YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

fahimci hakan……Al’amarin yay masifar ‘bata mata rai! da kyar ta samu bacci ya dauketa, saboda tsabar damuwa da ‘bacin ran da take ciki.
Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE‘Yr Bngr Sys
78
Sa’ko na mussaman zuwa gareka Amadu ‘kawayen Wasila irin su Mumy Farhan, Bomis Zainab kankara Mrs Aliyu Nafisa Buhari Hauwa Chindo, Sakina Ummee da dai sauransu, sunce kayi hakuri dan Allah karkayiwa Wasila kishiya kayi mata uziri saboda yarinya ce, idan kuma ka kuskura ka ‘kara aure to zaka gane baka da wayo dan duk wacce zaka aura ba zata kama ‘kafar Wasila ba, zaka dawo inda kake salati kana kiran sunan Allah???????? babu ruwana Sistar Sakina ce tafad’a???????? sannan Sistar Jamila tace duk wacce zaka aura sunanta salamatu salam dan ba zata iya da jarabarka ba???? babu ruwana! Jamila da Ummee ne suka fad’a ni dai ‘yar aike ce……Momyna tace kayi auranka dan ba Wasila ce kadai mace ba, takwara Fatima Yakubu ma haka tafad’a Sai sistar Hadiza Shall itama haka tace ka more rayuwarka, Shafa’a S Yari da Bilba sunce kayi aure ka more rayuwarka???????????? ni dai na isar da sa’kona Amadu sai ka yanke shawarar da zata fishe ka, nima nace ba Wasila ce kad’ai autar mat…….????????
Cikin sanyin jiki suka koma cikin gidan Hajja ta gansu duk babu kuzari a tare dasu tace”Ai kam ni kaina naso su zauna su danyi kwana biyu ku samu sakewa da mahaifiyarku amma ace daga zuwa sai su tafi wallahi banji dadin hakan ba sai kace wad’anda ake kora.”
Rashida ta goge hawaye tace”Nima naso su zauna wallahi yanzu anti Wasila yaushe zamuje to.” Wasila ta kalleta ranta duk babu dad’i tace.”Sai an d’an kwana biyu baby tayi ‘kwari zamuje insha Allahu.” Hajja tace”Kwarai kuwa hakan yana da kyau, Allah ya kaimu ya bamu lafiya mai amfani.” Duk suka amsa da “ameen.”
To har dai kusan goma da wajan rabi bai shigo gidan ba Hajja na kokarin shiga daki ta kwanta ya shigo da sallama a bakinsa……Dukaninsu suka amsa suna masa sannu da zuwa.
Ya kalli Hajja yace.”Ashe baki kwanta ba hajja ko kema kallon kike.”? Tace”Oh!oh kai nake ta jira ka dawo ai.” Yace.”To Allah yasa lafiya.”Ganin yana ‘kokarin zama ya sanya ta mi’ke a hankali ta bar gurin, Rashida ma ganin ‘yar uwarta ta tashi sai itama tayi yun’kurin mi’kewa yace.”Rashida koma kiyi zamanki ya kina kallo zaki tashi kuma.”
Cike da kunya da jin nauyi ta koma ta zauna ta maida hankalinta kan tv…..Hajja tace” Dazu munyi ba’ki a gidanan na sanya Wasila tayi kiranka a waya kazo ku gaisa duk da nasan da cewar kasan da zuwan nasu, bai kamata ace suzo har su tafi baka zo kun gaisa da juna ba.”
Ya d’an dafe kansa yana girgixa kai ya kai minti uku a haka kafin ya d’ago kansa yana kallon Hajjan yace.”Wallahi Hajja na manta shaf! ni da kaina na sanya Garba yaje ya daukosu amma kuma banyi tsammanin yau zasu koma ba shiyasa kwata kwata ban mai da hankalina gurin dawowa gida da wuri ba.”
Hajja tace”Aikuwa ko awanni uku basu cika ba suka tafi dan babu yanda banyi dasu su zauna su kwana biyu ba suka ki.”
Yace.”Ashsha! nima ban so hakan ba naso mu gaisa dasu wallahi amma babu damuwa Insha Allahu zamu shirya muje idan momy tayi kwari.”
Hajja tace”To yawwa yanzu naji kayi magana dan haka naji ita Wasilan ma ta fad’a to dan Allah ka mai da hankali kada ka shiririce ka kai yaran nan su kwana biyu tare da mahaifiyarsu.”
Yace.”Insha Allah Hajja.” Mikewa yay yace.”Bari na shiga nayi wanka.” Hajja tace”To sai da safe dan nima shiga zanyi na kwanta.”
Yace.”Hajja Allah ya tashemu lafiya.” Hajja ta mike ta nufi daki shima ya nufi dakinsa. suka var Rashida ita kadai tana kallo.
Wanka yay ya fito yana mamakin zuwan bakin da kuma tafiyarsu a gaggauce baiji dad’i ba gaskiya sai kace wad’anda ake kora ai sa bari su kwana tukkuna sai su koma gida, zuciyarsa ta shiga wasi-wasi kan Wasila yana tunanin kamar itace za tace su tafi tunda gashi tana fad’awa Hajja zasuje idan ankwana to kuwa idan hakane nufinta babu inda za taje duk wanda ke son ganinta daga can garin sai da yazo koda kuwa mahaifiyarta ce yana da inda zai sauketa, amma b
abu inda zataje masa da yarinya suje suyi kwana da kwanaki a wani guri.
Cikin jallabiya ruwan madara ya fito palon….Shuru dan Rashida ma bacci yaci karfinta ta kashe kayan kallo taje ta kwanta…..Daning ya zauna yana kokarin zuba abinci, wai kamar mara mace shike hidima da kanshi illar auran ‘kananun yara kenan ya tabbata yanzu inda Zeey ya aura lalla’bashi zata dinga yi tamkar ‘kwai amma wannan ‘kwalar ta sameshi a ‘bagas tana masa abinda ranta yake so, abincin ya zuba duk ya ‘bata daining din yana soma cin abincin Zeey ta kira wayarshi, koda ya duba yaga numbarta sai ya share ya’ki dauka, Zeey kuwa tun ranar da ya saurareta har yana cewa zaiyi shawara take jin tamkar an tsomata a aljanna gani take ma kamar har ya aure ta ya gama, Shine fa ta dingi kiran wayarsa babu ji babu gani, kuma tun jiya bai dauka ba, amma da ike bata da zuciya ba ta daina ba.
Yanzu ta kira ya kai sau takwasa yaki dagawa abincinsa kawai yake ci hankalinsa a kwance, yana goge bakinsa wani kiran ya sake shigowa wanda yay dai-dai da fitowar Wasila daga dakinta, kafad’arta sa’be da baby zahra tana d’an kuka da harbe harbe……Yana ganin fitowarta yay saurin daukar wayar ya bude murya sosai ya mike daga daining din ya nufi palon yana magana da Zeey.
Maganarsa ce ta sanya ta juyo da sauri dan ba tayi tsammanin yana palon ba, ta dan tsaya tana kallonshi lokacin da yake kokarin zama kan kujera yana dariya da fad’in “Zeey rigimarki yawa gareta yanzu yanzu na fito daga wanka naga kiran wayarki nima ban jima da shigowa gida ba.”
Taji gabanta yayi muguwar fad’uwa jin hannunta na rawa ya sanya ta ri’ke baby zahra da kyau! Yarinyar ta soma kuka tana cilla kafafu! da sauri ta dauke kainta ta juya ta cigaba da tafiya dakinsu Hajja ta nufa.
Kukan momynsa ne ya sanya duk abinda yake yi ya fita daga ranshi dan a rayuwarsa ya tsani yaji tana kuka yay saurin datse wayar yana fad’in “Ki bari zan kira ki anjima yanzu ina da uziri.” Mikewa yay yabi bayanta dakin.
Sai ya tarar da babyn Zahra hannun Hajja tana duba cikinta da ya dan kumbura. Yarinyar sai kuka takeyi, Hajja tace”Kuma da kika bata nono ta kar’ba.”? Murya na dan rawa tace”Eh mana bacci fa takeyi kawai ta tashi tana kuka nasa mata nono a bakinta ta’ki kar’ba shine nace to ko cikinta ne ke ciwo.”
Hajja tace”Da alama dai cikin nata ne ke ciwo dan gashinan ya nuna alama.”
Yakarasa kusa dasu dan har jikinsa ma na gogar nata ta kauce da sauri ta bashi hanya, ya tsaya gaban Hajjan yana kallon babyn yace.”Hajja meke damunta ne.”?
Hajja tace”Cikinta ne ke ciwo da alama dan gashinan ya kumbura.”
Ya dan tsuguna yana duba yarinyar hannunsa ya sanya ya dan bubbuga cikin yaji dummm! hankali a tashe ya kalleta tana tsaye itama jikinta dik yay sanyi yace.”Ina magungunanta.”? Tace”Suna d’aki.” Cike da bada umarni yace.”Kije ki dauko.” Fita tai daga daga d’akin,
Ta dawo dakin hannunta rike da wani d’an kwando da kwalayen magunguna a ciki.
Kar’ba yay yana duddubawa, kwata kwata babu maganin ciwon ciki a ciki.
Hajja Tace.”Ai duk ba wannan ba ke Wasila maza jeki kicin ki d’an had’a ruwan d’umi da gishiri kad’an ki kawo min na bata insha Allah ko yaya inda ya shiga cikinta za tayi gyatsa watakila kin bata nono a kwance ne.”
Wasila tace”Ina bata nono bacci ya daukeni sai kawai na kwanta ina kuma kwanciya ta fara kuka shine na bata nonon a kwance.”
Hajja tace”Ai kinji matsalar dama! dan Allah ku daina bawa ‘yayanku nono a kwance yana janyo musu illah babba har ‘kwa’kwalwa yana ta’ba musu idan suka ‘kware a haka sai kiga an samu matsala.” Ta bude baki kenan za tayi magana ya katseta, fuska a daure murya a kausashe yace.”Ai rashin hankaline dama kawai ki kwanta kina bawa yarinya nono a kwance meye amfanin hakan, ke zaki iya cin abinci akwance ne? Abinda kika kasan ba zaki iya ba to kada ki sake kwatantashi kan yarinyar nan! gashinan kin jawo mata lalura.”
Ba tare da tace masa komai ba ta kad’a kanta ta fice daga d’akin zuciyarta kamar zata babbake saboda tsabar bakin ciki da takaici…..Koda ta shiga kicin din ma kasa kata’bus tayi dan tama manta abinda ya shigar da ita, zama tayi kan wata kujera tana kuka ya kufce mata.