YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Palon ta fito cikin hijab hannunta rungume da baby ganin Hajja bata a palon sai ta nufi dakinta, tana kokarin fitowa suka gaisa ta mi’ka mata yarinyar tace”Yau zamu koma karatu Hajja ga ‘kawarki.”
Hajja tace”Dama yanzu nake shirin shiga ai nayi mata wanka.”
Wasila tayi murmushi tace” Ai kam da wuri ta tashi tayi ta tsotson nono ina shirin mata wanka Babanta yace zamu zauna karatu.” Hajja tace”To bari nayi mata wankan anan na shiryata.
Tace”Bari na dauko miki kayanta.”
Tana fitowa palo ta tarar dashi da Rashida sun soma karatu, ya dago kansa suka hada ido sai tayi saurin dauke kanta ta wuce dakinta. minti biyar ta fito rike da kayan a hannunta dakin hajjan ta nufa ta mika mata ta fito ta zauna gurin karatun.
A’lkur’ani ta bude dai-dai inda suke ta cigaba da sauraranshi har ya gama musu karatun yace su biya mishi yaji.
A nutse suka soma biya mishi aya goma yake musu da safe da dare shi kanshi yana mamaki da yanda Allah yayi musu kwakwalwar saurin daukar karatu sam basa bashi wuya gurin karatu nan da nan suke daukewa, mussaman Wasila.
Sauran littafan ya biya musu yana musu bayanin yanda zasu fahimta sosai, bayan sun kammala ne ya kalli Rashida a nutse yace.”Rashida ya karatunki na boko ina fatan komai yana tafiya dai-dai kina fahinta.”? Tace”Eh ina ganewa wallahi dan mun kusa jarrabawa tunda ina cikin wad’anda zasuyi jarabbawar fita.” Yace.”Alhamdullhi Ya kalli Wasila da hankalinta ke kan littafin zaduzjaujen Yace.”Kema ki shirya insha Allahu za’ayi yanza za’ayi ki shiga cikinsu kiyi jarrabawa tunda naga babu lefi kina ganewa i
dan Allah jarrabawar tayi kyau xanyi magana da abokina Prof ‘Dalhatu Nuhu dake jami’ar Bayaro a sama muku gurbin karatu a makarantar insha Allahu.” A hankali tace.”To mungode, mikewa yay ya nufi dakinsa, itama ta mike jikinta a sabule ta nufi nata dakin, ita kanta rashida jikinta yay sanyi ta lura kamar akwai matsala a tsakaninsu dan duk sanda suka zauna zaman karatun kafin su fara sai sunyi wasa da dariya a tsakaninsu, dan wataran ma idan sunayi ita har kunya suke bata, amma yanzu taga ita dashi sun bawa kansu tazara ko wanne fuskarsa a had’e.
Mikewa tayi tabi Wasilan dakinta…..Lokacin tayi wanka tana shiryawa rashida ta zauna gefan gado tana kallonta so take tayi mata magana amma kuma tana jin tsoro kar tayi mata masifa…..Wasila ta shirya cikin atamda java ja da baka d’inkin fetted gwon yay masifar fito mata da sharp dinta dan har sai da ta d’an saki zuf din rigar ta baya dake ta kwana biyu bata saka kayan ba, yanzu rigar ta matseta ire iren d’inkunanta ne na fitsara lokacin tana harkar siyasarta, Rashida tace”Anti Wasila dama wannan kayan suna nan.” Tace”Gasu kuwa kin gani.” Rashida tace”Yanzu sun matseki ba kamar da ba.” Tana fesa turare a jikinta tace”Eh na dan yi ‘kiba shiyasa.
Dankwalinta ta daura ta nannad’e gashinta dashi ya fito ta ciki ta danyi make up kadan a fuskarta tasa jan janbaki a le’bunanta, wani masifar kyau tayi tamkar ka sace ka gudu.” Rashida tace”Anti Wasila atamfar nan nayi miki kyau sosai.”
Tace.”Nima shiyasa nake sonta.”
Rashida tace”Anti Wasila dan Allah kada kice nasa miki ido wai me yake faruwa ne tsakaninki da maigidan naga tun bayan tafiyar Inna Hajara ke dashi kuka rage walwala magana ma da kyar kukewa junanku.
Wasila ta dan kalleta tana mamakin maganarta, ashe dai duk yanda take kokarin ‘boye al’amarin sai da aka gane, jikinta a sanyaye tace”Rashida abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, ke ‘kanwata ce kuma nasan kina da hankali kin kai munzali kuma kin san abinda ke faruwa, yanzu dan Allah kece ace ki haihu kisha wuya sannan ayi miki d’inki gurin be warke ba sannan mijinki yazo miki da bukatar yin sex dake shin zaki yarda ki amince dashi ya lalata miki aiki ko ba zaki yarda ba.”?
Rashida tayi shiru tana tunani tace”Gaskiya mutukar gurin be warke ba bazan yarda ba dan idan d’inkin ya lalace inaji ina gani za’a sake min wani kuma shima mijin nawa daga ranar ya daina ganin amfanina amma idan na tabbatar da gurin ya warke zan amince na biya masa bukatarsa tunda hakkinsa ne.”
Wasila ta sauke ajiyar zuciya tace”To abinda ke faruwa kenan a tsakaninmu lokacin Inna Hajara nan tana nuna kulawarta a kaina shine yake jin haushinta wai ita ke zugani, na nuna masa ba haka bane shine yake fushi dan da Inna Hajaran ma ta tafi baice komai ba ya nuna yaji dadin tafiyarta, Rashida ni ban hanashi hakkinsa ba da ya amince da sai na dinga biya mishi bukatarsa ta wata hanya har Allah yasa gurin ya warke amma sai ya nuna shi dole sai ya shiga gurin ni kuma na’ki amincewa saboda nasan halinsa, shine fa yake ta fushi na bashi hakuri yaki hakura, Ina ga ma neman aure yake dan kullum sai sunyi waya da budurwarsa.” Ta’karasa maganar muryarta na rawa tabbacin abin na mutukar damunta daurewa kawai take…….Rashida tace”To anti Wasila kema kina da gaskiya dan gaskiya kika sakar mishi jiki bayan kuma kin san da ciwo a gurin aiki ya ‘baci ke zai bari a ciki, amma ga shawara me zai hana ki koma asibitin su duba miki su tabbatar gurin yayi dai-dai idan hakane sai kawai ki shirya ki cigaba da kula da mijinki.”
Ajiyar zuciya ta sauke tace”Rashida tun Inna Hajara na nan da mukaje asibitin suka tabbatar aikin yay kyau dan gurin ya dawo normal kawai ni ina jin ciwo kadan kadan ne wallahi kuma ina jin tsoro kada wannan abun ya sanya wani abun ya faru sannan kuma kinga banyi wani gyaran jiki ba na fiso na gyara jikina sosai kafin sannan gurin ya sake yin ‘kwari yanda ake so.”
Rashida tace”Gaskiya wannan ba dubara bace anti Wasila to shi kuma sai yayi ta zama da lalura kawai dan biyan bukatarki, ai tunda an tabbatar miki da lafiyar gurin ki amince masa da bukatarsa.”
Shuru tayi tana tunani tace.”Shikkenan na dauki shawarark
i zan amince masa idan ya sake nema nima sam bana son irin wannan zaman da muke.” Rashida tace”Nima abin Bayayi min dadi gashi kuma naga kamar ya damu wallahi daurewa kawai yake.” Ta’be bakinta tayi tace”Ni idan ta nine magana ta wuce ko yanzu ya nema shikkenan idan kuma yayi zuciya shi ya jawo.” Rashida ta mike suka fita palo a tare
Shi kadai ne zaune a daning yana karyawa Hajja na zaune a kujera da baby zahra a hannunta tayi mata wanka tsaf ta shiryata cikin kayan sanyi kasancewar ranar an tashi da lillimi baby zahra sai kamshin turare masu dadi takeyi, sosai yarinyar take kara kyau da ki’ba saboda tana samun kulawa ta ko wane bangare.
Tun sanda suka fito daga dakin ya dora idanunsa kanta ya rasa nutsuwarsa, dan idonsa ya tsurata yana binta da wani mayataccen kallo tana tsaye tsakiyar palon suna magana da Hajja! Ya ‘kura bayanta ido da yake a d’an bud’e saboda ta saki zuf din rigar kadan dan har brexiyar ta ta fito daga ciki, ajiyar zuciya ya dinga saukewa gabanshi na wani irin fad’uwa ji yay yawun bakinsa ya tsinke! kwata kwata ya gaza dauke idonsa daga kanta idanunsa sunyi masifar galabaita gurin kallon d’uwawunka da suka fito dam! dam cikin rigar kamar zasuyi magana ga lafiyayyar fatarta dake she’ki da daukar ido lukwi lukwi da ita da wani irin kwantaccen gashi a kai.
Tsigar jikinsa ta dinga tashi sanyi ya soma ratsa jiki da ‘bargonsa…..Rashida tayi saurin daukar abinda zata dauka wanda zata karya dashi ta bar daining din dan ta lura hankalin Yayan nata nakan yayarta wanda ta fahimci kamar ma baya cikin hankalinsa dan har ta gama abinda za tayi a gurin be kalli inda take ba.



