NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Rau-rau tayi kamar zatayi kuka tace”Kawu Habibu haka halinshi yake kayi hakuri.” Yace.”Nine zan bashi hakuri ai kada ki damu duk sanda Allah ya saukeki lafiya zan daukeki muje har gidanshi na bashi hakuri ai tunda ina sonki babu abinda ba zanyi ba.” Hawaye suka zubo mata ta tsira masa ido tana kallonshi ta rasa wane irin so yake mata! Yace”Ke kam bakya gajiya da koke koke goge hawayenki.” Ya mika mata tissue kin kar’ba tayi tana shashsheka, hannunta ya rike ya mikar da ita suka nufi dakinshi.
Rungumeta yay ya rarrasheta tayi shuru kana ya bud’e wata drowar dake gefan gadonshi ya dauko mata wayoyinta da

jakarta, cinyarta ya aje mata yace.”Ki duba kiga abinda baki gani ba sai ki fada min.”

A hankali ta bude jakar tana dubawa komai nata data sani na ciki ga sabbin kudinta nan na sadakin auranta da sauran tarkacenta a ciki ta aje jakar tana kokarin kunna wayar, ya kar’ba ya kunna mata.
Numbar Kawu Habibu ta dauka a wayar tata ta soma kiranshi, aikuwa ya dauka duk suka cika da mamaki.

Muryarta na rawa tace”Kawu Ina kwana” Ya amsa yana tambayar wacece.”?

Tace.”Kawu nice Wasila.” Tana ji ya sauke ajiyar zuciya yace.”Wasila ya kuke ina fatan kunanan lafiya ko? ina mijin naki.”?

Ta dan kalleshi yana zaune yana jinsu, tace”Kawu gashinan kusa dani yana jinka.” yace.”Masha Allah.” Tace”Kawu dan Allah kayi hakuri ka daina fushi nice fa mai laifi dan Allah ka yafe masa kamar yanda mai allo ya yafe masa.”
Kawu Habibu yace.”Wasila ni tuntuni na yafe masa abinda ya faru kawai duk sanda na tuna sanda yazo gabanmu yace ya sakeki raina yake ‘baci sosai, amma ni bana rikon mijinki.” Tace”To Kawu me yasa idan ya kira wayarka baka dauka.”
Shuru yayi tace”Kawu kayi hakuri magana ta wuce nima nayi alkawari insha Allahu bazan sake baku kunya ba.” Yace.”Masha Allahu dama haka nake so naji.”

Amadu ya kar’bi wayar daga hannunta, a nutse yay sallama Kawu Habibu ya amsa cikin mutumci suka gaisa da juna, Kawu Habibu kunyar abinda yayi masa taso ta hanashi magana, inda shi kuma Amadu ya nuna masa komai ba komai bane ya kuma tabbatar masa da cewar abinda ya faru a baya insha Allahu ba zai sake faruwa ba a gaba……….Kawu Habibu yaji dadin maganarshi sosai da sosai dan yanzu babban burunsu shi da dan uwansa shine yarinyar ta zauna a dakin mijinta.

Mika mata wayar yay bayan sun gama ta karba tana fad’in “Kawu dan Allah idan ka koma gida ka bawa mai allo wayar ina so mu gaisa dashi.” Kawu Habibu yace.”Insha Allahu idan na koma gida zan bashi yanzu haka nayi tafiya wani gari zan kuma kwana biyu acan sai dai na koma din.” Tace.”To Kawu Allah ya dawo da kai lafiya.” Ya amsa da “ameeen.” Sukayi sallama cike da kaunar junansu……….Ajiyar zuciya ta dan sauke kanta a kasa, yanzu tana masifar kaunar kawunanta saboda ta gane yanxu sune gatanka……..Hannunsa taji cikin nata yana saka mata wani abu, ta dago kanta tana kallonshi, tana kuma kallon hannunta, wasu takardune guda biyu ya saka mata cikin hannunta……..Kallonshi tayi tana neman karin bayani.

Yace.” Kada kice komai ni nayi niyya kuma idan nayi kyauta ba’a cewa dani dan me? na jima da mallaka miki wasu kadarori nawa tun ranar da na amshi budurcinki na mallaka miki rumfunana biyu dake cikin kasuwar sabon gari, naki ne a halin yanzu halak malak, tun daga ranar dana mallaka miki kawowa yau din nan duk wani abun da aka samu na cinikayya suna cikin asusuna, insha Allah zamuje a bude miki account zan sa miki kudinki a ciki, bayan wannan kuma akwai sabuwar motar dana siya miki tana can gareji a ajiye, yanzu ki rike key d’in a hannuki.” Ya mi’ka mata key din motar yana murmushi.
Hannunta ne ya shiga rawa, ta rasa ma abinda zatace masa sai kawai hawaye ya ‘balle mata, rungumeta yay tsam a jikinsa yana shafa bayanta, cikin shashshekar kuka tace”Nagode mijina Ubangiji Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana Allah ya rabaka da sharrin masu sharri Allah ya bamu zaman lafiya da zuria masu albarka.” Ya dinga amsawa yana dan bubbuga bayanta a hankali.


Cikin ikon Allah da hukuncinsa komai na tafiya dai-dai a zamantakewar auransu, ta samu nutsuwa dashi ya samu nutsuwa da ita, yayin da karatunsu na al’kur’ani yayi nisa sosai yanzu sun wuce izifi ashirin tunda kullum sau biyu yake musu kari, bangaran littafan addini kuwa sun wuce matakin su ahlari da fikhu yanzu manyan littafai yake musu irin su Minhajil musulum zaduzjaujen Ismawi balaga……bangaran ilimin addini Wasila da Rashida ba’a cewa komai sai godiyar Allah.

Cikinta ya shiga wata na tara, lokacin kuma ciwuka suka tsananta yau ciwo gobe ciwo haka dai take daurewa duk sanda bala’in ya isheta sai ta shiga daki taci kukana ta koshi………….Gashi baya xama a gida sosai kusan kullum sai sun fita da jama’arshi yawon campain, wani sa’in ma

kwana sukeyi ko kuma su dawo cikin dare lokacin ta dade da yin bacci, ga Rashida ta soma zuwa makaranta abun dai duk babu sauki ta kowanne bangare wani lokacin hajja itake zama tana debe mata kewa idan kafafunta sunyi tsami ta matsa mata a gaskiya babu abinda zata ce da matar sai dai addua.
Akwai ranar da Anti Kubura ita da yaranta suka zo gidan suka tarar da Hajja na matsawa Wasila kafafunta duk sai suka shiga mamaki mai tsanani yanzu kamar hajja ke aikin matsar kafa…..Anti Kubura ta kufula ranta yayi masifar ‘baci ta kalli Wasilan shekeke tace”Wato asiri da surkullen naku na fulani ya dawo kan baiwar Allah wacce bataji ba bata gani ba, kawai saboda tsabar rashin arziki ki mike kafafu ki sanyata matsar kafafu shin itace tayi miki cikin da zaki dinga sata aikin wahala? ke ko kunya bakiji ba.” ! Hajja tace”A’a kubura nice nasa kaina ba itace ta sani ba, to idan ma itace ta sani laifine dan na matsa mata kafafunta ai lalura ce! bana son irin abinda kikeyi kubura.” Hajja ta karashe maganarta cikin jin rashin dadin abinda tayi…..Suhairat da takeji kamar taje ta turmushe Wasilan ita da cikin jikinta tace”A’a Hajja wallahi da sake! baxai yiwu ba idan suna cin ‘kasa to su kiyayi ta shuri! asirinsu da surkullansu ba zaiyi tasiri a kanki ba, shi da Yaya Amadu da yaga zai iya sai yaje yayi, amma kamar wannan mara gata da galihu ta saki a gaba kina mata matsar kafa! ai bata isa ba idan ita bata san darajarki ba to mu mun sani.”
Wasila ta soma kokarin mi’kewa ta bar musu gurin……Hajja ta dan rike hannunta tana mata sannu, hawayen dake kokarin zubo mata ta mayar ba tace komai ba tabar gurin, tana jin Suhairat na zaginta da kiranta ‘Yar iska jahila mai bin maza.” Wannan kalmomi sunyi mata ciwo sosai, kawai ta kwanta kan gado ta shiga kukan bakin ciki da takaici! Illar ka aikata mummunan abu kenan bata ta’ba zina ba amma gashi anzo har cikin gidanta ana kiranta da karuwa me bin maza…

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262alliya:
‘Yr Bngr Sys
72
Bayan shigar Wasila d’aki Hajja ta shiga yiwa anti kubura da Suhairat fad’a kan abinda sukayi bai dace ba suzo har gida s suna zagin matar gida……… aikin matsar kafafu itace tasa kanta ba wai Wasilan ce ta sanyata ba, tace mutukar idan kun san tashin hankaline zai kawo ku to ku daina zuwa dan kun san idan Amadu yaji ba zaiji dadi ba bana kaunar abinda zai ‘bata masa rai kamar yanda baya kaunar abinda zai ‘bata min rai! Ke suhairat ki iya bakinki wallahi naji kina kiranta karuwa a gidan ubanki tayi karuwancin? to wallahi kika sake Amadu yaji wannan maganar zai iya daureki kuma wallahi ba zance masa dan me ba tunda bakinki ne ya jawo miki.” Da jin abinda Hajja take fada sai kawai anti kubura ta fashe da kuka tana fyace majina tace”Haba Hajja ashe kudi yafi zumunci kada fa ki manta ni dake uwarmu daya ubanmu daya, Amadu kuwa bake ce kika haifeshi ba dan mijinki ne amma kike kokarin za’barsa akaina shikkenan nagode.”Anti kubura ta karasa maganar tana mikewa, tsaye suma Suka mike ransu a ‘bace! Hajja tace”Yanda kika dauki al’amarin ni ba haka na daukeshi ba Kubura nagode kwarai yau ni kikewa gurin haihuwa ko babu komai.” Anti kubura ta kad’a kan ‘yayanta suka fita daga gidan ransu a tsananin ‘bace! Hajja kuwa sai da ta matse hawaye kafin ta mike ta shiga cikin daki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button