YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Governor yayi murmushi yana fadin”Hakika wannan yarinya ‘kwalkwarki naja sosai wannan shawara taki itace dai-dai a halin yanzu duk abunda mukayi jama’a zasu gane mu da sauri shi kansa ma zai gane mu abinda zamuyi shine mu dauke hankalinmu daga kanshi ta bangaran auranshi da Wasila, mu cigaba da harkokin siyasarmu kamar yanda mukeyi……As yace.”To yanzu meye abinyi.”? Camas! tace”Ku bar komai a hannuna da sannu zan aiwatar mana da ‘Kudirinmu insha Allahu duk yanda zanyi zanyi in samu nasarar shiga gidan duk dai ya zuba matakan tsaro amma hakan bai zai hana na samu hanyar shiga ba, zan samu Wasila zamu tattauna kan maganar da muka yanke daku.”
As yace.”Ban ta’ba ganin d’an akuya ba kamar Ba Iya ka! ashe kwance kwance yayi mana, yasan wannan yarinya nada amfani a tafiyarmu sai da ya san hanyar da yabi dare da rana ya rabamu da ita, Zai gane shayi ruwa ne.”!!!!
To kamar yanda Dr Nasir ya fada hakane ya kasance da Wasila misalin karfe goma shabiyu na dare ta farka lokacin ruwan da aka daura mata ya kare, Ta farka da wata matsananciyar yunwa cikinta sai ‘kugi yake, hannunta ta dan daga kadan tana rintse ido sosai hannun yayi mata tsami! ta sanya daya hannun ta cire abin da akayi mata karin ruwan tana dan matsa gurin…..Tana zuro kafafunta da niyyar sauka daga bed din ya turo kofar dakin ya shigo…..Yana sanye da Pyjamas kirjinsa a bayyane kasancewar bai daure igiyoyin rigar ba….Da sassarfa ya karasa kusa da ita yana tambayar ta jikin nata….kasa kallonsa tayi ta rasa wane irin iskanci ne wannan haka kawai sai ya dinga zuwa inda take da kirji a bude shi gashi ‘kato, duk sanda idanunta suka sauka a kan faffadan kirjinsa takan ji wani iri a tare da ita, shiyasa ko da wasa bata son kallonsa cikin irin wannan shigar….Yana tsaye yaga ta mike tsaye jikinta da kwari bata tangadi da layi irin na dazu nan ya fahimci ta dan samu rangwame ya bita da kallo har ta shiga toilet……Minti biyar tayi a ciki ta fito,Bakinta ta wanke ta dan dauraye fuskarta babu abinda take muradi sai abinci ko wane iri ne….Ta zaune gefan bed, shi kuma ya fita, Bai jima ba ya shigo dakin hannunsa rike da plate mai murfi ya ajiye mata kasan kafet…A nutse yace.”Ga abinci nan dauki kici kafin kisha magani.” Ya dauka za tayi masa musu sai yaga ta sauko kasan kafet din da sauri ta bude plate din abincin, tana juyawa…..Pride rice wacce tayi kayan lambu da hanta a take taji yawun bakinta ya tsinke ta ciko cokali da sauri ta tura a bakinta….Fita yayi da niyar dauko mata magungunanta, Yana dawowa ya iske ta cinye abincin nan tas! ko ‘kwallon shinkafa ba ta bari ba, sosai ya shiga mamaki! ya dinga kallonta yana kallon plate din….Kunya ce ta kamata sai ta dinga dauke kanta tana zumbura baki…..Gyaran murya yayi yace.”Kar’bi magani kisha idan kuma abincin bai isheki ba akwai a kicin Okey.”!
Kamar ta’ki karbar maganin sai dai ta karba sai taga kuma kanta zata cuta ta mika hannu ta karba….Ya kama hanya ya fice daga dakin abinsa……Ajiye maganin tayi tana tunani, Ita abincin nan bai isheta ba gashi tana jin kunyar zuwa ta ‘karo….Mikewa tayi ta bude kofar dakin a hankali! Taga baya palon ta dauki plate din ta fita, da lalube ta iske kicin din, ta tsaya tana kare masa kallo, kicin sai kace d’aki anyi masa jere iri iri da na’urori har da Ac freezer irin na kwance guda uku shin kanshi Gas din dake kicin din bata ta’ba ganin irinshi ba, kicin din yayi masifar burgeta, ta dinga kalle kalle sai da ta gaji ta bude tukunyar dake kan gas din ta d’ebo abincin ta fito……Sun kusa buga karo dashi yayin da yake kokarin shigowa cikin palon ita kuma ta fito daga kicin din…Da sauri ta matsa gefe gabanta na faduwa! Ya kalli plate din hannunta yaga ta ciko da abinci , kamar yayi magana sai kuma yaja bakinsa ya kulle, ya nuna mata hanya da hannunsa, Simi-simi ta wuce kunyar duniya duk ta isheta karfa guy nan ya dauka ita mayunwaciya ce ko zulamammiya asali ma ita abinci bai dame ta ba takan iya yin ci biyu kacal a rana ko taci sau daya in dai za tayi ciye ciyen ta.
Koda ta sanya abincin a gabanta kasa ci tayi tunda tayi loma uku sai ta ajiye cokali ta zabga uban tagumi tunanin rayuwa ta shiga yi, tun da suka taso ita da ‘yar uwarta da mahaifiyarta suke shan wahala a duniya babu irin wuyar da mahaifinta bai sha kan asirinsa ya rufu har wanki da goga yayi kana kuma yayi faskaran ice ya sai da kayan miya duk wata sana’a da Yahuza mai rasuwa yasan zaiyi yanayi duk dan asirinsu ya lullu’bu! Sai dai kash! Allahn da ya hallici Uwani ya hallice ta ne mara godiyar Allah duk irin dauki ba dadin da Babansu yake yi a kansu bata gani, tun suna yara kananu take so ta koya musu bin maza tallah babu irin wanda bata dorawa Rashida, saboda itace mai dauka ita kuwa duk ranar data dora mata tallah to sai ta zubar da kayan a kwata tana sane dan haka sai ta daina dora mata, lokatan baya samari yan banabakwai har sun soma latse Rashida tun bata kai shekarun hakaba, wannan dalilin ne ya sanya bacin rai ya kwantar da Yahuza ashe kwanciya yayi wacce ba zai tashi ba yazo yayi mutuwa fuju’an!! Sai suka sake shiga tsananin takura da damuwa da rashi da kuma kangi na talauci!
Uwani itama marainiya ce ita sam bata ma taso tare da iyayenta a hannun Kanin babanta ta rayu rayuwar da tayi a gidan Kawunta mara dadi ce tasha wuya sosai matansa suka mayar da ita yar aiki komai itake musu ga yayansu baza su sanya su aiki ba sai ita tanaji tana gani zasu tura yayansu makaranta amma ita tana zaune dan da Kawun nata yayi niyar sanya ta a makaranta sai su ka nuna rashin amincewarsu saboda suna ganin duk sanda ta fara zuwa makaranta to aikin gida zai dawo hannunsu, shi kuwa dama mutum ne da baya kaunar bacin ran matansa da yayansa, sai ya kyale Uwani ta dawwama cikin bauta babu a rabi babu boko…
Gurin yawon cefane suka hadu da Yahuza a lokacin yana siyar da kayan gwari! Aikuwa tsabar kyawunsa ya sanya Uwani makancewa a kansa, duk da a lokacin manya mutane masu hannu da shuni sun fito suna sonta, ciki harda Ubangidan Kawun nata, tace Ita Yahuza take so, Kawu yayi yayi da ita ta amince da Ubangidansa ta’ki fafur! Gefe guda Matansa na kara ingita kar ta auri Alhaji Bala, domin suna ganin idan ta aureshi to ta wuce takaici sai suke bakin cikin hutun da zata samu suka dinga zugata da fadin”Idan ta aureshi matarsa sai ta kasheta dan Hajiya Larai bata zama da kishiya tasha haukawa kishiyoyinta, da jin wannan magana tasu sai Uwani ta sake rikicewa ta tsorata ta tuburwa kawu dole ta sanya yace da ita maza maza ta sanya Shi Yahuzan ya turo magabantanshi……Yahuza ya dauko Malam mai allo da Kawunsa suka zo har gurin Kawun Uwani aka tsaida maganar daurin aure……….. Ranar da aka daura auran Kawun ya bata sadakinta a hannunta yace.”Uwani tunda ke baki dauke ni a matsayin uba ba kina bujerewa umarnina to shikkenan kije na yafe ki daga zuria ta tunda Yahuza kika zaba kije babu ni babu ke kar in sake in sake ganin kafafunki a gidana duk sanda kika zo min gida to sai nayi miki korar kare kije yan uwan Yahuza su zama yan uwanki.” Uwani ta dinga kuka tana bashi hakuri, fatafata! yayi mata ya kore ta……. Wannan shine dalilin da ya sanya Uwani take rayuwarta ita kadai daga ita sai ‘Yayanta, kuma tun sanda Kawunta ya koreta bata sake taka kofar gidansa ba kana kuma bata barin su Wasila suje gidan.
Abinda ya janyo musu rashin jituwa da Kawu mai allo lokacin da Yahuza ya mutu da yazo ya dauke mata ‘yayanta tayi magana ya farfada mata magana mai zafi! ashe dama tun lokacin daurin auranta da Yahuza Kawunta ya dinga fadawa Malam din bata da hali bata jin magana gararrariya ce bata da biyayya dalili kenan da ya sanya yayi mata aure, to tun daga lokacin Kawu Malam yake mata kallon mara tarbiya gaba mai muni ta shiga tsakaninsu A cewarsa ai tunda ba tayi wa Kawunta biyayya ba to waye kuma za tayi wa….Da fadin wannan magana tasa ita kuma sai ta kudiri aniyar cewar in dai itace mahaifiyarsu Wasila to itama ta dauki alkwarin ba zasu ta’bayi masa biyayya ba zai ga rashin tarbiyarta a zahiri.