NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Ta hadiye wani kutun bakin ciki da ya tokare mata a makoshi, tace”Nayi nadama nayi dana sani Yanzu nagane abinda ‘Yar uwata keso na gane, dakin mijina shine suttura a gareni daku baki daya! Na gane duniya ba matabbata bace, a jiya dani daku da As mun nufi Ahmadu sharri sai Allah ya mayar dashi kanmu, idan da da ‘karar kwana da sai da a tsinci gawata a wani gari ruwa ya tafi dani, nan ta shiga warware musu abinda ya faru da ita jiya da irin taimakon da Ahamdun yayi mata, Uwani taja tsaki da fadin”To sai me dan ya fito dake daga ruwa aiko bai fito dake ba, idan Allah yasa zaki rayu zaki rayu….Wasila nifa bana sonki da wannn mutumin tunda bai san mutuncina ba bai ganina da daraja da mutunci, Yafi daukar wancan munafikin mutumin da daraja, sabida haka na tsani tarayyarku ke dashi wannan sakin da yayi miki shine dai-dai ni a gurina Nasan ke ba karamar mace bace zaki samu wanda ya fishi ki aura.”

Hawayen dake fuskarta tagoge tace”Uwani wai me yasa kike da ri’ko ne!? ki rabamu da dangin mahaifinmu saboda tsananin rikonki sannan kin sanyamu muyi musu rashin kunya kawai saboda ra’ayinki kin hanamu muje inda suke komai mai allo yayi mana mun yafe mishi kuma ni yanzu na daina ganin laifinsa a kanmu tunda muma ai bamu ganin kimarshi muna mishi fitsara da rashin kunya shiyasa ya kyalemu kuma sau nawa yana daukarmu kina zugamu mu gudo gida…..Ni yanzu shi kadai ne gatana shi zan nema domin ya sasanta ni da mijina domin hauwasa nacewa ta inda aka hau tanan ake sauka.”

Uwani ta mike tsaye! ranta idan yayi dubu ya ‘baci tace”Wasila idan kika saka kafa kikeje gurin wannan mutumin to wallahi ban yafe miki ba! mutukar nice na haifeki naci wahalarki kikaje gurin makiyina ban yafe ba, Saboda baki da hankali har zaki kirani mai riko meye banyi muku ba keda “yar uwarki shine har kike kokarin fifita Kawunki a kaina to na fada miki kikaje Garko gurin mai allo sai na tsine miki kin bi duniya.” Wasila da Rashida suka fashe da kuka jin abinda Uwani ke fada, zagi ta uwa ta uba takeyi wa mai allo daga karshe ma fashewa tayi da kuka ta shige daki……..Camas! dake tsaye ta kalli Wasila tace”Nifa wallahi banga abinda damuwa ba dan ya sake ki Haba kawata kamar ba kece wacce na sani ba shin wai me ma Ahmadu nan yake dashi ne

? Kawai ki watsar dashi ki cigaba da harkokin ai kamar yanda Uwani tafada wallahi sai kin samu wanda ya fishi kudi kyau mukami da sauran jin dadin duniya kefa matar manya ce.”

Wasila ta shiga girguza kanta bakin cikin duniya ya taru yayi mata yawa! Wai jama’a me uwani take so da itane shikkenan tunda tace bata yafe ba idan taje gurin mai allo ta amince da hakan zata zauna a gida amma kuma sai ta nemi mai ciyar da ita, Bayan haka kuma tayi al’kawarin har abada ta bar harkar jagaliya zata zauna ta killace kanta a gida…..Tace”Camas! dole fa naji ciwo mutuwar aure babu dadi wallahi ban san ina son mutumin ba sai da haka ta kasance dani, kina maganar zan sake samun wanda ya fishi ni bana fata nafi so kawai na koma dakina.” Camas! tace.”Yanzu dai kina nufin kin bar Siyasa kenan.”? Tace”Kwarai kuwa na bar wannan harkar abadah.” Uwani tace”Baki isa ba wallahi! Waye zai dinga daukar dawainiyarmu.” Wasila ta kalleta sosai tana nazarin maganarta, tace”Uwani kinga ni bana son ki d’aga min hankali tunda kin hanani zuwa gurin kawuna shikkenan maganar dawainiya kuwa kowa yayi dawainiya da kanshi, wannan gidan ma da muke ciki kada ki sanya ranki zaki dawwama a cikinsa, domin har yanzu governor bai bani takardar shi ba, da ko wane lokaci yana iya tashinmu mussaman idan yaji hukuncin dana yanke, saboda haka dake da Rashidan kowa ya nemi mafita, kada kuma kiyi la’akari da cewar ina da kudi a banki, kudina basu da wani yawa nima zan nemi wata sana ar ne.”
Uwani tace”Ai ba lallai sai siyasa zakiyi ba akwai sana’oi da zaki ki samu kudin da zaki cigaba da daukar nauyinmu saboda haka kije kiyi shawara ni dai na fada miki ban amince ki koma gidan wannan mutumi ba kuma ban amince kije gurin wannan dattijon banzan ba.” Tsabar bakin ciki da takaici bai bar Wasila tace komai ba idan ta fahimci maganar Uwani tana so ne ta turata d’aya sana’ar da tuntuni take so tayi ita kuma ta ta’kiyi (karuwanci) Mikewa kawai tayi ta shige daki ta barsu suna surutu Har dai Fada ya hard’e tsakanin Rashida da Camas! domin dai Camas! ita ke kara inginza Uwani tana sake baud’ewa! Yayin da Rashida ta fahimci haka sai ta hau cuccusawa Camas! ashar tana fad’in ta fice ta bar musu gida su dai Allah yasa sun gane gaskiya kuma karuwanci insha Allahu ba zasuyi ba, ita dai tunda ta dauki karuwanci sana’a to taje tayi! Camas! ta rataya jakarta ta fice daga gidan bayan sun gama zage zage da Rashida.

Littafin na kudi ne……!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262alliya:
‘Yr Bngr Sys
50

As ne zaune a tsakanin ‘yan sanda sai zare ido yakeyi rigar jikinsa duk tayi jirwaye fuskarsa duk tayi burd’in burd’in da cizon saura idanunsa sunyi jawur! fuskarsa ta kara baki sai maikon yake yi tamkar wanda rana ta daka!…….”Yanzu Yallabai tinda kace baka son kowa yaji maganar nan daga mu sai kai sai kuma Ahmadu to mun amince zamu rufa maka asiri amma tare da alkawarin muma zaka yi mana ihisani baka so sunanka ya ‘baci a gari mutane suyi maka kallon kwarto manemin matan mutane to zamu lullube sirrinka baza mu watsa a media ba muna so muji nawa zaka biyamu.” As yace.”Ku fadi ko nawa ne wallahi zan baku bana so Ahamadu yazo gurin nan ya sameni saboda nasan karon mu dashi ba zaiyi kyau ba, kuma ni ku daina zargin na nemi matarshi harkar siyasarmu ce ta hadamu da ita ba wani abun ba.” dan sandan yace.”Ka daina maganar Ahmadu domin tuntuni mun kirashi a waya ya tabbatar mana da cewar mu sake ka saboda bashi da lokacin ka, yanzu tsakaninmu da kai ne.” As ya sauke ajiyar zuciya yana jin sanyi cikin ranshi yaji dadi sosai da Ahmadu bai tona asirin abinda ke faruwa ba…..As yace.”Nace ku fadi ko nawa kuke bukata zan baku.” Babban cikinsu yace “Za bamu miliyan hamsin.” As ya zare ido yana kallonshi. Ba zaku samu miliyan hamsin ba yanzu.” Dan sandan yace.”Ashe kuwa kana so muyi maka tonan silili.” As yace.”Bana so kuyi min tonan silili wallahi zan duba nagani amma dai yanzu zan fara sa muku miliyan talatin daga baya sai na cika muku sauran.” Sukace Su basu yarda ba As ya shiga tunanin ina zai samu kudi cash a hannunshi duk kudinshi yana siyan filaye ne da gidaje da gonaki! yanzu duka kudin accont dinshi basu fi miliyan saba’in ba dama yana sanya rai kan governor zai bashi wata kwangila to anan yake so yayi cuwa-cuwar shi, wata shawara ce ta fad’o masa yace.”kuyi hakuri ku kar’bi! Miliyan talatin nayi muku al’kawari nan da sati biyu zan baku ashirin din.” Sukayi a rubuce ta da sharadin idan bai cika musu ba sun shirya tsaf zasu tozarta shi.
Ya mike yana karkade rigarshi ya dauki hularsa yasa kana daya daga cikin ‘yan sandan ya daukeshi a mota ya kaishi gidanshi, dake Tarauni.

Bacci yayi mara dad’i mai cike da mafarkai marasa dadi, sai wajejen azuhur ya tashi yay wanka ya fito damuwa fal cikin ranshi, bayan yay sallah ya dauki waya ya kira Khalifa tare da shaida masa cewar yazo gidanshi yana son zasuyi magana! Hausawa sukace abokin kuka shi ake fadawa mutuwa…..Baici wani abincin kirki ba, ya kwanta a kan kujera yana duba wayarshi, nan yay ta ganin numbers din mutane da rocuding din Wasila da As duk wani magana da Wasila keyi da As da Camas sai da ya gani dake wayarshi tana adana mishi abubuwa koda kuwa ya goge su, Al’amarin yayi ta bashi mamaki! ashe haka yarinyar nan tayi nisa, dama duk sanda ta dauki wayarshi abinda takeyi kenan! sosai ya dinga mamakin hatsabibancin ta, yana ganin rabuwa da ita shine yafi al’kairi a rayuwarshi…..Amma kuma har yanzu yana jin wani irin tsunkuli da zuciyarsa takeyi masa mussaman idan ya tuna da abubuwan da suka faru a tsakaninsa da ita a cikin zamantakewar da sukayi sai yaji gabanshi ya fadi sai ya kira sunan Allah yake samu sassauci! Hannunshi ne ya subce ya danno ma’adanar hotunanshi kawai hotunan da sukayi ita dashi ranar da al’amarin zai faru, suka wanke masa fuska, ya dinga duban hotunan yana mamakinta, sam! babu wata alama data nuna masa a ranar da zai gane ta shirya plan! Aje wayar yay dan baya son ya cigaba da kallonta sakamakon wani irin abu da yaji yana taso masa a cikin zuciyarsa, girgiza kanshi kawai yake yi babu shakka yarinyar nan tayi mishi ba zata!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button