
bude idona nayi ina sauke numfashi, nanemo number yaya sadiq na danna masa kira. Sadiq dawowarsa kenan daga restaurant yaje yasiyo musu abinci bisa takurawar aunty, dataga alamar babu me niyyar cin abinci, shine tace yaje yayo musu take away, ba’azauna haka ba’aciba. fita yayi daga dakin rejecting yayi sannan yakara kiranta. dama nasan baze dagaba sedai ya katse, kullum yaya sadiq cikin sakamun kati yakeyi amma baya taba daga kirana, sedai nakira aliya ko salimat musha hirarmu. dagawa nayi tare dayin sallama, amsamun yayi. Senaji muryarsa kamar bashi da lafiya. “Yayana lafiya kuwa, naji muryarkar haka?” Natambayeshi cikin kulawa. Numfasawa sadiq yayi yace, “lafiya kalau maryam, ina kikashiga naita kiran wayarki akashe?” Batare dana yarda da amsar daya baniba, nace. “Agajiye nadawo daga school ne, kuma ina dawowa bacci yadaukeni bandade datashiba” “ohk” kawai yace yayi shiru. nima shirunnayi na wasu sakanni kafin na katse shirunnamu dacewa, “anya kuwa yaya lafiya kake, naji muryarkafa akwai damuwa acikinta,pls dan Allah kafadamun meke damunka” wani zazzafan huci ya fesar yace, “maryam gaskiya da akwai matsala,yaya ne yau aka wayi gari bashi da lafiya,cuta me tsanani yanzuma muna asibi…..wata muguwar faduwar gabace ta ziyarceni, cikin gigita na katse yaya sadiq da fadin” wanne yayan kuma?” “yaya mustapha mana” shima yabani amsa. cikin sauri nace, “meke damunshi” bayanin halin da mustapha yake ciki sadiq yayiwa maryam atakaice. Kasa magana nayi saboda tsabar tashin hankalin jin heartbeat bashida lafiya. wani uban gumine yahau karyomun ta ko’ina ajikina, dukda banganshiba amma gabadaya tausayinsa yagama cikamun zuciya, naji babu abunda nake da bukata duk duniyarnan sama danaje nagansa naga halin dayake ciki. “Hello,maryam” muryar yaya sadiq tadawo dani cikin nutsuwata. wani yawu me daci na hadiye dakyar cikin tattaro nutsuwata, da sanyin murya nace, “na’am yaya, yanzu yajikinnasa” “dasauki za’ace maryam” “Allah yakara sauki,yabashi lafiya” “Ameen maryam,bari nakoma ciki.” Sallama mukayi yadatse wayar. Tagumi na rafka cikin matukar damuwa, Ashe dama bashi da lafiya shiyasa yau befitoba har rana. Wayatace tahau vibrate alamun kira. Ahankali nakai hannu nadakko, ganin aliyace nadauka dasauri. “Hello maryam Ashe yayan kano bashi da lafiya” “wlh aliya nima yanzu yaya sadiq yake sanarmun” “nima naje school ne nadawo natarar aunty batanan shine masu aikinmu suke sanarmun tataho kanone yaya bashi da lafiya,inata kiran wayarta taki shiga,shine nace bari nakiraki” hankali nane yakara tashi jin abunda,aliya tace. Kenan ciwonnashi ya tsananta matuka tunda har aunty dake wani garin tazo. bamuyi wata hirar kirkiba mukayi sallama, dukanmu zuciyoyinmu babu dadi,tadaicemun gobe zasuzo ita da abbansu. Zarya nafarayi adaki ina tunanin hanyar dazanbi inje asibiti ayau ingano yaya mustapha, dan inbanganshiba akwai matsala. yunwar danake jima tuni nanemeta narasa,hankalina gaba daya yanaga inje inga jikin heartbeat ………
Acan asibiti kuwa jikin mustapha ne yakara rikicewa numfashin nasa dayake fita dakyar dinma yadauke dif, hankalinfa su mommy gabadaya inyayi dubu yatashi, mommy ma faduwa tayi sedaukarta akayi itama aka bata gado, aka mata allura tasamu bacci. Suhailat kam kuka takeyi sosai iya karfinta, tana sumbatu tana fadin, “dan Allah yaya katashi karka mutu katafi kabarni” ire_iren wadannan kalamai kawai takeyi. Aunty kuwa babu kuka na ido sena zuci. Fitowa sukayi gabadayansu daga dakin dayake, sukuma likitocin suka dukufa akansa domin ceto numfashinsa.
su aunty suna bakin gurin atsaitsaye cikin karayar zuci, su haidarma se kuka suke, ga yaya ba lafiya ga mommy ma ta fadi,abun gwanin ban tausayi. Fiye da awa daya likitoci suna kan mustapha, har wani babban likitane yazo daban mesuna Dr, jibril. Karshema su aunty gani sukayi anfito dashi akan gadon tura marasa lafiya an nufi wani dakin daban dashi. Cikin tashin hankali su aunty sukabi bayansu dukansu, amma kafin su karasa har sun shige dashi dakin sun rufo. Hankalinsufa ya kara tashi, suka kara gigicewa. Se bayan magriba likitocin suka fito suna share gumi, dakyar suka samu numfashin mustapha yadawo ahakanma seda suka samasa oxygen, su Kansu likitocin ciwon mustapha ya tsoratar dasu yakeyi, gashi sunkasa gano takameman meke damunshi, sun masa gwajin jini, sundau hoton zuciyarsa, har gwajin kwakwalwa sun masa amma babu abunda suke gani na sakamakon wani ciwo nadamunsa. Abunda yake kara tsoratar dasu zafin da jikinsa yakeyi. Gabadaya su aunty sukayi kansu da tambayarsu ya jikinnasa, Dr, jibril ne yace musu subari suje suyi sallah su dawo, sesu musu bayani. Suma su sadiq din aunty cewa tayi suje suyi sallar, itama tatada tata agurin dama da alwalarta ta sallar la’asar. Suhailat kuwa tana zaune fuskarnan tayi jajur saboda kuka, wai ita batayin sallar. koda su yaya sadiq suka idar da sallah suka fito daga masallacin dake asibitin daddy yakirasa yasanarmasa yakaraso yana airport yazo ya daukesa. Shida zannurain suka tafi dakkonsa haidar da faruq kuma suka koma ciki. Aunty da suhailat na dakin mommy daketa bacci azaune, sunyi jigum_jigum. ahaka su haidar suka shigo suka samesu. Ahankali mommy ta bude idonta tana karewa dakin kallo, zumbur kuma ta mike zaune tana kokarin sakkowa,dasauri aunty da suhailat sukayi kanta suka riketa. Rungumeta suhailat tayi ajikinta tana fashewa da kuka. “Saudart, ina my son, yamutu ko, dan Allah karkicemun ya mutu” mommy ta fadi haka tana haki. Aunty bata,bata amsaba seda tajinginata da filon dake kan gadon sannan tace, “be mutuba aunty atika,amma suncanza masa daki kuma sunki barinmu shiga,amma babban likitan yace zasuje suyi sallah seyazo ya mana bayanin abunda kedamunsa” lumshe ido kawai mommy tayi batace komaiba. Mikewa aunty tayi domin sanarwada Dr,mommy ta farfado. a tare sukadawo dakin dawata nurse mace, sannu tayiwa mommy tare da tambayarta jikinta, dakai kawai mommy ta amsa mata. Duddubata takarayi ta fice. Su haidarma sannu sukayiwa mommy suka sanarmata isowar daddy. Agigice daddy yakaraso cikin asibitin, su sadiq na biye dashi abaya. dakin da sadiq yanuna masa mustapha yana ciki yanufa direct da nufin shiga,amma Dr jibril yatsaidashi. Tsayawa daddy yayi yana kallon Dr. Hannu Dr, yamikawa daddy sukayi musabaha yakara da fadin. “Ranka yadade, barka da wannan lokacin dafatan ka sauka lafiya” “lafiya kalau” daddy ya bashi amsa akagauce.danya matsu yaji meke damun dannasa. Fahimtar hakan da Dr, yayi seyace. “Idan babu damuwa,mu shiga nan dakin namuku bayanin gabadaya dan bayanin bazeyiyu atsayeba” yakarashe zancen da nuna dakin da mommy take ciki. dakin suka nufa gabadayansu. Mommy tana ganin daddy, takara rikecewa,itadai abarta taje taga danta. Karasawa kusa da ita daddy yayi cikin rarrashi yace, “kikara hakuri, atika insha Allahu zaki gansa anjima.” Cikin kuka mommy tace, “daddy danbaka halinda my son yake cibane, bafaya numfashi….” lallaba mommy daddy yahauyi, dukda shima dauriya kawai yakeyi, amma zuciyarsa kwadayin ganin dansa kawai takeyi. bayan mommy tayi shiru, suka maida hankalinsu duka akan Dr dominjin mezece. Gyara murya Dr,yayi yafara magana yana duban daddy. “Ranka yadade, azahirin gaskiya munkasa gano takamaimen ciwon dake damun yaronka, munyi iya gwaje_gwajenmu akan duk abunda muke zargin ze iya haifar masa da wannan ciwon, amma result din dai baya bamu da wani ciwo ajikinsa. ” haba doctor duk halin da dana yake ciki, amma kace kunkasa gano ciwon dake damunsa gaskiya Dr, nalura kamar bakusan aikinkuba, nidai Ku sallamemu kawai mucanza wani asibitin, kokuma mu fita dashi waje.” Cewar mommy cikin zafin zuciya. Duban mommy Dr, yayi yace. “Hajiya bahaka bane, tun safe likitocinnan suke kansafa, ganin sun kasa gano mekedamunsa suka kirani. Ni’inama tsaka da aiki suka kirani, dabama zanzoba seda suka sanarmun yaronkune dakuma halin dayake ciki, haka na katse komai danakeyi nataho. ina zuwa ko zama banyiba nadukufa akan dubasa,amma haryanzu danake muku bayaninnan bamu gano meke damunsaba. amma ina ganin ta bakin naki zamubi, afitar dashi wajen kawai,su zasufimu gano mekedamunsa. Numfasawa aunty tayi tace, “bantari numfashinkaba doctor amma ni ayanda naga jikin mustapha dakuma bayananku kamar ba ciwon asibitine kedamunsaba, ina ganin kawai mukoma gida ayi masa na hausa.” “Wanne irin na hausa kuma, mekike nufin yana damun yarona, nidai babu maganin hausan daza’ayiwa dana, kawai a fitarmun dashi waje aduba lafiyarsa.” Mommy tafadi haka cikin hayayyakowa. Gyada kai doctor yayi yana kallon aunty yace, “tabbas abunda kika fada hajiya gaskiyane. Don muna samun irin wannan case din, na irin wadannan ciwukan da’ake rasa kansu dadama. Amma daga ankoma gida anyi nahausa sekaga andace idan Allah yaso. Ni likitane danasan aikina,amma idan zakuyi amfani da shawarata, ku koma dashi gida Ku nemar masa maganin hausa, idanma fitar dashidin zakuyi to kukaishi kasa me tsarki. (saudiya) domin gaskiya bana tantama ciwon dake damun mustapha bana asibiti bane, kodan wani irin zafi da jikinsa yakeyi……..✍️