NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Inna Hajara ce kadai a palo ita hajja ta shiga daki domin daura alwalar sallahr walha to tana ganin wucewarsa ba tare da ya ko kalli inda take ba sai jikinta yay sanyi a hankali ta mike ta nufi dakin Wasilan…..Ta tarar da ita xaune tana kuka. Zama tayi kusa da ita a hankali tace”Goge hawayenki.” Wasila ta goge hawayenta tana sunkuyar da kanta…..Inna Hajara tace”Ni banzo da niyyar na kashe miki aure ba Wasila, na lura mijinki bashi da hakuri ko kad’an, ni kuma ke nake tausayawa saboda irin wahalhalun da kika sha kafin ki haihu Uwa uba akazo aka yanka ki aka d’inke kamar ‘kwarya, dole a sanya ido sosai a kanki domin ingantuwar lafiyarki! Bayan haka kuma dole ne kafin ki komawa miji sai an gyara miki jikinki domin haihuwar da kikayi duk wata ni’ima da kike dashi babu nida a tunanina ma ina so idan zan tafi gida muje tare dake can in gyaraki sosai da sosai to amma tunda naga take taken mijinki to zan tattara nawa nawa na tafi dama akan dole nake zaune a gidan, bana so yazo ya dinga jin haushina ko ya fahimci cewar nice nake hanaki biya masa bukata.”

Tun kafin Inna hajara ta ‘karasa maganarta ta rike hannuwanta tamau! tana kuka sha’be!sha’be! “Wallahi Inna ba zaki tafi ba sai nayi ar’bain sai kace wata mara gata da galihu! ai haihuwar fari nayi kuma koda zanyi haihuwa goma a gidanan kina da damar da zaki zo ki zauna tare dani tunda ina cikin gidan…..Inna nasan abinda nakeyi nima bazan yarda ya haike min ba kawai ya cuceni bayan ban gama dawowa dai-dai ba, na amince zan jure ko wane irin fushin da zai dauka dani nasan idan ya gaji zai daina..”
Inna hajara tace”A’a Wasila ni bazan so kullum ki dinga kwana da tsiniwar Allah da mala’ikunsa ba, kibi mijinki sau da ‘

kafa kiyi masa biyayya kan abinda yake so ni dai na fad’a miki yau yau zan tafi dan naga kamar haushina yake ji to zai dawo ya tarar na bar masa gidansa.
Wasila ta dinga kuka tana bata hakuri Inna Hajara ta rufe idonta ruf ta fita daga dakin domun zuwa ta had’a kayanta…….Hannunta na kyarma ta d’auki wayarta ta shiga kiransa…..Lokacin yana cikin company sa tare da ma’aikatansa yaga kiran wayar tata ya’ki dauka har yanzu haushinta yake ji
Ta kira ya kai sau biyar bai dauka ba sai kawai ta aje wayar ta fito palo tana goge fuskarta tasan haushinta yake ji shiyasa bai dauki wayarta ba, tana fitowa palo ta tarar Inna hajara da hajja suna fafatawa, Inna Hajara taurin kan tsiya ne da ita ta’ki sauraran hajja hannunta ri’ke da jakar kayanta ta kama hanya ta fita Wasila tabi bayanta har wajen harabar gidan……Garba ya iso gurin da sauri ya karbi jakar kayan hannunta shi baiyi tunanin wani abuba saboda ya dauka inna zata tafi gidane….Can parking ya nufa da jakar kayan ya fito da mota har inda suke tsaye Inna hajara ta bude ta shiga tana ‘bata rai! Wasila kallonta kawai takeyi domin ita har ta gaji da magiya da bata hakuri, tana tsaye har garba yaja motar suka fita daga gidan, ta girgiza kanta ta juya domin komawa ciki tana kokarin mayar da hawayen dake so ya zubo mata.
Tana shiga ta tarar da Hajja a tsaye a tsakiyar palon itama tana cikin alhini na tafiyar Inna hajaran Tace”Wasila kodai wani abu akayiwa hajara ne irin wannan tafiya haka da gaggawa, kuma na lura kamar dai ranta a ‘bace yake.”!
Ta d’an d’auke hawaye a hankali tace”Haka kawai ta tubure wai gida zata tafi babu abinda akayi mata.”
Hajja ta zauna kan kujera jikinta a sanyaye tace”To ai shikkenan Allah ya sauketa lafiya.” Ta amsa da “ameen tana kokarin shiga d’aki.


“Haba Uwani wai dan Allah tun yaushe nake miki magiya kan ki kaimu muga d’akin yarinyar amma kin’ki kaimu kullum nayi miki magana sai kice zamuje to sai yaushe zamuje? kada fa ki manta da cewar kwanaki dani dake mukayi lissafin watannin cikin yarinyar har ki kecewa cikin ya isa haihuwa nace watakila ma ta haihu to kinga yana da kyau muje muga halin da ake ciki.” Kuluwa ce zaune a gaban Uwani take wannan maganar cikin ‘kas’kantar da kanta…….Uwani ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Kuluwan kamar ba itaba wai yau an wayi gari Kuluwa nayi mata magana cikin kalami mai dad’i lallai duniya kenan.

Tace”Kuluwa ba wai bana so muje bane gaskiya bana so muje gidanan kiyi wani abu da zai sanya kima da mutuncinmu ya zube mutumin nan ba karamin mutum bane kuma kinga mu sirikai ne dole mu kama girmanmu ke kuma kuluwa baki da girma sai na jiki idan kin amince cewar xaki kiyaye kuma zaki nutsu sosai to shikkenan sai mu shirya idan Allah ya kaimu dani dake da Kawu da kuma su Inna mai waina muje muga abinda yarinyar ta haifa.”
Cikin kwantar da kai Kuluwa tace”Haba Uwani wallahi bazan aikata abin kunya ba zan kula sosai bazan baki kunya ba insha Allahu.” Uwani tace”Shikkenan to yanzu zan tashi na shirya na nufi gidan Inna Tabawa domin na shaida mata halin da ake ciki.” Kuluwa tace”To hakan yayi bari idan na sauke abinci sai na d’an d’umamaki ruwan wanka kafin ki tafi kiyi sai kinfi jin dad’i.” Mikewa tayi ta nufi kicin……..Uwani tabi ta da kallo cike da mamaki.

Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
76
Koda Rashida ta dawo ta tarar Inna hajara ta tafi itama sai da taji rashin dad’i tayi ta tambayar Wasila dalili, kunya ta hanata fad’a mata kawai sai tace”Rashida kin san dai rigimar Inna hajara dama da kyar na samu ma ta zauna tayi wad’annan kwanakin amma babu wani abu da akayi mata wanda zai sanya ta tafiya kawai dai dama tayi ra’ayi ne.” Rashida ta amince da maganar Wasila suka zauna suna jimamin tafiyar Innar tasu.

To can ‘bangaran su mai girma governor Lawan Rabo sun tada aiki sosai shida mu’karrabansa duk dan ganin yanda al’ummar jahar suka tashi hankalinsu gurin ganin sun rusa tafiyarshi da kuma jam’iyyar da yake ciki gabakid’aya jamiyyar da yake ciki dashi kansa sun daina power gabakidaya jama’a nata komawa jam’iyyar CPC jam’iyyar su Amadu kenan duk ta doke sauran jam’iyyun da suke adawa da junansu……Hankali mai girma governor yayi masifar tashi, babu shakka idan ya tsaya kallon ruwa to kuwa kwad’o zaiyi masa ‘kafa, tuni ya kira ‘yan fadarshi irin su As da mataimakinsa suka zauna zaman meeting inda suka yanke shawarwarin da suke ganin zasu taimaka musu gurin campaig, governor ya fitar da miliyoyin kudi ya rabawa ‘yan gwangila irinsu As yace aje ayi duk abinda ya kamata a cikin jahar domin a jawo hankalin jama’a jam’iyyarsu……..As suka fara aiki gadan gadan inda suka fara rushe rushen gidajan jama’a da masana’antu wai zasuyi babban titin da jirgin ‘kasa zai dinga wucewa, jama’a da yawa suka shiga halin damuwa an rushe musu muhalli ba’a basu diya ba masu sana’oi suma an rugaza musu guri ba’a biyasu ba, a mai dasu gida an tsuganar, takaici ya ishesu sai kawai suka soma shiga gidan redio suna zage zage da fad’in Allah sai ya saka musu wannan zalincin da ake musu…..Mai girma governor ya tafi katsina gurin abokinsa ya samu labarin abinda yake faruwa a jahar tashi, a take ya kira As yace ya shirya da kanshi ya shiga gidan redio yayi bayani wanda zai dauki hankalin jama’ar gari su amince da manufarsu.
As ya shiga gidan redio na salama ya dinga zabga ‘karya da ‘karairayi kan cewar mutukar jama’ar gari sun sake za’bar lawan rabo to babu shakka zasuji dad’i a wannan karon komai zaiyi sauki za’a samu sauyi na rayuwa sannan yace.”Duk wanda aka rushe masa gida da gurin sana’arshi a gurin aikin titin da sukeyi to duk su kwantar da hankalinsu za’a biya su hakkinsu……Ashe jama’ar gari sunyi dafifi a wajen gidan redion koda su As suka fito dashi da ‘yan rakiyarsa da ‘kyar suka sha dan ma da akwai security a tare dasu amma dai dik da haka sai da sukayi raga raga da gilashin motocinsu suna tafad’in “bamayi! kano ta d’an musa ce.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button