NOVELSYAR BANGAR SIYASA COMPLETE

YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

Ranar Amadu da Khalifa sun sha dariya hankalinsu kuma ya kwanta sosai ganin suna samun nasara a cikin tafiyar tasu kullum ‘kara samun masoya sukeyi ta ko wane fanni.

Tun ranar da Inna hajara ta bar gidan a tsakaninsu suka daina samun jituwa wanda gaisuwa ce kawai take had’asu daga haka shikkenan zai fice harkokinsa, kuma koda ya dawo gidan yaga bai ga Inna Hajara baice mata komai ba itama ba tace masa komai ba, dukaninsu sun shiga cikin damuwa mai tsanani babu kamar ya ita kullum sai tayi kuka, ita bata ga abin fushi da daukar gaba ba ta lura yana da hakuri sosai amma bai iya fushi ba dan haka sai ta yanke shawarar tunkararsa ta bashi hakuri idan ya hakura shikkenan idan bai hakura ba zata rabu dashi duk ranar da ya gaji ya sauko dan kanshi………….Yau da wuri ya shigo gidan dan goma ma ba tayi ba, sai da ta bari Hajja da Rashida sun bar palon tukkuna ta fito daga dakinta tayi kwalliya sosai sai ‘kamshin turare take.
Murd’a kofar dakin tayi ta shiga da sallama a bakinta…..Babu kowa sai dai tana jin alamun motsi a toilet dinshi ta dan zauna gefan gadon tana bin dakin da kallo yaushe rabonta da shigowa tun ranar suna gashi yau kwananta talatin da bakwai da haihuwa saura kwana uku tayi ar’bain……Tana zaune tana sa’ke-sa’ke ya fito daga toilet d’in ‘kungunsa daure da towel da karami a hannunsa.
Had’a ido sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad’uwa…..Kadaran kadahan ya kalleta ba tare da yace komai ba ya ‘karasa bakin mirror ya dan tsaya yana sake

goge fuskarsa…..A sanyaye ta mi’ke ta isa inda yake tsaye ta ‘karbi towel din hannunsa tana so ta goge masa jikinsa, sai kawai ya bar mata gurin, Ta bishi da kallon mamaki yaje ya nemi guri ya zauna gefan gado yana shafa vasillin a jikinsa, ba tayi zuciya ba ta isa inda yake a hankali ta sanya hannunta ta ‘karbu vasilin d’in tana marairaicewa, Ya mi’ke kawai ya barta a gurin……..Wardrobe ya nufa domin daukar jallabiyarsa, da gudu taje ta rungume faffad’an bayansa tana shashshekar kuka tace”Kayi hakuri kaji.” Ajiyar zuciya ya sauke yana dan jin sassauci cikin zuciyarsa, shima dik abinda yake daurewa kawai yake yi yana dai so ya nuna mata kuranta ne, amma ba dan ya cuzguna mata ba, idan da ta kwantar da hankalinta shima ai yasan abinda yake yi ba zai ta’ba cutar da ita ba, amma ranar nan ya kwadaitu da ita mutu’ka ya kuma nemi ta a gaza masa ta’ki! dashi d’in manemin matane to babu shakka a ranar sai yaje ya biyawa kansa bukata amma haka ya hakura ya cireta daga cikin ranshi duk dan ya nuna mata kuskuranta

A nutse ya jiyo da ita suna fuskantar junansu, kasa hada ido tayi dashi ta sunkuyar da kanta ‘kasa tana goge fuskarta, a hankali ya sanya hannunshi ya goge mata hawayen fuskarta ya tallafo fuskarta sosai cikin tafin hannuwansa ya kallonta.
Takasa d’aga kanta ta kalleshi saboda kunya da kuma tsabar kwarjin da Allah yayi masa.
Murya a kasa kasa yace.”Me kikayi min kike bani hakuri.”? Sai ta dago fuskarta tana kallonsa.

Ya sanya d’an yatsansa saman le’banta na ‘kasa yana shafawa a hankali a hankali shi dai yana masifar son le’bunanta.

Kasa cewa tayi komai ta maida kanta ‘kasa tasan yana sane yake tambayar ta yafi kowa sanin kan abinda yasa take bashi hakuri.
Murmushi yayi a hankali ya cika fuskarta ya juya ya dauko jallabiya cikin wardrobe yana fad’in “Ina momyna ko tayi bacci.”? A hankali ta d’aga kanta tace” Yanzu nan na lalla’bata ta kwanta…..Hannunta ya ri’ke yace.”Muje parlo yau ke zaki bani abinci a gajiye nake.”

Taji dad’in yanda ya saki jikinsa sosai wannan ya sake tabbatar mata da cewar ya hakura da fushi da ita kuma ta lura dama kamar daurewa kawai yakeyi yana hakuri.

Ya zauna kan kujera yana dan dubawa babbar wayarshi yace.”Ki had’o abincin ki kawo min nan zanci.” Da sauri ta nufi daining din ta had’a mishi abincin komai da komai ta kawo gabanshi ta ajiye……’Kasa ya sauko hankalinsa na kan wayarshi yana dan juya abincin da cokali, sai ta kar’bi cokalin ta fara d’ebo abincin tana sa masa a bakinsa…….Kar’ba ya din gayi ba tare da ya kalleta ba hankalinsa gabakidaya yana kan wani text da Zeey tayi mishi.
Kafin ma ya gama karanta text din kiran wayarta ya shigo wayar tashi.
Dama tuntuni ya goge number ta cikin test dinta ma dan tasa sunanta ne ya ganeta.
Ganin numbarta tace ya sanya shi daga wayar a nutse yay sallama dake hands free ya bud’e Wasila najin muryar Zeey tana fada’in “Ranka ya dad’e barka da dare yau dai naci sa’a an d’auki wayata.”
Gabanta ne ya shiga fad’uwa sai hannnta ya soma rawa tana kokarin sanya masa a bacin a baki cokalin ya su’buce daga hannunta abincin ya zube a jikinsa sa kasan gurin.
Dan dubanta yay yana dan gyarawa hankalinsa nakan maganar da zeey ke masa yace.”Zainab ya kike ya gida ya kwana biyu.”
Zeey tace”Alhamdullhi yallabai Wallahi kwanaki nayi ta kiran wayarka domin nayi maka Allah ya raya baka dauka ba nace to ko wani laifin nayi.'”?
Murmushi yay a hankali ya dan koma saman kujera yace.” Ai ke bakya laifi Zainab mybe lokotan da kike kiran wayar ina da uziri ne shiyasa amma nagode kwarai kuma naji dadi da kulawarki.”
Zeey tace”Ai har taron suna nazo sai dai ban dad’e ba na tafi domin a ranar ana bikin wata friend dina ne.” Yace.”Masha Allah kema ai yana da kyau ki futar da miji kiyi aure Zeey kin kwana biyu fa.”
Zeey tayi dariya me shashshe’ka tace”Yalla’bai kenan aini da aure sai dai inga anayi namiji daya nake so a duniya amma ya’ki aurana.”
Yasan inda maganarta ta dosa sai ya nuna bai gane komai ba, Yace.”Zeey meye abunki? kina da ilimi sosai kana kina da kyau dai-dai gwargwado me kuma ake nema.”?
Murmushin takaici Zeey tayi tace”Duk da ina da abubuwan da ka

fad’a yanzu to shi banyi masa ba.”
Dariya yasa yana d’an sosa gemunsa yace.”Haba dai sai kace makaho ni da ba dan nayi aure ba da kawai na shigo anyi dani.” Zeey tayi wata dariya me shashsheka tana sake ma’kale murya tace”Ashe kasan inda maganata ta dosa tunda naga ka d’auko hanya, Yallabai ko yau kazo ni a shirye nake dama ai Ubangiji cewa yay kuyi Hud’u mutukar zakuyi adalci.” Ya bud’e bakinsa zaiyi magana yaga ta jefar da cokalin hannunta ta mi’ke rai a ‘bace ta bar gurun……Ya bita da kallo har ta bude daki ta shiga ta bugo kofar da karfin gaske…..sai kawai ya girgiza kansa ya cigaba da hira da Zeey inda take ta tsara masa kalamai ita dole sai ta samu shiga a gurinsa……..Yace.”Ki bari zan duba maganarki a tsanake zan kira ki a waya.” Cike da farin ciki da jin dadi Zeey tace”Shikkenan Yallabai ina sauraranka.” Kashe wayar yay ya ajiye ta kusa dashi ya gyara zamansa sosai ya cigaba da cin abincinsa.

Koda ta shiga dakin kwanciya tayi kan bed taci kukanta ta koshi ta kuma dauki al’kawarin yi masa rashin mutunci tunda dai shi bai san hakkin d’an adam ba in bansa wulakanci da rashin mutunci ya rasa ma a inda zaiyi hira da budurwarsa sai gidanshi kuma a gabanta lallai zata nuna masa cewar ta san abinda takeyi duk da take jahila to tasan ciwon kanta.

Sai da ya kammala cin abincinsa a tsanake tukkuna ya bita dakin, lokaci har tayi wanka ta kwanta tana bawa baby zahra nono ta tashi daga bacci, yazo ya tsaya kansu yana kallonsu, ganin yanda tayi bala’in shan kunu ne ya sanya ya kasa cewa da ita komai sai kawai ya tsuguna ya mannawa ‘yarshi sumba a saman goshinta ya mi’ke ya fita daga d’akin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button