YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Muje Zuwa
BINTA UMAR ABBALE
[7/18, 2:01 PM] Bintu: ‘YAR BANGAR SIYASA!!
???? romantic love story????
NA:
BINTA UMAR ABBALE ????
????Manazarta Writes asso
‘Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*PEGE 'DIN YAU NAKI NE*
*Real Eshaa????*
Marubuciyar book d'in.
*NAGA RAYUWA*
Fatan alkairi har karshen rayuwa aysha Allah ya kawo miji nagari wanda zai rike min ke tsakani da Allah????????
~~~~~~~
*Free Pege15*
Cikin nutsuwa Garba yace."Aramma alamu sun nuna kamar kana da ala'ka da masu wancan gidan, dan Allah idan babu damuwa ina so in san wani abu dangane da wata yarinya a gidan mai suna Wasila." Malam mai allo yace."Ni a matsayin mahaifi nake a gurin Wasila da kanwarta Rashida Yahuza mahaifin yaran kanina ne ciki daya muka fito kuma mu 'yan asalin garin garko ne Yahuza yazo kano neman kudi tun yana saurayi sai ya sai gida yayi aure tare da wannan matar wacce ta kasance a matsayin mahaifiyar su Wasila da Rashida......Garba ya katse shi ta hanyar fadin"Alhamdullhi dama abunda nake so naji kenan ashe faduwa tazo dai-dai da zama malam idan babu damuwa zamuje can gidan ubangidana wanda shine ya sanya ni nayi masa bunkice akan asalin iyayen yarinyar to kuma sai nayi katarin had'uwa da kai, kar kadamu arrama idan mun isa sai kayi masa cikakken bayani akan yarinyar." Malam yace."Yaro ina fata dai ba laifi yarinyar tayi ba domin nima abunda ya taso ni kenan saboda na samu labarin cewar tana cin mutuncin manyan mutane a gari tana fakaicewa da siyasa wannan shine dalilin zuwa na garin." Garba yace."Kar ka damu arrama alheri ne insha Allahu muje koma meye zakaji daga bakin mai gidana." Malam yayi shiru yana nazari yana tsoro kar daga zuwan sa ya shiga masifar yarinyar nan tasa a daure shi baiji ba bai gani ba....Girgiza kai yayi yace."Babu damuwa samari muje kawai Allah yasa alheri ne." Garba ya kunna motar yaja suka futa daga cikin unguwar.
Suna tare da Khalifa a harbar gidanshi suna hutawa motar su Garba ta shigo cikin gidan.....Can parking spece ya nufa yayi parking din motar ya fito ya budewa malam mota yana fitowa Idanun Ahamdu suka sauka a kanshi A fuzge yaga suna kama da yarinyar babu tamtama wani nata ne amma babu shakka Garba ya iya aiki bai dauka futa ta farko za'a samu nasara ba to amma yanda yaga kamilin mutum sai yasha jinin jikinsa anya wannan kudi zasu rud'ashi ko dai ya sauya wata hanyar ne dan baiga alamar zalama ta kudi a idon dattijon ba......A nutse ya mike yana masa barka da zuwa dake suna zaune a wata rumfa wacce aka kewaye ta da wasu kujeru masu kyau tsakiyar kujerun katon teble ne da lemuka akai kana ganin gurin kasan na hutawa ne....Malam mai allo ya zauna nutse suka gaisa cikin girmama juna......Garba yace."Yallabai Allah ya takaita mana wahala ina zuwa unguwar nayi katari da wannan bawan Allahn shine yake shaida min shi din shine mahaifin Wasila shima zuwanshi kenan garin to anan na nemi alfarma a gurinshi kan yazo kana son magana dashi."
Cikin girmamawa Ahamadu yace."Alhamdullahi naji dadi da hakan ta faru dama ni nafi so nayi magana baki da baki da mahaifin yarinyar dan haka Garba kana iya tafiya babu damuwa." Garba ya bar gurin yana godiya....Ahamadu ya sake mikewa Malam hannu suka sake gaisawa Yace."Malam kan maganar wannan yarinya ne Wasila.'' Malam mai allo ya kalli Ahamadu ganin nutsuwa da kuma a kamala a tattare dashi ya sanya hankalinsa ya kwanta yace."Alhaji ina fatan dai yarinyar nan ba wani laifi tayi muku ba dan wallahi dukkanin abunda takeyi bamu sani ba tunda bama tare dasu labarin abunda takeyi ne ya iskemu hakan ya sanya hankalinmu tashi, muka yanke shawarar zuwa domun mu tattara su mu koma can inda muke da zama dama kuma zamansu hakan bai dace ba a matsayinsu na 'yaya mata komeye zai iya faruwa da rayuwarsu.
Khalifa yace."Kwarai kuwa malam muma abunda muka hango kenan ya sanya muka sa ayi mana bunkice akan asalin yarinyar sai kuma Allah ya takaita mana lokaci guda kazo gari ashe ma ba a kurkusa kuke ba." Malam yace." Mu 'yan karamar hukumar Garko ne Yahuza mahaifin yaran ciki daya muke dashi mu hudu iyayenmu suka haifa ni ne babba sai Habibu sai shi Yahuza sannan kanwarmu Kattime To shi kadai ne ya tsalle a cikin mu ya tawo nan yake sana'oinsa har Allah yasa ya samu sana'a ya siyi gida kana yayi aure ya hayayyafa yanzu shekaranshi Takwas da rasuwa bayan karamar jinyar da yayi wanda muma sai labarin mutuwarsa mukaji......Dalili kenan da ya sanya nazo da kaina na dauke yaran har da ita mahaifiyar tasu na tafi dasu can garin namu ko sati daya ba suyi ba suka gudo........Tiryan tiryan Malam ya zayyane musu rayuwar dasu Wasila suka dinga yi tun farkon mutuwar mahaifinsu da irin rashin kunyar da mahaifiyarsu ke sawa suyi musu da yanda shi kuma yayi zuciya ya zare hannunsa daga kansu....Sai wannan karon da yaga abun yayi tsamari ya sanya yace bari ya dauki mataki na karshe kan abunda sukeyi.
Ahamadu yace."Arrama yanzu idan ka tafi dasu can Garkon kana da wanda zaka bawa auransu ne."? Malam yace."Ba za'a rasa ba Alhaji kasan shi auran karkara ba'a tsawwala da yawa insha Allahu sati biyu ba zasuyi a gida ba zab daura musu aure."
Yace."To idan babu damuwa ni ina son abani auran babbar kuma bana so a ja dogon lokaci idan da hali wannan juma'ar mai kamawa nake so a daure aure."
Malam yace."Alhaji da dai 'karamar ka dauka dan sai naga kamar tafi babbar hankali hankalin ka zaifi kwanciya da ita karamar." Yace."Kar ka damu malam shi aure ni'ima gareshi watakila ta sanadiyar auran namu sai kaga tayi hankali fiye da tunani mai tunani idan da hali a amince mun in bada sadaki na yanzu." Malam yace."To to ai babu damuwa nima zanfi jin dadin hakan kaga sai in koma gida da karfin gwiwa ta kuma in sanar da 'yan uwa abunda ke faruwa."
Ahamadu yace."Kwarai naji dadin yanda ka yarda dani ka amince min auran yarinyar da wuri ba tare da kaga waliyai na ba insha Allahu ranar juma'a zamu zo tare da kanin mahaifina Wanda shi kadai ne ya rage min a halin yanzu kasancewar nima tun ban kai matsayin wannan shekarun ba mahaifina ya rasu na rayu tare da yan uwansa wannan kuma da kake gani a zaune kusa dani abokina ne sha'kikina tare mukayi karatu kuma muke harkokinmu a tare insha Allahu tare zamu zo dashi ranar juma'a."
Malam yace."To masha Allah Alhaji ai ni ganin farko da nayi maka naji hankalina ya kwanta da kai wallahi babu d'ar! zan baka auran Wasila koda banga Waliyinka ba nasan zaka rike mun ita da kyau da amana, babu abunda zance sai dai ince Allah ya saka da alkairi saboda ka gama min komai tunda har ka yarda zaka auri wannan yarinya." Ahamdu yace."Babu damuwa malam, ai an riga an zama daya kuma Allah dai ya kara girma." Mikew yayi ya nufi cikin gidan..........mintuna goma yayi a ciki ya fito hannunsa rike da wata doguwar takarda dake cike da kudi." Ya mikawa malam na fad'in"Wannan shine sadakin Wasila malam."
Malam ya kalli uban kudin da ya mika masa sai ya girgiza kai a nutse yace."Ashe baka so auran yayi albarka ba Alhaji Annabi Muhammdu SAW yace."Mafi albarkar aure shine karamin sadaki wannan da yayi yawa duk da ban lissafa na gani ba amma idona ya gane min kudi ne masu yawa, saboda haka dubu biyar kacal zaka biya sadakin wannan yarinya."
Ahamadu yace."Malam ka ka'rba don Allah ai ba wani kudi masu yawa ba dubu dari ne kacal kuma kasan dai yanda kudin mu suke basu sa wani daraja kar damu insha Allahu aure zaiyi albarka."
Malam yace."Shi dai ba zai kar'bi wannan zunzurutun kudin ba a matsayin sadakin Wasila ya fiso idan yayi mata aure ta zauna mutuwa ce zata raba.....Ahamadu da Malam suka dinga ta'kardama da jayayya shi ya dage sai ya 'karba shi kuma yace ba zai kar'bi dubu dari ba dubu biyar zai 'karba....Khalifa ne ya raba gardama ya ciro kudi daga jikinsa dubu goma ne ya irga dubu biyar ya mikawa Malam yace."Ga sadakin Wasila daga Ahamadu." Malam ya sanya hannu biyu ya kar'ba yana fadin"Ubangiji Allah ya tabbatar da alkairi Allah ya basu zuria mai albarka." Khalifa ya amsa da "ameen rabbi malam muna godiya da karamci."
Ahamdu yaji haushin abunda khalifa yayi masa amma bai nuna ba sai ya aje takardar kudin kan teble din gabansa dauki wayarshi ya kira Garba......Garba na zuwa yace maza ya fito da mota ta zuba kayan abinci komai da koma yazo ya dauki malam ya kaishi har Garko Garba ya wuce da sauri domin aiwatar da aikin da aka sa shi. Ahamadu yace."Malam yanzu Garba zai kai gida maganar su Wasila kuma da kaina zan sanya a kai maka su har inda kake daga gobe jibi insha Allahu." Yace."To Alhaji Allah ya saka da alkairi ya biya dukanin bukatu na alkairi."
Bayan tafiyar Malam mai allo Khalifa ya kalli Ahmadu yace."Na lura wannan dattijon na arziki ne wallahi sai duk naji jikina yayi sanyi musamman yanda naga ya tsaya kai da fata akan ba zai kar'bi wannan kudin da ka bashi a matsayin kudin sadaki na fahimci yana so auranku da yarinyar yayi albarka wanda kai ba haka abun yake ba a zuciyarka, dan Allah ka kar ka watsa wa mutumin 'kasa a ido ka rike yarinyar nan amana ko dan saboda karamcinsa kamar yanda ka fad'a masa watakila ta sanadiyar auran sai kaga tayi hankali duk abubuwan da suka faru a baya su wuce kamar ba'ayi ba."
Shiru yayi yana nazarin maganar khalifa din yace."Nima jikina yayi sanyi lokacin da naga mutumin sam! ban dauka zanga kamilin mutum daga bangaran yarinyar ba ashe ta fito daga tsatso mai kyau gaskiya wannan mutumin ba duniya ce a gabanshi ba ka duba ka gani kudi a wannan zamanin sam basu gabansa wasu iyayen da suke so in kaje neman auran 'yayansu ka sakar musu kudi a gurinsu hakan burgewa ce, shi kuma na lura albarka kawai yake nema."
Khalifa yace."Shine ai shawarar da nake baka rike masa yarinyar shine zai sanya ya tabbatar da cewa kai d'in mutumin kirki ne.""
Murmushi yayi yace.''Kai nifa ina nan kan bakana wallahi! sai naci uban yarinyar nan wallahi in keta ta kuma in saketa."
Khalifa yace."Subahanallahi! wai me yasa kake hakane? ka sani kake takewa yanzu meye amfanin hakan da za kayi."? Sosa kanshi yayi yace."Ai kai dama ba za kaga amfani ba saboda ba kai akayi wa auran nan da zanyi zanyi shine da manufofi da dama kaga na farko zan tashi daga sunan Gwauro kamar yanda ta fad'a zata zame min garkuwata a siyance na biyu zan dawwamar da rayuwarta a cikin 'kunci da ba'kin ciki in takure ta guri guda in muzguna mata har sai ta durkusa gwiwa bibbiyu tana bani hakuri na uku kuma na taimake ta daga wannan yawace yawacen banzan da takeyi a gari tana zubda mutuncinta na killace ta a guri guda....Na hudu kuma auranta zai wanke ni daga zargin da tasa jama'ar gari suke min....Ita ta nufe ni da sharri ni na saka mata da alkairi kaga anan jama'ar suka ji labarin na aureta za tasha tofin ala tsine da zagi sannan ita da harkar Siyasa har abadah! na biyar bukatata ta biya na raba abokanan adawata da ita tunda yanxu kamar itace a matsayin yarinyar su wacce suke sanyawa nayi musu abu ba tare da shakkar kowa ba, nasan kafin su samu 'yar siyasa mai mutukar a'kida irinta za'a sha wuya, kasancewar siyasarmu ta yanzu ta zama sai a hankali duk inda mutum yasan zai samu nan zaije hakanan za kagansu yau su zagi wancan gobe su zagi wanannan sam basu da gwani mutum in dai zaka bashi na 'batarwa shikkenan magana ta kare, amma ita yarinyar ns fahimci ba wannan ke gabanta ta tsaya bangaransu su kadai shiyasa suka riketa hannu bibbiyu saboda sun lura abokiyar tafiya ce....Kuma kasan ba zasu ta'ba bari tayi aure ba zasuyi ta bata kudi tana shirme a gari rayuwarta ta lalace a banxa a wofi.''''' Khalifa yace."Kayi tunani me kyau gaskiya amma dai duk da haka don Allah ka sassauta mata idan ta shigo.
Murmishi ya saki mai dauke da manufofi da dama ta'be bakinsa yayi yace."Kana 'bata bakin ka ne khalifa yanda yarinyar nan tasa ni 'bacin rai itama ranta sai ya 'baci."
_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/18, 10:18 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
???? romantic love story????
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE ????*
*????Manazarta Writes asso*
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
???? romantic love story????
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE ????*
*????Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
NA KUDI NE…….!
Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za’a tura kudin.0542382124…….Binta Umar gtbank….Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din….07084653262_08089965176 sai na fad’i yanda za’a biya kud’in…..Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars…….90899076_88137740 katin airtal ko orange
Free Pege16
Uwani ta fito daga kicin tana fad’in”Da alama dai mutumin nan ya gaji da tsayuwa ya tafi haba! jama’a wai babu dama aga Allah ya rufawa mutun asiri sai a dinga bakin ciki! kiga mutum da rigima haka kawai ka ni’ko gari gari ya gari kazo kace zaka dauke min ‘yaya saboda munafurci nasan magulamata ne suka kai masa gulma shine shi kuma ya bazamo babbar riga yazo har gidana ya nuna min iko to ni babu wanda ya isa yace zaiyi min iko da ‘yayana ‘yan uwana ma ban d’agawa ‘kafa ballanta wani saboda haka ke Rashida maza maza ki kira Wasila a waya kice tazo yau d’in nan ta dauke mu a mota mu bar nan tunda har wannan tsohon ya soma zuwa shikkenan kuma zai ta daga mana hankali gwara kawai a nemu mu a rasa a unguwar.”
Rashida tace”Ni wallahi tausayinsa nakeji gaskiya Uwani banji dadin abunda kikayi masa ba Kamar uba yake a gurinmu kin tozarta shi a unguwa.” ” Ayyo kina so ki nuna min kinfi kaunarsa a kaina ni dana tsuguna na haifeki naci kashinki da fitsarin ki shine zaki butulce min shi me ya ta’ba tsinana miki a rayuwa.” Rashida tace”Wallahi kafin babanmu ya mutu ya fada min lokacin da aka haifeni da ya rasa yanda zaiyi da hakika can kauye ya nufa gurin Malam mai allo din ya bashi katuwar tinkiya aka rada min suna da ita.” Uwani tayi kasake tana kallon ‘yar tata ashe kafin mijin nata ya mutu sai da ya fada musu abubuwan da suka faru a baya…..”To ai hakika dama dole ce a wuyansu take idan basuyi ba ai sai a kira ki da shegiya gwara ma ki daina wannan magana dan bayan ya bada tinkiya anyi miki rad’in suna babu abunda ya kuma tsinana miki.” Rashida tace.”Gaskiya dai ki daina ci masa mutunci.” Uwani ta fashe da kuka tana fadin”Sai ki zageni Rashida ki fito fili kawai ki zageni yau naga matsayina a gurin ki shiyasa ni Wasila tafi min ke sau dubu duk abunda tasan za tayi ta faranta min rai shi takeyi duk abunda nace tayi tana yi min babu musu ke kuwa fa sai dai ta nemo kudi kina daga kwance kice, to duk rashin mutuncin da kikeyi min sai na fada mata.” Tana gama maganarta ta shige daki tana matse hawaye…..Wayarta ta dauka da Wasilan ta siya mata ta hau kiranta….Lokacin suna tare da mai girma governor suna meeting Wasila taga kiran amma bata dauka ba sai bayan sun fito daga dakin meeting din ta kira ta….Uwani na daga wayar ta fashe da kuka “Wasila maza ki zo gida Rashida na nan tana min rashin mutunci duka na ne kawai ba tayi saboda zuwan Malam mai allo.”
Rai a ‘bace! ta kashe wayar ta nemi numbar Rashidar…..Rashida ta daga wayar tana zumbura baki “Wallahi Rashida ki shiga hankalin ki! dan Kutumar ubanki me malam mai allon ya tsinana miki da har kikewa mahaifiyarki rashin kunya har kin manta irin wahalar da tasha akanmu ashe dama kika bawa malam din yaci mata mutunci kamar yanda ya saba to wallahi sai ranki yayi mugun ‘baci! kan hakan.” ”Aunty Wasila ki saurara kiji abunda yake faruwa.” Rashida ce ke ta magana amma taki sauraranta sai zaginta take cikin jin haushi ta kashe wayar….Wasila ta tsaya tana mamaki! lallai Rashida bata da mutunci ta gama wahala da ita amma ta kashe mata waya….Mahaifiyar tasu ta kira tace”Kinga Uwani na soma zargin yarinyar nan wallahi harda hadin bakinta gurin zuwan Mai allo gidanan dan haka hankalina ba zai kwanta ba komai dare zan shigo unguwar in daukeku ku zauna cikin shiri.” Uwani tace”Nima dama shawarar dana yanke kenan dan tunda malam din yazo nasan sauran ma suna tafe haka kawai su rusa mana rayuwa waye zai koma kauye ya zauna? sai dai duk abunda zasuyi suyi.” Duk dai magana ta kare ku zauna cikin shiri.” Uwani tace “To shikkenan sai kinzo.” kashe wayar tayi ta iske inda Camas take zaune tana kallonta.
Har kusan karfe goma da rabi na dare Garba na layin su Wasila cikin matasa yayi basaja so yake yaga ta inda Wasila zata ‘bullo, shiru asalima tunda ya zauna ko kare bai gani ba a bakin kofar gidan nasu…..Yananan zaune mutane suka fara raguwa saboda dare kowa na tafiya gida shima sai ya yanke shawarar tafiya dama a Mashin yazo roba roba ya sanya mukuli zai kunna kenan ya hango tawowarsu Wasila jikinta sai walwali ya keyi kasancewar material din dake jikinta mai kyalline wani bala’in kamshin turare ya bakunci hancinsa lokacin data giftashi ta suka shige ita da Camas! wace ta nufi gidansu ita kuma ta hau buga kofar gidan……Matasan dake kusa dashi ne suka fara magana kasa kasa…”Shegiya karuwa kawai ina su Mado nanan da sunci ubanta ta gama guje gujen ta dawo karuwar banza da wofi! ai sai munci ubanta wallahi.” Zaginta sukeyi suna kwashe mata albarka garba na jinsu bai ce komai ba yana nan zaune yaga sun fito ita da sauran mutanan gidan…..Gidan suka kulle suka wuce simi simi kamar munafuka…nan yaji matasan dake kusa dashi na fad’in”Ai babu matsiyaciyar uwa sama sa wannan matar duk itace ta sanya ta take wannan rashin mutuncin dazu fa wan mahaifinsu ne yazo suka rufe masa kofa ai wallahi mun kusa tashin su daga unguwar nan.” “Kai kasan me zamuyi ma yanzu.”? girgiza kai yayi yace.” Kone gidan zamuyi dan uwarsu in sun dawo su kwana a waje.” Kai wannan shawara tayi kyau abokina.” Tafawa sukayi suka mike tare…..Garba ganin sun bar gurin sai shima ya hau mashin dinsa yabi bayan su Wasila can ya hangosu tsallaken titi inda tayi parking din motarta suka shiga a take ya bi bayansu amma yanda yake binsu a hankali ba zasu dauka su yake bi ba.
Dake unguwar masu hannu da shuni ce ko ina haske babu duhu da tarin kazanta daga can bakin titi Garba ya tsaya ya kafe mashin dinsa a hankali yabi bayan motar inda yaga ta nufi wani estete wanda manya manya mutane ke zaune a ciki Garba yayi mamaki sosai babu shakka yarinyar samu kudi ganin motar ta tsaya a bakin gate din wani tangamemen gida ginin zamani, yana kallo mai gadi ya bude gate din ta shigar da motar ciki, sai ya juya da sauri ganin sucurity na nufowa inda yake, da sauri ya tashi mashin dinsa ya bar gurin a guje……A daran ya shaidawa Ahamdu unguwar da Wasila take sam baiyi mamaki ba saboda yasan zasu iya yi mata abunda yafi haka, kudi ne gasu nan a banzace ayi abunda ya dace an’kiyi ana watsar dasu a banza a wofi jirgin sama ma zasu iya siya mata mutukar bukatarsu zata biya.
Uwani da Rashida suka gigice ganin ubangidan da Allah ya mallakawa Wasila suka dinga shige da fice a gidan suna ta’be ta’ben abubuwa Uwani dai kusan zautuwa tayi saboda ta masifar rudewar da tayi taga uwar daula da duniyar da ‘yarta ta cikinta ta samu…..Wasila tace “Ko wanne ya dauki daki daya ya ishe shi bukatar rayuwarsa Uwani kinga Abunda Allah yayi mana ko? da kina cewa muje muyi karuwanci shine zamuyi kudi da gaggawa to wannan sana’a da nakeyi mutukar ta karbe ka nan take zakayi arziki yanzu ina da kudi cikin account dina da ban san a dadin su ba kullum ‘yan fadar mai girma governor tura min kudi suke bamu da matsalar komai a halin yanzu Allah ya yaye mana kuncin talauci ba tare da mun aikata sa’bo ba.