Kafin mu shiga kofar falon seda muka jira aka bude mana,wowww na furta acikin zuciyata saboda girma da tsaruwar falon,babu wani tarkace acikinsa,amma falon ya matukar haduwa fiye da wadanda muka wuce na baya.kalle kallena nakeyi bansan mun iso gaban mutanen gidanba,seda hajiya ta taboni sannan na dawo hankalina,zubewa hajiya tayi akasan carpet, din dake malale a falon.nima tsugunnawa nayi kaina a kasa,araina nace lallai gaba da gabanta.Hajiyace ta fara magana cikin girmamawa,”Hajiya barka da hutawa,dafatan kina cikin koshin lafiya,dafatan na sameku lafiya.wata murya me cike da aji da izza naji tace”lafiya kalau lami,kin cika alkawari dafatan yarinyar ta cika duka sharadan Dana lissafo miki.”eh hajiya gaba daya ta cika,babu matsalar komai.maida dubanta matar gidan tayi kaina tacemun “yan mata yaya sunanki.se alokacin na dago na dubeta kai masha Allah,ta dace da gidannan gaskiya,kyakkyawace sekace India,tayi ado cikin wani rantsatstsen less,koda bansaniba amma babu shakka kunnanta da hannuwanta da wuyanta daham,saboda yanda suke daukar ido. “maryam” na furta a hankali, saboda tsareni da tayi da ido tana kallona.kawar da kaina nayi gefe,kyawawan samari guda hudu idanuwana sukayi tozali dasu,tamkar babu su a falon kowannensu yanata latsa wayarsa.kamarsu daya gaba dayansu dayane kawai ya banbanta dasu.sunkuyar da kaina nayi saboda wani mugun kallo da daya Daga cikinsu ya wurgomun. Muryar hajiyar gidan naji tana cewa”shikenan lami,zaki iya wucewa zan miki transfer zuwa anjima,sauran abubuwan kuma zamu tattauna awaya. “To hajjaju makkatu,nagode Allah ya kara girma da daukaka da arziki Mara yankewa,na barki lafiya. Da ameen kawai ta amsa mata.mikewa hajiya,danaji itama ankirata da lami tayi,tayi mata sallama.dafa kaina tayi “to maryam Nina wuce,semun sake haduwa. Kawai senaji kwalla tacikomun idanuwana,senaji banaso tatafi ta barni domin bansan taya zanfara rayuwa awannan gidanba.gyada mata kai kawai nayi,har lokacin kaina yana kasa.ina wasa da yatsun hannuna.
Bayan tafice daga falon hajiyar gidan,ta umarci wadda ta mana jagora datakaini dakin dazan zauna.tashi nayi nabi bayanta.Acikin falon ta nunamun dakin dazan zauna.abude yake hakan yasa tura kofar dakin nayi kawai na shige.katon dakine me dauke da saitin kayan gado masu tsananin kyau da daukar ido.tsayawa nayi ina karewa dakin kallo,ko ina tsaf dashi tamkar da mutum aciki.”Yanzu ni zan kwana a wannan dakin nikadai,a wannan dakin zanci gaba da rayuwata,dakin da ko rabinsa a kyau bantaba tunanin shigarsaba,Jan kafata nayi na karasa bakin gadon,na zauna.katifar dake kan gadonma ita kanta ta dabance.ajiye kayana nayi.ina cigaba da karewa dakin kallo tare da sake_sake iri iri araina,da sabuwar rayuwar dazan fara.
Kiran sallar magriba ne ya tasheni daga karanta wasikar jakin danakeyi.wata kofa Dana gani acikin dakin na nufa wadda nake kyautata zaton ta bayice.ina budewa kuwa naga toilet ne.shima toilet seda nayi kauyanci araina nace sekace daki shima.wasu abubuwan dabantaba ganinsuba nagani,banyi karambanin taba komaiba,famfo kawai na kunna nayi alwala nafito.na idar da sallah,kenan ina addu’oina matar data kawoni dakin ta shigo da sallamarta.amsa mata nayi se alokacin nasamu damar gaisheta amsamun tayi fuskarta dauke da murmushi. Tace”Kizo inji hajiya tanason ganinki. ” Mikewa nayi nayi bayanta muka fice daga dakin.kamar dazu yanzumma ita da yarantane,sedai yanzu naga wata mace,tana kwance akan cinyar hajiyan ita kuma tana shafa kanta,tana mata magana.agabansu naje na durkusa kaina a kasa nace “hajiya gani. Dasauri naga budurwar dake kwance akan cinyarta ta mike zaune………✍️
By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
0️⃣6️⃣
…………Nunani ta farayi da hannunta tana jifana da wani mugun kallo”mommy wannance me aikin. shafa kumatunta hajiyan tayi “eh,itace daughter.”Ammafa mommy senaga kamar bazata iya aikinba,kalletafa sanyinta yayi yawa.jifa yanda take tafiya kamar bata da laka. ” hmmm,daughter kenan rabu da ‘yayan talakawannan idan sunason kudi zagewa sukeyi,suyi aiki.tabe baki tayi bata kara cewa komaiba,amma se kallona takeyi.nidai ina durkushe ina dubansu. Maido da dubanta hajiya tayi gareni ta faramun magana. “Maryam kikacemun sunanki ko? “eh hajiya. “ohk, Aikin dazakiyi agidannan iya part dinnanne,kawai.anjima za’azo a miki bayanin aikin daza kidingayi.ina fata bazan samu matsala dakeba,kinga wadannan,ta nunamun duka matasan dake dakin.ahankali na dago ina dubansu.taci gaba da magana.dukansu ‘yayanane,idan sukaje aiki suka dawo anan suke zama,saboda haka kome suka saki kiyi,banason bacin ransu kokadan dan haka kibisu sau da kafa. “Insha Allah hajiya zankiyaye. nafada cikin sanyin murya ta.”zaki iya komawa,dakinki.harna mike sekuma naga dacewar naje nagaida ‘yayannata. Gabansu naje na durkusa nace. “ina wuninku.”Daga Wanda yadago ya wurgamun kallon banza,seme bina da harara,da kallon tsana.guda dayane Wanda kamarsa ta bambamta danasu.ya ajiye wayar hannunsa,fuskarsa dauke da fara’a ya amsamun gaisuwata.harda ‘yan tambayoyi yamun.tare damun fatan nasara arayuwata.naji dadi sosai yanda be kyamaceniba kamar sauran ‘yan uwansa.mikewa nayi jikina a matukar sanyaye na fara tafiya.karaf idona ya hadu Dana wannan budurwar.wani kallon tsana naga tana jifana dashi se wani yamutsa fuska takeyi tamkar taga kashi. “Jibeta yanda take tafiya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki.muryar budurwar na tsinkayo tana fadar haka.kwashewa da dariya naji sunyi,”to kekuwa suhailat bataci ta koshiba ai dole kiganta haka.da sauri na karasa dakin danasauka,dan bazance nawaba.idona ya cicciko da kwalla.saboda na fuskanci mutanennan basusan darajar dan Adam.yanzu haka zanyi rayuwa acikinsu.tsanata da kyamata kawai nake hangowa a atattare dasu,nabar kyarar gwaggo Ashe nanma zan tadda wata.hawayene yafara zubowa Daga idanuwana,na tausayin rayuwata.
Turo kofar dakin akayi,da sauri na dago ina kallo bakin kofar.wata ‘yar tsohuwace domin ko tantama banayi tayi jika dani.sallama tayi na’amsa mata,ina goge hawayen fuskata.tsugunnawa nayi cikin girmamawa na gaisheta.murmushi tamun,tana amsamun gaisuwata.kamo hannuna tayi muka zauna a bakin gado.”yarinya yaya sunanki. “Sunana maryam. “Allah sarki,maryama ta baban gida,.ni kuma sunana talatu nice babba a masu aikin gidannan,nice wadda hajiya ta turo in miki bayanin aikin dazakiyi amma kafin sannan,idan bazaki damuba inason jin labarinki,wato tarihin rayuwarki. Dasauri na dago ina mata kallon mamaki. “mamaki kikeyi ko ‘yannan,na shigo na tarar dake kina kuka,Daga gani dole akayi miki a aikinnan,inason jin labarin kine domin insan ta inda zan iya taimakonki.
shiru nayi ina juya maganganunta araina,banason tuno abubuwan da suka faru a baya arayuwata,amma kuma a kallo daya danayiwa matar ta shiga raina,kuma bazan iya mata musuba,kodan kasancewarta babbace. ” Baaba,labarina yanada yawa amma zan takaita inbakishi. “Yawwa yarinya,dafatan bantakuramikiba,inason sanin wani abune Daga gareki,domin nima inason sanar dake wani Abu game da gidannan.numfashi naja tare da gyara zama na farabawa baaba talatu tabarina.