u kan mintinan dana baka dan haka al’kawarinmu ya rushe. Murmushi yay wanda ya tsaya iya la’bbanshi ya mika hannunsa yana kokarin daukar tissue tayi saurin cirowa tana goge mishi bakinshi dai-dai inda ya ‘bata a gurin cin abincin…..Kunyace ta rufe ta ganin yana mata wani irin kallo ta juya zata bar gurin……Hannunta ya rike yana me narkar da kwayoyin idanunsa cikin nata.

Taji wani irin yanayi a jikinta, a duk sanda zai mata irin wannan kallon nashi takan ji tamkar wani mayen son shi a cikin zuciyarta.

Mairairaice fuska yay ya mai da kanshi karamin yaro ya wani kankance murya yace.” Ina so ki zama mutum mai cika alkawari kan abinda kika al’kawaranta, kada kice min komai kece kikayi min al’kawarin zaki bani du abinda na nema idan naci abinci yanzu kuma kice min alkawari ya rushe.”
Yanayin yanda yake kallonta da kuma yanda yake magana kasa-kasa yasa ta fahimci inda ya dosa, sam dazu bata gane abinda yake nufi ba sai yanzu da ya nuna mata zahiri……Jikinta a sanyaye tace”To ai baka da lafiya.

” Ya dan kalleta cike da bege gami da tsantsar sha’awa yace.”Duk cutar dake damuna dana kusance ki za tayi nata guri ke dai kawai ki bada kai bori ya hau.”

Gabanta na fad’uwa tana d’an kallon gefansu Hajja tace”Tom na amince amma dan Allah kada kayi min da karfi kuma sau daya za kayi.” Da sauri yace.”Haba!! ai nasan duk abinda ke faruwa ba zan mayi da kaina ba kece zakiyi abinki yanda kike so.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button