NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Cike da takaicinta tace”Dan Allah Kuluwa ki nutsu mana bafa a aljanna kike ba da kike ta wannan rawar jikin haba! ki daina haka dan Allah idan ba haka ba to ni kada ki sake zuwar min gida dan ba zaki zo ki bani kunya ba.” Kuluwa ta hau ya’ke cike da kunya tace”Yi hakuri ‘yar nan al’amarin ya rud’ar dani wallahi ban ta’ba shiga irin wannan daular ba sai yau gaskiya ke d’in ‘yar baiwa ce Allah ya samu a danshin ku.”
Tsaki kawai Wasila tayi ta bar gurin, Uwani tace”Kuluwa kafin muzo gidan nan fa sai da mukayi magana dake wai me yasa kike hakane kada da mai gidan nan ya shigo ki bamu kunya a gabansa.”
Kuluwa tace”Kai jama’a wai ya kuke so nayi ne? to shikkenan bari nayi gum! da bakina na daina sanya albarka tunda dai itace bakwa so nasa.” Rashida tace”Hakan shine yafi alkairi dake.” Kuluwa taja bakinta tayi shuru sai dai muzurai kawai takeyi tana gyara zamanta, haka suka ci abinci mai cike da nama da lemuka masu sanyi

Bayan sun gama cin abincin Hajja ta fito daga daki tana kallon Wasila tace”Yana da kyau ki kira mai gidan a waya yazo su gaisa tunda naji kamar suna cewa yau zasu koma.” Ai kafi ma Wasilan tace wani abu Kuluwa tace”A’a ba yau zamu koma ba sai mun kwana biyu tukkuna dan haka malam yace mu zauna mu yauta tukkuna.” Hajja tace”A’a to masha Allah hakan ma yayi kyau ai babu damuwa.” Ita kanta Hajja ta fahimci matar kamar bata da hankali.
Wasila jikinta yay sanyi ganin abin na Kuluwa naso ya wuce gona da iri babu shakka baza ta so zamansu a cikin gidan ba ba dan komai ba sai dan kada su zauna Kuluwa ta zubar musu da d’an sauran mutuncinsu da suke dashi a idon maigidan dama hakan ma ya aka kaya yana musu wani irin kallo to ballanta kuma yazo yaga irin haukan da Kuluwa takeyi ai raini ne zai sake shiga tsakaninsu……Ke’bewa sukayi da mahaifiyarta Tace”Uwani gaskiya gwara ku tafi ni bana so ku zauna a gidannan saboda waccan matar mara hankali kawai idan Kunyi sallah sai ku tafi.”

Uwani tace”Rabu da shashasha, ai dama mu ba zama zamuyi ba sai kace wasu marasa hankali yau din nan zamu koma tunda Allah yasa mun ganki lafiya da yarinyarki ai anyi barka ita idan zata zauna sai ta nemi guri kwad’ayayyar banza kawai.”
Wasila tace”Ai naga alama so takeyi ta zauna min a gida kuma baza ta zauna ba wallahi.” Uwani tace”To yaushe ma ai ‘kafarmu ‘kafarta.” Wasila ta shiga bata labarin irin zaman da sukeyi dashi da kuma dalilin da ya sanya Inna hajara barin gidan.
Uwani tace”To in banda abinshi shikkenan daga an haihu babu wani gyara sai a koma masa ai ba zakiyi daraja a idonsa ba kada ki yarda ya kusance ki sai kin gyara kanki sannan kin tabbatar wannan d’inkin da akayi miki yayi dai-dai sannan idan kin koma masa a haka yazo yaji wani sauyi ai wulakanci ne zai biyo baya.”
Wasila tace”Nima abinda nake so ya fahinta kenan ya kasa fahinta.” Uwani tace”Aikuwa ba zai ta’ba fahimta ba tunda idanunsa sun rufe kiyi kokari kawai ki san yanda zakiyi ki biya masa bukatarsa idan ta taso kuma kada ki dinga yi masa rashin kunya tunda kinga ba sa’anki bane ni da nake mahaifiyarki watakila ma ya girme ni.” Hawaye ta share tace”Uwani nifa bana mishi rashin kunya sai jiya da yau da safe kuma duk shine ya jawo kin san dama can ni bana shiri da wanda ba zai ga darajar iyayena ba Uwani banta’ba jin kaunarki da tausayinki cikin raina ba sai da na haihu sannan na tabbatar da cewar Uwa uwace kuma dolene kayi kishinta koda mahaukaciya ce.” Uwani tayi murmushi a hankali tace”Ai dama baka ta’bata sanin me duniya take ciki sai ka haihu tukkuna zakayi hankali Allah yay miki albarka, dake da d

uk zuriar da zaki samu.” Wasila ta amsa da ameen tana goge hawaye ta mike a nutse ta shiga janyo manya manyan akwatinan dake gefe a jere
Manya manya atamfofi ta shiga fitowa dasu da mayafai masu kyau da tsada, ta zubesu gaban Uwani tace”Ki za’bi wad’anda sukayi miki sauran kuma sai ki bawa su Inna mai waina.” Uwani ta shiga d’aga atamfofin tana dubawa tace”Masha Allahu mungode sosai Allah yayi miki albarka.” ta amsa da ameen tana zuba mata kayan cikin sabuwar akwati…..Wani dan karamin akwati ta dauko ta bude kudi masu yawa ne a ciki ta tura gaban Uwanin tace”Ki d’ibi iya yanda kike so wannan kud’in da tarin atamfofin nan na samesu ne a haihuwar da nayi….Uwani ta tsorata da ganin Uban kudin dake cikin akwatin tace” Ki dai bani abinda kikayi niyya Wasila duk wannan kudin naki ne.”? Girgiza kanta tayi tace”Uwani basu kadai bane ma kinga wad’annan takardun shaidar mallakar rumfuna ne cikin babbar kasuwar dake cikin gari (sabon gari) wanda maigidan ya mallaka min duk saboda ya sameni cikkakiyar budurwa yanzu haka ban san iya adadin kudin da ake samu ba cikin ko wace rana, yace dai zamuje a bude accont ya dinga sanya min kudin a ciki.” Uwani ta fashe da kuka tana kallon ‘yar tata tace”Nagode Allah da mazon Allah da Allah be sanya kun d’auki hud’ubata ba kun zubar da mutuncinku a titi nasan da mutumin nan be sameki cikkakiyar mace ba da ba zai miki wannan halaccin ba, kuma da tuni zamanku Baiyi nisa irin haka ba (‘kalube gare ku ‘yan mata kuyi tattalin budurcinku domun ku mi’ka shi ga wanda ya dace shine mijin auranku, koda namiji bai maka kyauta ba to abin alfahari ne ya sameki cikakkiyar mace)

Wasila tace” Kinga dama abinda nake ta so ki gane krnan nima nasan da bai sameni da budurci ba da tuni ya sakeni wallahi.” Uwani ta goge hawaye tace”A koda yaushe ina alfahari dake Wasila kuma kullum cikin shi miki albarka nake shiyasa kike ta samun cigaba a rayuwarki, nasihata zuwa gareki shine kiyi wa mijinki biyayya ku zauna lafiya da juna kada naji kada kuma nagani yanzu wannan mutumin shine uwarki da ubanki kuma shine gatanki duk wani umarni da zai baki kibi mutukar bai sa’bawa addinin Allah ba.” Wasila tace”Insha Allah Uwani zanyi kokari nagode……. Wasila ta irgi kudi kimanin dubu dari biyu ta zuba mata cikin akwatin tace “Uwani gashinan ki siyi waya kiyi sana’a da sauran ga numbar wayata zan rubuta miki idan kun koma gida sai ki kirani mu dunga gaisawa duk kuma abinda kike so ki siya kici abinda baki dashi kiyi min waya insha Allah zamu zo nida rashida bada jimawa ba.” Uwani tace”Kudin da kika bani basuyi yawa ba kuwa kada na aje Kuluwa ta sace.” Wasila tace”Kada ki aje akwatin a gidanta ki kai kayanki kidan Inna Tabawa.” Uwani tace”Yawwa to hakan zanyi.” Mi’kewa sukayi a tare suka fito palo, suka tarar da Rashida da Kuluwa sai musayar yawu sukeyi Hajja na musu dariya Kuluwa da dai taga kowa nayi mata kallon mahaukaciya sai ta shiga taitayinta ta kimtsa kanta sai dai har yanzu ba ta daina mamaki da al’ajabi ba.

Uwani tace”To Hajja mun fito mu zamu tafi.” Hajja tace”A’a ba zaku tsaya maigidan yazo ba ku gaisa.” Uwani tace”Ai yamma tayi.” Hajja tace”Kuma da naji Kuluwa tace kwana biyu zakuyi.” Uwani tace”Haba Hajja kamar wasu marasa hankali ai tunda munga lafiyar yarinya da abinda ta haifa zaman me zamuyi.” Kuluwa tayi saurin kallonta tana so tayi magana, Uwani tayi bala’in shan kunu babu fuska, Kuluwa ta sunkuyar da kanta ‘kasa ranta duk a ‘bace! lallai idan sun koma gida sai ta shukawa Uwani rashin mutunci tunda tana ba’kin cikin su zauna suyi kwana biyu su dandali arziki.
Hajja tace”To ke Wasila baki kira mijin naki a waya ba, ai be dace ba ace su zo baizo sun gaisa ba.” Tace.”Hajja kina ji fa Inna Tabawa tace shine ya tura aka d’aukosu ai yasan da zuwansu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button