NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

kananun yara kenan ya tabbata yanzu inda Zeey ya aura lalla’bashi zata dinga yi tamkar ‘kwai amma wannan ‘kwalar ta sameshi a ‘bagas tana masa abinda ranta yake so, abincin ya zuba duk ya ‘bata daining din yana soma cin abincin Zeey ta kira wayarshi, koda ya duba yaga numbarta sai ya share ya’ki dauka, Zeey kuwa tun ranar da ya saurareta har yana cewa zaiyi shawara take jin tamkar an tsomata a aljanna gani take ma kamar har ya aure ta ya gama, Shine fa ta dingi kiran wayarsa babu ji babu gani, kuma tun jiya bai dauka ba, amma da ike bata da zuciya ba ta daina ba.
Yanzu ta kira ya kai sau takwasa yaki dagawa abincinsa kawai yake ci hankalinsa a kwance, yana goge bakinsa wani kiran ya sake shigowa wanda yay dai-dai da fitowar Wasila daga dakinta, kafad’arta sa’be da baby zahra tana d’an kuka da harbe harbe……Yana ganin fitowarta yay saurin daukar wayar ya bude murya sosai ya mike daga daining din ya nufi palon yana magana da Zeey.
Maganarsa ce ta sanya ta juyo da sauri dan ba tayi tsammanin yana palon ba, ta dan tsaya tana kallonshi lokacin da yake kokarin zama kan kujera yana dariya da fad’in “Zeey rigimarki yawa gareta yanzu yanzu na fito daga wanka naga kiran wayarki nima ban jima da shigowa gida ba.”
Taji gabanta yayi muguwar fad’uwa jin hannunta na rawa ya sanya ta ri’ke baby zahra da kyau! Yarinyar ta soma kuka tana cilla kafafu! da sauri ta dauke kainta ta juya ta cigaba da tafiya dakinsu Hajja ta nufa.
Kukan momynsa ne ya sanya duk abinda yake yi ya fita daga ranshi dan a rayuwarsa ya tsani yaji tana kuka yay saurin datse wayar yana fad’in “Ki bari zan kira ki anjima yanzu ina da uziri.” Mikewa yay yabi bayanta dakin.
Sai ya tarar da babyn Zahra hannun Hajja tana duba cikinta da ya dan kumbura. Yarinyar sai kuka takeyi, Hajja tace”Kuma da kika bata nono ta kar’ba.”? Murya na dan rawa tace”Eh mana bacci fa takeyi kawai ta tashi tana kuka nasa mata nono a bakinta ta’ki kar’ba shine nace to ko cikinta ne ke ciwo.”
Hajja tace”Da alama dai cikin nata ne ke ciwo dan gashinan ya nuna alama.”
Yakarasa kusa dasu dan har jikinsa ma na gogar nata ta kauce da sauri ta bashi hanya, ya tsaya gaban Hajjan yana kallon babyn yace.”Hajja meke damunta ne.”?
Hajja tace”Cikinta ne ke ciwo da alama dan gashinan ya kumbura.”
Ya dan tsuguna yana duba yarinyar hannunsa ya sanya ya dan bubbuga cikin yaji dummm! hankali a tashe ya kalleta tana tsaye itama jikinta dik yay sanyi yace.”Ina magungunanta.”? Tace”Suna d’aki.” Cike da bada umarni yace.”Kije ki dauko.” Fita tai daga daga d’akin,
Ta dawo dakin hannunta rike da wani d’an kwando da kwalayen magunguna a ciki.
Kar’ba yay yana duddubawa, kwata kwata babu maganin ciwon ciki a ciki.
Hajja Tace.”Ai duk ba wannan ba ke Wasila maza jeki kicin ki d’an had’a ruwan d’umi da gishiri kad’an ki kawo min na bata insha Allah ko yaya inda ya shiga cikinta za tayi gyatsa watakila kin bata nono a kwance ne.”
Wasila tace”Ina bata nono bacci ya daukeni sai kawai na kwanta ina kuma kwanciya ta fara kuka shine na bata nonon a kwance.”
Hajja tace”Ai kinji matsalar dama! dan Allah ku daina bawa ‘yayanku nono a kwance yana janyo musu illah babba har ‘kwa’kwalwa yana ta’ba musu idan suka ‘kware a haka sai kiga an samu matsala.” Ta bude baki kenan za tayi magana ya katseta, fuska a daure murya a kausashe yace.”Ai rashin hankaline dama kawai ki kwanta kina bawa yarinya nono a kwance meye amfanin hakan, ke zaki iya cin abinci akwance ne? Abinda kika kasan ba zaki iya ba to kada ki sake kwatantashi kan yarinyar nan! gashinan kin jawo mata lalura.”
Ba tare da tace masa komai ba ta kad’a kanta ta fice daga d’akin zuciyarta kamar zata babbake saboda tsabar bakin ciki da takaici…..Koda ta shiga kicin din ma kasa kata’bus tayi dan tama manta abinda ya shigar da ita, zama tayi kan wata kujera tana kuka ya kufce mata.
Wai shin dame zataji ne? a cikin gidanan kullum babu kwanciyar hankali abu kadan sai masifa daga kawai ta bawa yarinya nono a kwance sai ace taja mata lalura duk dai so da kaunar da yake wa yarinyar bai kai ya nata ba itace ta haifeta tasha wahalar daukar nauyin cikinta kafin tazo duniya kome za

i nuna akan yarinyar bai kai ya ita ba…………Jin shuru bata dawowa yabi bayanta a fusace!
Ya lura sa yarinyar nan so take ta kashe masa ‘yarsa….Sai dai me? yana shiga kicin din ya tarar da ita ta had’a kai da gwiwa tana kuka, sai kuma jikinsa yay sanyi a hankali ya shiga kicin din motsinsa ya sanya ta d’ago kanta da sauri! ganinsa ya sanya ta saurin mai da kanta, bai kalli inda take ba ya soma dube dube a kicin din kwalbar gushirin ya d’auko dake saman kanta ya bud’e ya samu cup karami ya zuba kadan kana ya tsiyayi ruwan d’umi dai-dai misali ya dan motsa ruwan da gishirin suka had’e sai da ya fara sawa a bakinsa yaji dai-dai sannan ya wuce ya fita daga kicin din hannunsa rike da cup din ba tare da ya kalli inda take raku’be ba.

Yana shiga da’kin da ruwan gishirin a hannunsa Hajja ta kar’ba a hankali ta dinga dandala mata a bakinta tana tsotsewa sai da tayi mata sau uku sannan ta mike tana kokarin sata a kafad’a, Rashida tace”Hajja koma ki zauna kawo in dan zagaya da ita.”
Hajja ta zauna tana fad’in ” A kafad’a zaki sanyata insha Allah yanzu za tayi gyatsa.” Rashida ta kar’bi babyn tasa a kafada ta shiga zagaye da ita a dakin…..Cikin ikon Allah kuwa ta daina kukan da takeyi ta shiga sauke ajiyar zuciya tana sakin gyatsa.
Hajja tace”Alhamdullhi yanzu zakaga tayi bacci.”
Yace.”Ai gwara tayi baccin Hajja yarinya kankanuwa cikinta yay irin wannan kumburin wanda ko a gurin babba ma zaiji jiki ballanta yaro karami irinta.”
Hajja tace”Mafi akasari dama ‘kananun yara kamarta sunayin irin wannan kumewar cikin, sai hankali suke dainawa wasu kuwa sai suyi kwana da kwanaki ma basuyi bayan gari ba.” Yace.”Idan hakane kuwa al’amarin akwai ban tausayi wallahi.” Hajja tayi murmushi tare da gyara kwanciya tana fad’in ” to nidai sai da safe jama’a ina baccina tsohuwa ta tasheni dan dai kawai sunan kishiyata ne da ita shiyasa na saurareta da badan taci darajar sunan Yafindo ba to da sai dai ta nemi wanda zai rarrasheta.”
Rashida tace”Kai Hajja ai yanzu ma bake kika rarrasheta ba Momynra ce.”
Hajja na hamma tace”Haka kika ce ko.”? Rashida na dariya tace”Ai gaskiya na fada Hajja gani ina rarrashinta har tayi bacci kice kece kika rarrasheta.”
Hajja tace”Shikkenan dan dai ba’a fatan cuta ne da sai nace gobe ma rana ce.”
Rashida tasa dariya tana dan bubbuga bayan baby zahran wacce ke lumshe ido bacci na fuzgarta…..A hankali yace.”Kawota nan Rashida kema kije ki kwanta an tasheku kuna bacci ko.”
Cike da jin nauyi ta mika masa yarinyar tace”Haba babu komai Wallahi kaga ma bacci zatayi.” Ya kar’be ta tare da rungumeta a jikinsa, yace.”Ki dinga yiwa yayarki fad’a har yanzu ta’ki hankali.” Kanta ta sunkuyar tana d’an murmushi, ya kama hanya ya fita daga dakin rungume da yarinyarsa a jikinsa.
Tana kwance a gado tana tunanin rayuwa ya tura kofar dakin ya shigo, rufe idanunta tayi taki yin kwakkwaran motsi mugun haushinsa takeji dan duk wani girma da ‘kimarsa da take gani ada yanzu sun zube a idonta.
A hankali ya kwantar da babyn a gadonta, ya dan tsaya a kan yarinyar minti biyar ya tofe mata jikinta da addua kana ya juya da niyyar fita daga dakin.
Ja yay ya tsaya yana tunani, sai kuma ya bud’e kofar dakin ya fita, tana jin fitarsa ta bude idanunta ta mike zaune tana jan tsaki! Yarinyar ta dauko ta dawo da ita kusa da ita ta kwanta tare da rufe jikinta da bargo, bacci har ya soma daukarta taji an bude dakin an shigo shine dai ya kara shigowa, dake ta kashe fitilar dakin sai ya kunna wayarsa yana duba gadon babyn, wayam babu ita, da sauri ya kalli bed din ya gansu a lullebe! a jiyar zuciya ya sauke, ya kashe wayarsa ya aje saman bedside ya zare jallabiyar jikinsa dake akwai singlet a jikinsa da gajeran wando sai kawai ya shiga cikin bargon nasu yay kwanta rigingine fuskarsa na kallon rufin dakin, ya dora hannuwansa a kirjinsa, yana addua, sai da ya gama tukkuna ya tofe musu jikinsu gabad’aya kana ya rufe idanunsa, Wasila gabanta tun yana fad’uwa har ya daina fad’uwa ganin tunda ya kwanta baiyi kuskuran koda rik’e d’an yatsanta ballanta yay mata wani abun asali ma ya bada tazara mai yawa a tsakaninsa da ita sanda tayi dubarar juyawa ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button