NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Wasila dake can aikin Ya’bawa Fastocin Ahamad kwata da ‘bakin mai!! ta hango abunda ke faruwa Abokanan tafiyar ta sun suna shigewa mota saboda ‘Kumd’um! dan daban nan ya soma fitarwa da wasu jini sai suka razana suka soma shiga mota…..Da gudu tazo shiga mota ‘Kumdum’ ya fuzgo hijab din jikinta ta dawo baya ‘Kara ta ‘kwallara! ganin yana ‘kokarin kai mata sara da ‘katuwar addar dake hannunsa ta rintse ido gabanta na buguwa fat! fat! fat! shikkenan ta mutu!!! Shiru taji gurin yayi ta bude idonta a hankali tana bin mutanan gurin da kallo……Shi ta gani tsaye a gabanta hannuwansa cikin aljihu yana mata wani mummunan kallo still ga ‘Kumdum rike da shar’bebiyar addarsa a hannu.!!

Kallon juna suke ita dashi! tsaf! ya gane yarinyar nan ce da shigo masa gida jiya tabbas ga maganar Garba ta fito ashe da wata manufa ta ziyarceshi ya gode Allah da bai sanya masa kwad’ayin mata ba da badan hakaba da tuni bukatarsu ta biya a kansa.

Ya kalli ‘Kumdum dake zare ido yana ciccije baki!!! Yace.”Rabu da ita kar kayi mata rauni ko ka zubar mata da jini! taci albarkacin sunan mace da ta amsa mace duk inda akasanta mai daraja ce da kame kai Astagafurullah wannan yarinyar ta ‘batawa mata sunansu idan ka daketa ko ka zubar mata da jini duk a banza tunda na lura da akwai bakin iyaye a kanta so ka kyaleta taji da abunda ke damunta zamu dai cigaba da yi mata addua idan mai shiryuwa ce kuma insha Allahu muka samu mulki a hannunmu duk zamu tattara ire irensu mu samu mu had’asu da mazaje dai-dai dasu muyi musu aure babu shakka za’a samu sassaucin wasu abubuwan.”
‘Kumdum! ya saki hijab d’in Wasila dake damke! a hannunsa yana fad’in”Eh! Yanda kace haka zakayi mahadi mai dogon xamani insha Allahu kano ta kace ko ana ha! maza ha! mata sai ka tuge! wancan wawan! da bai iya komai ba sai hauka.”!!!!!! Jama’ar dake gurin suka sa ihu! da fadin””Maganarka haka take ‘Kumdum Kano ta d’an Musa ce ko ana so ko ba’a so sai yayi.”””!!! Wannan damar da Wasila ta samu ya sanya tayi wuf! ta bar gurin can inda motocinsu suke ta nufa ta tarar duk an ragargaza gilashin motocin Camas! ta bude motar ta shiga da sauri wani matashi ya daki motar da kafarsa yana musu ihu!!! Sai da suka yi nisa da gurin sai suka saki wa’kar gwamnan dake ci a yanzu Mai taken Munyi muku fintinkau!!!!!! Kano sai kallo daga nesa mai raba gardama yazo Enginer Lawan Rabo, duk wanda zai ja dakai shine wawa!!!!! Wasila ta fito da jikinta ta saman mota tana watsawa Ahamad da’kuwa! da dukanin hannunta tana sake fad’id”
Wanda zai ja da Engener Lawan Rabo shine wawa!! Ahamad yana kallon sanda take watsa masa hannayenta da sunan da’kuwa! {Zagi!} ransa ya ‘baci sosai lallai yarinyar nan bata da kirki ya lura yar adawa ce mutuka dole ne ya sanya ayi masa bunkice akanta domin abun nata ya wuce gona da iri.

Mota ya shiga tare da jama’arshi jama’ar gurin sai daga masa hannu suke suna masa fatan alkairi yana amsa musu cikin sakin fuska amma in zaka tona zuciyarsa a lokacin zaka tarar tayi ba’kikkirin sakamakon zagin da Wasila tayi masa wanda ba kowa ne zai fahinta ba sai shi wanda akayi dominsa.

Muje Zuwa
BINTA UMAR ABBALE
[7/13, 4:15 PM] Bintu: ‘YAR BANGAR SIYASA!!
???? romantic love story????
NA:
BINTA UMAR ABBALE ????
????Manazarta Writes asso
‘Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi

 *NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300   Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176  sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko Orange_

*Free Pege7*
Wani irin gudu motocinsu sukeyi kan kwalta, suna sakin ihu!Wa'kar injiniya Lawan Rabo ta tashi a motocinsu jama'ar gari suma suka dinga ihu! da fad'in "Ba mayi!!! insha Allahu kano ta d'an Musa ce! su dinga jifan motocinsu da duwatsu suna ihu!!! Su Wasila da kyar suka sha amma dai hakan yayi musu dadi tunda dai sun rusa shirin *Ahamadu* sun hanashi aiwatar da nufinsa wannan ya nuna musu suke da nasara a kanshi.

Khalifa ya kalli fuskarshi ya ganta a murtuke! yasan ranshi a 'bace yake gyaran murya yayi yace." Wai wannan cin maganin da kakeyi na menene dole fa ka fuskanci irin wannan 'kalubalan al'amarin siyasa sai addua komai mutuncinka sai ya zube kauda kanka kawai zakayi.

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya d'an gyara zamanshi yace."Khalifa sam abunda mutanan suka turo ayi mun bai dameni ba saboda nasan sunyi abunda yafi wannan......Shin wai baka ganin zagin da yarinyar tayi min ne."!?
Khalifa ya dan gyara zaman hularshi yana sakin murmushi a hankali yace."Duk akan idona al'amarin ya faru sosai nayi mamakin tsaurin idonta na fahimci kuma harkar takeyi da gaske so kar ka damu da wannan Siyasa ce a gabanka ma sai a zage ka a jefe ka kai dai tunda kace za kayi to sai ka daura d'amara!

"No!!! Karya ne wallahi." Yafada a zafafe! ya kalli Khalifan da jajayen idanunsa da suka rine da 'bacin rai! yace."Khalifa Siyasa ba hauka bace kamar ni wannan yarinyar gantafalfala ta zageni! kai kanka kasan halina bana ya fiya mutukar mutum ya shiga gonata ban hanata tayi min komai ba na yarda siyasar 'kasa ce amma banda zagi sai na ci mutuncinta wallahi."!!! 

"Clm dwon mana ka nutsu fa ba'a saurin yankw hukunci da gaggawa ka kyaleta kawai idan ta sake sai ka dauki mataki a kanta amma yanzu kana yi mata wani abu zasu 'kulla maka wani sharrin kasan halin su dai."

Ya rintse ido yana sake hango lokacin da take watsa masa hannuwanta da sunan zagi! Ya bude ido yana sauke numfashi idan fa bai rama abunda yarinyar tayi masa zuciyarsa zata iya tarwatsewa mutum ne shi mai bala'in kishin kansa da 'kaunar iyayensa ya tsani na 'kasa dashi ya raina shi ko ya zageshi baya daukar irin wannan rainin  shiyasa yanzu hankalinsa ya tashi mutuka duba da yanda yarinya 'kankanuwa wacce bata wuce 'yar cikinsa ba ta zageshi dole yayi bunkice a kanta.

Khalifa ya dinga tausarsa da kalamai masu sanyi yana nuna masa haka lamarin siyasa yake dole fa sai ya kauda kansa ga dukanin abunda 'yan adawa zasuyi masa idan ba hakaba kuwa zai 'bata rawarsa da tsalle kawai ya share yarinyar ya bari kawai duk sanda ta sake to suma baza su kyale ba.

Garba Da Hadi suka ce "Sir da ka bari wannan 'dan daban ya koya mata hankali wallahi yarinyar bata da mutunci ko kadan muma munga abunda tayi maka wallahi munyi rantsuwar duk sanda ta sake maimaita abunda tayi sai munyi mata tsirara sai mun tujara ta a gari karyar iskanci takeyi.

Ajiyar zuciya ya sauke ya dan ji sanyi cikin ranshi Yace." Na rabu da ita saboda maganganunku ammafa ku sani duk sanda ta sake kwatanta zagina wallahi ranar sai ta raina kanta sai tayi nadamar zuwanta duniya babu ruwana."

Khalifa yace."Yawwa mai girma Governor haka ake son shugaba da daukar shawara insha Allahu kai ke da nasara a kansu" Hannu ya bashi suka rike suna sakin dariya Ahamadu yace." *CPC."* gabad'anyansu suka amsa da *"Sa'a!* Ya sake fadin." *CPC."* Suka amsa da *"Sa'a."!* Yace." Mulki na Allah ne."! suka amsa da fad'in "Insha Allahu kai Allah zai bawa." Ya amsa da "Allah ya bamu Sa'a." Suma suka amsa da "ameen." 


Wasu Wasila kuwa kai tsaye gidan Governor suka nufa domin su alhaji Ma'aruf nacan gidan suna meeting sai sukace su samesu a can, suka samu wata katuwar rumfa suka zazzauna kamar wasu almajirai   suna jiran fitowarsu.....Can sai gasu sun fito daga wani dakin wanda yake nuna alamun dakin taro ne sun kai su goma wannan yana wane wannan sun sha lafiyayyun shaddodi sai motsi takeyi tana she'ki masu Cot a cikinsu kad'an ne......Kai tsaye rumfar dasu Wasilar suke suka nufa ta ganinsu sun doso gurinsu sai ta mike da saurin gaske ganin harda Governor  ya sanya ta fara masa kirari da bambad'anci! dama Wasila akwai shegen za'kin murya tsiya Governor tun kafin su karaso yake murmushi babu shakka wannan yarinyar za'aje da ita irin wannan washi haka!!!! Gabadayansu suka mike tsaye ganin sun iso gurin Lauje dake jin haushin abunda Wasila takeyi ya buga mata tsawa da fad'in"Ai sai ki saurara haka domin mai girma governor ya iso ki bamu damar magana." Wasila tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.

Gaisuwa suka mike garesu suka amsa sosai Alhaji Ma'aruf ya kalli Lauje yace."Kaine wakilin tafiyar ya akayi alamu na nuna mana cewa akwai nasara a tafiyar." Kafin Lauje yace komai Wasila tayi karaf! tace"Alhamdullihi muke da nasara insha Allah domin  tun zuwanmu gurin muka watsa shirinsu muka tashi hankalinsa dana jama'arsa ni da kaina na dinga bin pastes dinsa da suke mannawa ina yagewa ina watsa masa ruwan kwata da bakin mai! da 'kyar! nasha a hannun wani d'an daba."!

Governor Ya kallesu yana fad'in"Da gaske maganar haka take."? Duk suka amsa da "Hakane ranka ya dad'e."! Lauje yaji tamkar yaje ya sha'ke wuyan Wasila shin wai me take nufi ne? yarinyar fa ta za'ke da yawa anya ba sai ya taka mata burki ba kuwa."

Governor Ya kalli Wasila yana murmushi Yace."Dama tun kafin na ganki na samu labarinki gurinsu Alhaji Ma'aruf gaskiya ne *'Yar gaske!* kin cancanci ayi miki komai zamu zauna dake insha Allahu ki fada mun dukanin bukatunki." Wasila aka saki murmushi ana gyara tsayuwa farin ciki duk ya isheta tace"Godiya nake mahadi mai dogon zamani governor da ba ta'bayin irinshi ba ba za'ayi ba insha Allah." tana gama maganarta Ta koma ta zauna inda take kana ganinta zaka gane tana cikin farin ciki babu shakka bukatarta ta kusa biya sun kusa yin hannun riga da talauci.

Alhaji Tasi'u ya kalli Lauje dake faman cin kunu babu shakka katsalandan din da Wasila ke masa akan harkarsa ya isa har yaushe ta shigo harkar da zata dinga za'kewa da za'kalewa kan komai kafin zuwanta shine yake jagoranta al'amura da suka shafi harkar jagaliya amma ya lura yarinyar idanunta kar suke zata iya komai bayan haka kuma macace dole tafi shi samu power a kanshi

Yace."Duk wasu bayanai munji su daga bakin *'Yar gaske!* kuma kun tabbatar da maganarta babu shakka munji dadin kasancewarta a wannan tafiya tamu, domin ta nuna mana ita jaruma ce kuma mai alkawari zata iya fansar da ranta a kan wannan harkar Kai Lauje daga yau Wasila *'Yar gaske*  itace shugaba a wannan tafiya taku abunda tace muku shi  zakuyi kai kuma in yaso sai ka zama mai take mata baya.

Lauje wani irin gumi! ya shiga yanko masa kai!!! 'Karya ma kenan! wannan afiruwar yarinyar itace za'ace zata jagorance shi aikuwa da sake!!! wallahi ba zai yarda ba. Cikin ranshi yake wannan zantukan amma a fili sai yace."Gaskiya ne Yallabai dukaninmu mun yaba bajintar yarinyar dan haka zamu bata hadin kai dari bisa dari mu dai fatanmu mulki ya cigaba da dawwama a hannunmu."

Governor Ya kalli Alhaji Ma'aruf yace."Ayiwa *'Yar gaske* kyauta ta mussaman Kafin mu zauna da ita.....Lauje da sauran yara suma ayi musu kyauta dai-dai gwargwado ai sun faranta min rai mutuka."

Aikuwa Alhaji Ma'aruf ya d'auko daurarrun kudi 'yan dubu dubu sabbi fil fil ya mikawa Wasila dauri hud'u....Kana ya mikawa su Lauje dauri hud'u kwatankwacin na Wasilan Ita kuma Camas aka bata dauri d'aya.....Wannan al'amari yayi masifar 'batawa su Lauje rai!! lokaci guda sukaji sunyi masifar tsanar Wasila daga zuwanta zata zo ta kar'be musu fada lallai da sake sai sun dauki 'kwakkwaran mataki a kanta.

Wannan karon da wuri suka koma gida wajejan karfe biyar da rabi tunda suka doso layin Wasila ke sakin murmushi ta hango gidansu da 'kofa lafiyayya sannan  an d'an kwaskware wasu guraran da suka ruguje hakan yayi mata dadi sosai babu abunda ta tsana irin taga ana hango mahaifiyarta da kanwarta a waje.....Gidan sai 'kamshi yakeyi Uwani an dage ana ta soya miyar dage dage Rashida kuma na gefe tana yanka salak gefe guda kifi ne manya manya (sukunbiya) an soya cikin kwalanda za'a sa a miya....Uwani ta amsa sallamarsu tana washe baki Rashida ta gyara tabarmar da take zaune tana fadin "Aunty Wasila yau da wuri kuka dawo Allah yasa dai an samo wasu kudin.....Wasila ta cire hijab din jikinta ta ta shiga zazzage  kudin da suke cikin jakarta......Uwani ta razana! ganin uban kudi gaban Wasila sun tassama dubu dari biyar! Sai kawai ta dora hannunta a saman hancinta ta dinga rangwada bud'a yi takeyi kamar zata tsine hancinta. Sai da tayi mai isarta sannan ta iso inda suke zaune Rashida sai faman irga kudin take tana ihu!!

" Kai jama'a! ashe dai zanga wannan rana ni Uwani, ashe idona zai ta'ba ganin irin wadannan uban kudade masu yawa lallai wannan sana'a tafi irin wacce nakw cewa kiyi 'yata Wasila ina alfaharin haifarki Allah yayi miki albarka Wasila." Uwani ta gigice sai sambatu takeyi Camas da Rashida sai dariya suke mata....Wasila kam mikewa tayi jikinta duk ya mutu duk sanda ta tuni artabunsu da *'Kumdum!* sai gabanta ya yanke ya fad'i shikkenan fa idan da da tsautsayi da karar kwana da tuni ta zama tarihi domin ta lura babu imani a cikin zuciyar dan daban ta wani gefan kuma guy nan ya  taimake ta dan sai yanzu take nadamar zagin da tayi masa kuma ta lura ya gani ya kuma ji rashin dad'i, sosai abun yake dan ta'ba zuciyarta babban mutum ne da shekarunsa suka wuce tayi masa haka domin zuwanta gidanshi na farko bata tantance kamaninsa da shekarunsa ba sai ganin da tayi masa a dazu.....Ganin zuciyarta na damunta ya sanya ta tattara ta watsar da al'amarin babu wani abunda zai faru dan ta zageshi ai Siyasar 'kasa ce kowa yana da 'yancin yin abunda yake so ga wanda baya so....Wanka tayi ta fito ta tarar Camas ta tafi gida ta kalli Rashida dake zuba musu abinci tace"Idan anjima zamuje Sto muyi siyayya dukanin abunda bamu dashi walau naci dana sha da daurawa." Rashida tace"Shikkenan bari nima nayi wankan sai muci abinci mu tafi."

Uwani kam sai faman juya miya takeyi tana murmushi Ah!! Allah maiyin yanda akeso dare daya Allah kanyi bature Arziki ya sakko musu lallai babu abunda yafi haihuwa rana a duniya shiyasa masu karin magana ke cewa ko kana gudu haifi ka jefar ita dai gashi haihuwa tayi mata rana.





_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/13, 10:52 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
   ???? romantic love story????
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE ????*
*????Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_

NA KUDI NE…….!
Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za’a tura kudin.0542382124…….Binta Umar gtbank….Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din….07084653262_08089965176 sai na fad’i yanda za’a biya kud’in…..Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars…….90899076_88137740 katin airtal ko orange

Free Pege 8
Suna idar da sallahr magariba suka fito har Uwani domin tace itama zata bisu kasuwar suka sanyawa kofar gidan katon kwado kana suka fito titi domin samun abun hawa, suna tsayawa wani mai d’an sahu ya tsaya gabansu Wasila tace” Al’Ikilas zaka kaimu.” Yace.”An gama hajiya nawa zaku bayar.”? A ya tsine tace”Muje dan Allah bana son harkar fatara ko nawa ne kudinka zan baka.”
Me dan sahu yace.”A’a hajiya daga magana karfa ki zageni dan wallahi kika zageni ba yarda zanyi ba.” Rashida tace”Kai dan Allah muje kana jan duguwar magana ai laifinka ne meye na tambayar nawa zamu bayar mu ba mutsiyata bane.” Yace.”Bana son in dauke ku ne bamu daddale daku ba sai kunzo sauka ku kawo min kauli da ba’adi shiyasa nake so naji nawa ne kudina.” Wasila taja tsaki! tana kokarin shiga babur dole ne ta siyi sutturu masu tsada saboda ta lura suma ‘yan a dai-da ta basu da kirki daga sunga mace da kod’addiyar atamfa sai su hau wulakanci in kuwa suka ga mace da dankareran lesi da gwala gwalai har rubibin daukarta sukeyi saboda sun san ko nawa sukace ta basu zata basu.

Wasila har waya take so ta sauya sai dai kuma abun yayi yawa dole gobe ma su sake fita dan yau kayan kwalliya zasu siyo da atampopi da mayafai da takalma, har bakin super Sto din ya ajiyasu ta dauko dubu daya dal ta mika masa baiyi tsammanin haka daga gareta ba ya dauka zaiga ta fito da dukukkunanniyar dari biyu canji yake kokarin dauko mata tace”Rike na barka maka.” Ya sako baki yana kallonsu sun juya suna tafiya, kai! ammafa yayi mamakin lamarin nan ashe arziki ne yake binsa yana basarwa duka kudinsa dari uku ne gashi ya tashi da dari bakwai sun isheshi karin kummalo da safe dan haka sai kawai ya nufi gida ya tashi daga aiki sai kuma gobe.

Su Wasila kuwa zagaye Store din suke suna so suga iyakarsa sun kasa babban store ne da sai wane da wane ke zuwa gurin duk abunda ke cikin gurin ba na yarwa komai kudi ne Wasila suka dauki atampopi kusan kala bakwai suka d’ibi lesuka da mayafai sannan suka nufi gurin kayan make up nan ma ta dinga hada kayan kwalliya so take ta dawo babbar mace ta dinga cin kwalliya dama can ita bata yarda da karamar shiga ba, Can bagaran turirrika ta nufa su Uwani da Rashida suka tsaya gurin gwala-gwala sai ‘kyauyanci sukeyi……….Yana kai hannunsa kan wani kwallin turare itama ta kai nata hannun ya sauka akan nashi.

Da sauri ta dauke hannunta tana kallon zatinsa gaggausa mutum ta gani tsaye a kanta yayi mata rumfa kasancewar ta mace mara tsayi sosai…..Sai ta daga kanta tana kallon fuskarta a lokaci guda taji wani irin miyau! ya tsinke mata a baki ganin wanda yake tsaye kusa da ita. Ahamdu Da sauri tayi ‘kasa da kanta tana adduar Allah yasa bai gane ta….’Kokarin wucewa takeyi taji yo muryarshi na fad’in”Zo ki dauki turaranki na samu wani.” Gaba tayi ba tare da ta amsa masa ba, suka hadu da Garba wanda yake kokarin isa inda ubangidansa ke tsaye…..Sarai! Garba ya ganeta sosai dan har waiwayenta yakeyi Ahamdu yace.”Kai! kula dallah! kallon me kakeyi ne.”

Da sauri yacs.”Sir baka gane waccan yarinyar ba.”? Tsaki yaja yana d’an ya tsine fuska yace.”Meye ya dame ni da ita da zan tsaya tantance wacece.”? Garba yace.”Sorry sir yarinyar nan ce fa ta d’azu.” Ya zare gilashin dake fuskarshi yana kallon Garba da mamaki yace.”Da gaske.”? Garba yace.”Wallahi itace sir wai baka gane yanayinta bane ai naga a furgice ta bar gurin nan.”

Murmushi yayi kawai ya mai da gilashinsa, ashe ita ta ganeshi shiyasa tayi gaggawar barin gurin yanzu ya gane Jagaliyarta ta ‘karya ce tunda bata iya tsayuwa a gabanshi ta mai da masa da martani….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button