NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Rashida ce ta sa mata kayan shi kuma ya dauketa a hannunshi suka fita daga dakin……..Garba ne ya tukasu zuwa asibitin dr nasir yayin da jikin wasila ya sake rikicewa sai salati takeyi tana yin wani irin nishi wanda kana jinsa kasan tana cikin halin ciwo……..Amadu addua kawai yake mata hankalinsa duk ya tashi lokacin ita kuma ta dinga rirrike masa hannunsa tana wani irin murkususu a jikinsa.

Littafin na kudi ne….
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
BINTA UMAR ABBALE
BINTA UMAR ABBALEalliya:
‘Yr Bngr Sys
73
A mutukar galabaice aka shiga dakin haihuwa da Wasila, Dr Nasir da wasu narses biyu suka rufu a kanta har sai da suka samu nasarar tsayar da jinin dake zuba daga jikinta, lokacin kuma ta daina duk wani yunkuri da takeyi duk karfinta ya kare bata gane wanda yake kanta, Dr Nasir ganin halin da take ciki na baraxana da rayuwarta ya sanya ya fita daga dakin da sauri, nan ya iskesu a tsaitsaye Amadu sai zurga zurga yake a gurin hankalinsa a tashe.
Dr yace.”Yallabai muje ofis zamuyi magana.” Amadu ya juyo yana kallonshi, ganin yanayin fuskar dr din ya sanya jikinsa yin sanyi sai kawai yabi bayanshi yana mi’kawa Allah a’lamarin.

Dr Nasir yace”Yallabai yarinyar nan ta galabaita sosai dan duk wani karfinta ya kare, ba zata iya haihuwa da kanta ba kayi hakuri ka sanya hannu yanzu mu shiga idata tiyata.” Wani irin gumi ne ya shiga yanko masa, idanunsa sunyi jawur ya karbi takardar dake hannun Dr din jiki a sanyaye ya sanya hannu ya aje takadar yana me dafe kansa Dr ya mike a hankali yace”Yallabai ka kwantar da hankalinka insha Allah za’ayi nasara.” Kanshi na ‘kasa har dr din ya fita daga ofis din bai dago ba dik ya rasa yanda zaiyi yana ganin kamar rashin hakurinsa ne ya janyowa yarinyar shiga wannan matsala……..Hannu yasa ya goge gumin fuskarshi ya mike ya fita daga ofis din da sa’bulallan jiki…..Hajja da rashida na ganin yanayin sa ai duk hankalinsu ya tashi,Rashida kam kuka tasa tana adduar Allah ya raba ‘yar uwarta da wannan wahala da take ciki.
Dr Nasir na komawa dakin sai yaga nurses din sun rufu a kanta, tun kafin ma ya fadi abinda ke bakinsa daya daga cikinsu tace”Dr insha Allah zata iya haihuwa da kanta dan gashinan yaron ya soma fitowa sai da babu karfi a jikinta wanda zata taimaki kanta.”
Dr nasir yace.”Alhamdullhi kuyi mata duk wani kokari da kukeyi mu gani idan bata haihu ba nan da minti goma za’ayi mata Cs domin ceto rayuwarta.
yana gama maganar sai ya fita daga dakin yaje yana shaidawa Amadu halin da ake ciki hannunsa ya daga sama yana rokon Allah ya sauketa lafiya.

To cikin ikon Allah Wasila ta dan samu karfi da kuzari a jikinta ta dan dunga taimakawa kanta gurin yin nishi yayin da su kuma narses din suke mata dabaru irin nasu, har Allah yasa kan babyn ya soma fitowa sai kawai suka yanke shawarar yankata domin rage mata wahala guri daya suka yanka, aikuwa tana yin wani yunkuri babyn ya fito tare da mahaifarshi…..Lokacin taji wani irin sanyi duk wani ciwo da takeji ya dauke da kyar ta kalato miyau ta hadiya ma’kogwaronta ya bushe kamas.
Cike da farin ciki narses din suka shiga gyara babyn suna kwarzanta kyawun yarinyar gata katuwar gaske tamkar ba haihuwar fari ba………Wasila na jinsu sama sama tsabar wuya da galabaita ta hanata motsa koda d’an ya tsanta ballanata ta bude ido taga abinda ta haifa.

Da saurin nurse ta fita cike da walwala da farin ciki ta samesu sunyi jugum jugum da sauri tace”Dr ta haihu yanzu an samu baby girl.” Dr Da Amadu suka mike da sauri sai suka soma rige rigen shiga dakin Amadu sai washe baki yake kamar gonar audiga…….Ita kam rashida zubewa tayi a gurin tana sujjadar godiya ga Allah…..Dukaninsu suka shiga dakin, muryoyinsu ya sanya Wasila dan bude idonta tana kallonsu dishi dishi taga sai murna da farin ciki sukeyi suna dariya, rintse idanunta tayi tana ajiyar zuciya tabbas sai yau tasan tazo duniya ashe haka mahaifiyarta tasha wuya kafin ta haifeta…….Dr Nasir ya kalli Amadu dake kokarin zuwa gadon da take kwance yace.”Yallabai ina ganin dole ayi mata karin jini saboda ta zubar da jini da yawa.” Yace.”Dr ayi komai idan da hali ma za’a iya daukar nawa idan zaiyi dai-dai da nata.” Dr Nasir yace.” okey to zan gwada yanzu.”
Kusa da ita ya tsaya yana dan kallon fuskarta lokaci kankani ta rame duk tayi zuru zuru, ya kama hannunta ya rike cikin nashi, idanunta ta bude tana kallonshi, a hankali yace.”Sannu.” Kanta ta daga mishi ta maida idanunta ta rufe………Hajja da Rashida suka karaso gurin suna mata sannu ba tare data bude idanunta ba ta daga musu kanta…..Hajja ta kalleshi da fadin “Gaggawa ta sanya bamu dauko komai ba dole aje a dauko mata kaya t

unda na jikinta sun baci.” Yace.”Bari na koma gidan yanzu.” Hannunta ya saki da sauri ya fita daga dakin……..Suna tsaye ita da rashida nurses din suka fito daga wani daki sun shirya baby tsaf da ita cikin kayan sanyi tana kamshin turare me dadi…..Hajja ta sanya hannu ta karbeta sai washe baki take tana musu godiya……..daya daga cikin narses din ta tsaya kusa da Wasila tana mata magana……bude idanunta tayi tana kallon narse din da kyar tace.”jiri ne kawai ke damuna sai bacci.” Nurse din tace”To bari na taimaka miki muje toilet na gyara miki jikinki sai ki kwanta kafin Dr ya shigo.” Daga kanta tayi narse din ta kama hannunta suka mike tsaye a hankali a hankali suka nufi toilet din dake cikin dakin…….ma dai-daicin ruwan dumi narse din ta hada mata ta zaunar da ita a jikin ruwan kana ta samu towel mai tsafta da wani ruwan d’umin tana dan danna mata jikinta………Fitowa tay daga toilet din wanda yayi dai-dai da shigowarsa dakin hannunsa rike da ledoji Hajja tace”Yawwa kayan ne ko.”? Yace.”Sune Hajja ina take.’? ya fada yana rarraba idanunsa a dakin….Hajja tace “Tana bandaki.” Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya dan tsaya kusa da rashida yana le’ka fuskar babyn tashi…..Hajja ce ta karbi kayan hannunsa ta mikawa nurse din ita kuma ta kar’ba ta daukar mata riga da zani na atamfa da pants da audiga guda biyu, ta juya da sauri ta koma toilet din

Rashida ta mi’ka masa babyn tana murmushi tace”Yayana kamarku daya da yarinyar na dauka ma zata dauko kammanin anti na saboda wuyar data bamu kafin tazo duniya.” Murmushi yayi ya karbi yarinyar yana kallonta yace.”naji dadi da tayo kammanina rashida nima ai nasha wuya kafin na sameta.”
Rashida na cike da farin ciki tace”Ubangiji Allah ya rayata ya bawa mamanta lafiya.” Ya amsa da “ameen lokacin da yake kara bakinsa kunnan yarinyar yana mata hud’uba gami da kiran sallah.

Ganin nurse din ta fito da ita daga toilet din a kimtse gashi tana tafiya da kafafunta sai ya sauke ajiyar zuciya yana sake godewa Allah da ya sanya komai yazo cikin sauki…….Dr ne ya shigo yace.” Yallabai zamuje yanzu a dauki jinin.” Sai yay gaggawar mikawa rashida babyn dake hannunsa suka fita daga dakin tare da dr din…..Rashida da hajja suka nufi gadon da Wasila ke kwance suna sake yi mata sannu, kai kurrum take iya daga musu bakinta ya mutu murus har yanzu tana tuno irin bakar wuyar da tasha acikin awannin da suka gabanta, rashida ta dan zauna kusa da ita a hankali tace”Anti wasila baki dauki babyn ba.” idanunta ta bude a hankali take kallon rashidan da babyn tayi murmushi a hankali tace “Rashida yarinyar na kama da babanta ko.”? Rashida tasa dariya tana kallon Hajja tace” Eh mana nida hajja ma haka muka ce.” Murmushi ta sakeyi ta rufe idanunta a hankali tace”Allah yayi mata albarka.” Rashida da hajja suka amsa da “ameeen”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button