NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wai shin dame zataji ne? a cikin gidanan kullum babu kwanciyar hankali abu kadan sai masifa daga kawai ta bawa yarinya nono a kwance sai ace taja mata lalura duk dai so da kaunar da yake wa yarinyar bai kai ya nata ba itace ta haifeta tasha wahalar daukar nauyin cikinta kafin tazo duniya kome zai nuna akan yarinyar bai kai ya ita ba…………Jin shuru bata dawowa yabi bayanta a fusace!
Ya lura sa yarinyar nan so take ta kashe masa ‘yarsa….Sai dai me? yana shiga kicin din ya tarar da ita ta had’a kai da gwiwa tana kuka, sai kuma jikinsa yay sanyi a hankali ya shiga kicin din motsinsa ya sanya ta d’ago kanta da sauri! ganinsa ya sanya ta saurin mai da kanta, bai kalli inda take ba ya soma dube dube a kicin din kwalbar gushirin ya d’auko dake saman kanta ya bud’e ya samu cup karami ya zuba kadan kana ya tsiyayi ruwan d’umi dai-dai misali ya dan motsa ruwan da gishirin suka had’e sai da ya fara sawa a bakinsa yaji dai-dai sannan ya wuce ya fita daga kicin din hannunsa rike da cup din ba tare da ya kalli inda take raku’be ba.

Yana shiga da’kin da ruwan gishirin a hannunsa Hajja ta kar’ba a hankali ta dinga dandala mata a bakinta tana tsotsewa sai da tayi mata sau uku sannan ta mike tana kokarin sata a kafad’a, Rashida tace”Hajja koma ki zauna kawo in dan zagaya da ita.”
Hajja ta zauna tana fad’in ” A kafad’a zaki sanyata insha Allah yanzu za tayi gyatsa.” Rashida ta kar’bi babyn tasa a kafada ta shiga zagaye da ita a dakin…..Cikin ikon Allah kuwa ta daina kukan da takeyi ta shiga sauke ajiyar zuciya tana sakin gyatsa.
Hajja tace”Alhamdullhi yanzu zakaga tayi bacci.”
Yace.”Ai gwara tayi baccin Hajja yarinya kankanuwa cikinta yay irin wannan kumburin wanda ko a gurin babba ma zaiji jiki ballanta yaro karami irinta.”
Hajja tace”Mafi akasari dama ‘kananun yara kamarta sunayin irin wannan kumewar cikin, sai hankali suke dainawa wasu kuwa sai suyi kwana da kwanaki ma basuyi bayan gari ba.” Yace.”Idan hakane kuwa al’amarin akwai ban tausayi wallahi.” Hajja tayi murmushi tare da gyara kwanciya tana fad’in ” to nidai sai da safe jama’a ina baccina tsohuwa ta tasheni dan dai kawai sunan kishiyata ne da ita shiyasa na saurareta da badan taci darajar sunan Yafindo ba to da sai dai ta nemi wanda zai rarrasheta.”
Rashida tace”Kai Hajja ai yanzu ma bake kika rarrasheta ba Momynra ce.”
Hajja na hamma tace”Haka kika ce ko.”? Rashida na dariya tace”Ai gaskiya na fada Hajja gani ina rarrashinta har tayi bacci kice kece kika rarrasheta.”
Hajja tace”Shikkenan dan dai ba’a fatan cuta ne da sai nace gobe ma rana ce.”
Rashida tasa dariya tana dan bubbuga bayan baby zahran wacce ke lumshe ido bacci na fuzgarta…..A hankali yace.”Kawota nan Rashida kema kije ki kwanta an tasheku kuna bacci ko.”
Cike da jin nauyi ta mika masa yarinyar tace”Haba babu komai Wallahi kaga ma bacci zatayi.” Ya kar’be ta tare da rungumeta a jikinsa, yace.”Ki dinga yiwa yayarki fad’a har yanzu ta’ki hankali.” Kanta ta sunkuyar tana d’an murmushi, ya kama hanya ya fita daga dakin rungume da yarinyarsa a jikinsa.
Tana kwance a gado tana tunanin rayuwa ya tura kofar dakin ya shigo, rufe idanunta tayi taki yin kwakkwaran motsi mugun haushinsa takeji dan duk wani girma da ‘kimarsa da take gani ada yanzu sun zube a idonta.
A hankali ya kwantar da babyn a gadonta, ya dan tsaya a kan yarinyar minti biyar ya tofe mata jikinta da addua kana ya juya da niyyar fita daga dakin.
Ja yay ya tsaya yana tunani, sai kuma ya bud’e kofar dakin ya fita, tana jin fitarsa ta bude idanunta ta mike zaune tana jan tsaki! Yarinyar ta dauko ta dawo da ita kusa da ita ta kwanta tare da rufe jikinta da bargo, bacci har ya soma daukarta taji an bude dakin an shigo shine dai ya kara shigowa, dake ta kashe fitilar dakin sai ya kunna wayarsa yana duba gadon babyn, wayam babu ita, da sauri ya kalli bed din ya gansu a lullebe! a jiyar zuciya ya sauke, ya kashe wayarsa ya aje saman bedside ya zare jallabiyar jikinsa dake akwai singlet a jikinsa da gajeran wando sai kawai ya shiga cikin bargon nasu yay kwanta rigingine fuskarsa na kallon rufin dakin, ya dora hannuwansa a kirjinsa, yana addua, sai d

a ya gama tukkuna ya tofe musu jikinsu gabad’aya kana ya rufe idanunsa, Wasila gabanta tun yana fad’uwa har ya daina fad’uwa ganin tunda ya kwanta baiyi kuskuran koda rik’e d’an yatsanta ballanta yay mata wani abun asali ma ya bada tazara mai yawa a tsakaninsa da ita sanda tayi dubarar juyawa ta fahimci hakan……Al’amarin yay masifar ‘bata mata rai! da kyar ta samu bacci ya dauketa, saboda tsabar damuwa da ‘bacin ran da take ciki.

Littafin na kudi ne…..!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
79
Wajejen ‘karfe uku da rabi ya farka ya lalubi wayarshi ya kunna haskenta yana dubasu Baby Zahra bacci take sosai da’alama kuma tana jin dadin baccinta, fuskar Wasila ya haske ya dan tsira mata ido sai yaga kamar fuskarta ta ta d’an kumbura mussaman fatar idonta alamu ya nuna kafin tayi bacci taci kuka ta koshi, ya jima yana kallon fuskarta yana jin wani irin tausayinta na ratsa jikinsa, ya girgiza kanshi a hankali ya mika hannunsa kan hannunta data dan kwanta akansa hakan zai iya janyowa hannunta data kwanta akai yayi mata tsami! gyara mata yake kokarin yi ta bud’e idonta tana dan mi’ke kafafunta, hakan da tayi sai ya dan rankwafo jikinta, tayi gaggawar mikewa zaune shi kuma yay saurin sauka daga bed din ya kama hanya ya fice daga dakin, Shuru tayi tana tunani to da me zaiyi matane? bata da mai bata amsa, sai kawai ta kunna fitilar dakin haske ya gauraye ta kalli agogo taga hudu saura minti ashirin har an soma kiran sallahr farko….A hankali ta dan gyarawa baby kwanciyarta ta mike ta nufi toilet
Wanka ta soma yi kafin ta daura alwala ta fito ta shirya cikin duguwar riga da hijab mai tsayi ta hau kan dadduma, nafila tayi raka’a biyu bayan ta idar ta daga hannunta sama tana addua tana hawaye kan Allah ya za’ba mata abunda yafi alkairi dangane da zamanta da mijinta.
Al’kurani ta dauka ta fara karantawa tun daga fatiha har sai dai tayi izifi biyar tukkuna ta rufe al’kur’anin ta tada sallahar asubahi…….Tana idarwa baby zahra ta tashi ta soma kuka da neman nono,
Da sauri ta cire hijab din jikinta ta dauki yarinyar ta ciro nono tasa mata a baki.
Yarinyar na tsotsar nono ita kuma tana share hawaye daga haihuwar fari har gishiri ya salamce daga jikin kaza ashe dama duk k’aryace ba wani sonta da yake tunda gashi tun ba’aje ko ina ba yana wulakanta kan abinda bai taka kara ya karya ba, ta tabbata jiya yana sane ya’ki daukar wayarta kawai saboda ya wulakanta, kuma tasan domin ya kuntata mata ne yake waya da budurwarsa a gida insha Allah ba zata sake kiransa a waya ba domin tana masifar jin ciwon rashin amsa mata da yakeyi.
Gari ya dan soma yin haske ya shigo dakin ya sauya jallabiya yanzu ba’ka ce a jikinsa mai gajeran gannu da dogon wuya jallabiyar dai larabawa sunfi anfani da ita, hannunsa rike da cazbaha ya ‘karaso gabanta.
Kanta a ‘kasa tace”Ina kwana.”? Idanunsa kan baby zahra Ya amsa babu yabo babu fallasa.” Shuru tayi fuskarta a cukune.
Yace.”Ya jikin Mommy.”? Da sauki.” tafad’a a takaice. Yace.”Ki fito yau zamuyi zaman karatu.” Shuru tayi masa, ya kama hanya ya fice daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button