YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Kira ne ya shigo wayarshi dake hannun Hadi yana daga kwance ya mika hannunsa ya ‘karba, Hajiya babbah ce! mikewa yayi zauna ya kara wayar a kunnanshi ya risinar da murya yana gaisheta ta amsa da sakakkiyar murya tana tambayarsa iyali! sai yaji wani iri jin abinda tace wai ya iyali? ya waske da fad’in”Lafiyarsu lau hajiya ya gida kwana biyu uzirrika sun sha kaina ban samu na shigo mun gaisa ba.” Tace.”Aikam dai jama’a nata cigiyar ango ranar da nayi yini na da jama’ata kowa haka ya hakura, duk sunayi maka Allah ya sanya alkairi.” Ya amsa da “Ameen Hajiyata mybe gobe ki ganni insha Allahu.” Tace.”To to ai sai mu d’aga tamu tafiyar tunda zaka zo da mun shirya zuwa gidan naka tare da matan Kawun ka Almu.” Yace.”To babu laifu Hajiya sai kunzo din zan tsaya jiranku duk da ina da babban uzirin da zai fitar dani goben amma babu matsala naji dadin zuwanku.” Tace.”Ai ba za’ayi haka ba kuma kada mu katse maka hanzari.” Yace.”Ko wane irin hanzari gareni idan ina neman albarka dole in tsaya in saurari zuwanku.” Taji dadin maganarshi sosai tace”To Allah yayi maka albarka Ahamdu kaima Allah ya baka ‘yaya masu yi maka biyayya.” Ya amsa da “ameen ya rabbi nagode. Sallama sukayi ya mikawa Garba wayar kana ya mike da towel din a hannunshi yana karkade gwiwarshi da ta dan ‘baci! Yace.” Garba zan shiga in kwanta in huta yau babu in da zani Khalifa nan zuwa tare da iyalinshi idan ya kira waya kace na kwanta nasan sai bayan axuhur za su shigo lokacin na matse insha Allah.” Garba yace.”Okey sir zan fad’a mishi insha Allahu.” Ya kama hanyar shiga cikin gidan…….Suka ce a tashi lafiya Yallabai.” Ya amsa da “ameen.” Yana daga musu hannu…..Dai-dai lokacin da ta fito daga dakin da take a dai-dai lokacin ya shigo palon……Sai da ta kusa faduwa saboda razana! masifaffiyar yunwa ce ta fito da ita wacce take baraxanar cinye mata ‘yan hanji taji zata mutu ta futu afujajan domin samawa kanta abinci….Shi kuma wannan motsa jikin da yayi cikinsa kamar anyi masa yasa haka yake ji sai kokawa ‘yayan hancinsa sukeyi…Kalon kallo aka shigayi tsakaninta dashi, fuskarsa akwai alamun sassauci ba kamar ko da yaushe ba, Juya tayi ta koma dakin fuskarta babu walwala har yanzu haushinsa takeji……Girgiza kai yayi ya nufi daining din, Rabe ya shirya break fast kamar yanda ya saba, a nutse ya had’a komai da kanshi ya zauna yana karyawa hankali a kwance.
Gefan bed ta zauna ta zuba tagumi! abin duniya yayi mata yawai wai shin ya za tayi da wannan kad’dararran auran da aka la’ka ba mata, komai na rayuwarta ya tsaya! ta taso da kwajinta da bajinta an tsugunar da ita guri guda, wai me take jira ne? da ba zata nemawa kanta mafita ba, Wata zuciyar tace mata “Ta ina zaki nemawa kanki mafita cikin wannan gidan dake tsautsare da matakan tsaro? Shawarar Camas! itace abun dubawa dole duk haushinsa da takeji ta saki jiki dashi ta samu ya bata Pose dinta domin tsira da muhiman abubuwanta dake ciki, sashe na zuciyar ta yace mata ” Kinga idan yaga kin saki jiki a gidan kin karbi auran hannu bibbiyu to zai dauka kin hakura xaki zauna zaman auran dashi kuma zai sassauta matakan tsaro a kanki daga nan sai ki samu damar guduwa abinki ki kai su ‘kara kotu daga shi har malam mai allon.! Wannan shawara ta yanke a zuciyarta.
Yana gama break fast dinshi ya nufi bedroom dinshi wanka yayi ya fito ya shiya still cikin ‘kananun kayan dai, farare tas riga t_shart da wando 3Qutar mai aljuhunai gaba da baya, gaban rigar hoton zuciya ne an rubuta heart da bakin rubutu, sosai yayi kyau ya taje saisayayyiyar sumarshi mai tafe da sajensa cikin tsari! ya fesa turarenshi mai dadin kamshi, har yayi nufin kwanciya sai idanunsa suka sauka kan ledojin da ya shigo dasu jiya da daddare , ‘Kananun kaya ne ya shigo mata dasu yasan za tayi amfani dasu tilas watarana, daukar ledojin yayi ya bude dakin……Idanunsa suka sauka a kanta zaune kan kujerar daining din da cup din tea a hannunta tana kurba tana hadawa da plantain, Ya karasa kusa da ita saitin kafafunta ya dure ledojin ”Gashinan nasan zasuyi miki amfani watarana.” Kamar yanda bai kalleta ba sanda yake maganar haka itama ko inuwarsa bata kalla, Har yayi nufin barin gurin sai kuma ya tsaya ya d’an kalleta da gefan ido, Yarinyar nada wani irin madarar kyau! gani yake har yanzu bai gama saninta ba kullum sai ya sake ganin abinda ke burgeshi a jikinta…..”amm!!! Magana yayi niyyar yi sai kuma ya dagata, Ta kalleshi sa kwala kwalan idanunta da suke furgita ‘yan maza! ta wani risinar da kwayar idon cikin tashi tana masa wani malalacin duba, ta lura da akwai magana a bakinsa sai kawai ta dauke kanta tana cigaba da kurbar tea din a yangace sai kace wata d’iyar sarakai!! Hakan da tayi masa yasa yaji wata irin shakkar ta abinda bai ta’ba faruwa dashi ba kenan ace yana jin shakkun yiwa wata d’iya mace magana, Dauriya ya aro a take yace.”Idan anjima muna da baki! nasan dai zaki shaida babban abokin nan nawa Khalifa, shine zai zo tare da Iyalinshi.”! Ya kare maganar idanunsa tsaye a kanta.
Ta’be bakinta tayi ba tare da tace masa komai ba…..Yasan taji abinda yace, sai bai tsaya sauraran iskancin da take masa ba ya kama hanya ya shige bedroom dinshi ya kule yayi kwanciyarsa.
Tana kammala breakfast din ta dauki ledojin da ya ajiye mata ta shiga dasu dakinta.
Zazzagesu tayi kan bed tana duddubawa, had’addun kananun kaya ne da wasu lafiyayyun kayan bacci amma kuma tsaraicinsu ya fito fili duk da ita kadai ke kwana ba tajin zata iya amfani dasu a jikinta saboda tsaro….Za dai tayi amfani da kananun kayan domin sun burgeta, dogwayen wanduna ne masu mannewa suma rigunan irin masu kama jikin nan ne da budaddan wuya, wasu ma babu hannu sai dai wasu ‘yan igiyoyi sune ma dadin hannun rigar, duk wannan tana ganin zata iya saka su ai ba wani abu bane domin ita dai a rayuwarta tana masifar son kananun kaya tun ba da tasan suna mata kyau ba……Wanka ta shiga tayi ta fito daure da towel tsaye tayi gaban mirror tana gyara gashinta ta daureshi da katon ribbon ta tattaro gashin ta gaba ta tufke yayi jela ta sake shi yana reto a gadon bayanta, turaran jiki ta shafe a jikinta ta dan shafa mai sama-sama ba tare da tasa pant ko breziya ba ta dauko wasu shegun kaya cikin kayan dazu ta tusa a jikinta, Wow! Ita kanta sai da tayi mamakin yanda kayan suka kar’be ta sai wani juya takeyi sassan jikinta na motsawa ko yaya tayi motsi nonowanta sai sun motsa, ga d’uwawukanta sun wani fito radau sun kame guri guda rigar ta manne a jikinta harta da nipples dinta sai ta nuna, kayan sun kasance bakake ne masu taushin gaske, Duk da cewar Wasila ba fara’a bace kayan basu sanya ta muni ba sai ma wani bala’in kyau da sukayi mata,Sosai duk wanda ya ganta cikin wannan dressing din yayi sha’awar ta zama tamkar wata fure dan kyau, ta kama hanya a hakan ta fita palo tayi zamanta kan kujera tana kallo hankalinta kwance.
Kamar yanda na fad’a a pege din da ya gabata cewar barin najasa ko wace iri ce itake kawo shafar jinnu Haka ne ‘Yar uwa idan kina cikin al’ada ma’ana kina jinin haila duk rintsi kar ki kwanta sai kin daura alwala wannan alwalar da kikayi itace garkuwa a gareki…..Idan kun gama mu’amular aure da mijinki kiyi wankan tsarki idan akwai uziri ki daura alwala za ta zame miki garkuwa amma dai anfi so a wanke wannan janabar, Matsalar dake sanya kenan har Namij dare (bakin aljani!) ya aureki kenan kin bar janaba a jikinki yazo ya kwanta dake shima yana saduwa dake ba tare da kin sani ba, wannan ba’kin aljanin yana wa mata da yawa illah kuma da yawa mune muke jawo shi jikinmu saboda sakaci da rashin kula da tsare tsaraicinmu da kula da ibadah!!! Idan kina kaf kaf da jikinki kina kuma hirji da azkar to komai najin bakin aljani dole ya gusa daga inda kike….Allah ya kare mu da kariyarsa????????