Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

BY
ZEEY KUMURYA
ABINDA KASHUKA…

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣0️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Ya ƙarashe zancen da lakucewa Abul kumatu, shiko se bingira masa dariya yake abunsa. murmushi Aunty zuhura da YaSaddam sukayi me sauti. Umaimah kuwa sakin baki da hanci tayi tana kallonsa cikin tsananin baƙin ciki da takaicin yanda ya dizgata a gaban matarsa. ita mamakima take ko a ina yasan gashinnata oho?. kallonsa nake nima cikin mamakinsa, kamar bashi yayi maganar ba ya wani waske yanawa Abul wasa. A hankali ya juyo ya kalleni ya kannemun ido ɗaya tare da dagemun gira, lumshe idona nayi a hankali saboda salonnasa ya tafi dani. Mayafin Maryam daya ɗan zame yasaka hannunsa ya janyo tare da maida mata gashin daya fito ciki. numfashi na sauke a hankali still idona na lumshe saboda tattausan hannunsa daya taɓa gefen fuskata. umaimah ta hadiye wani yawu me daci da kyar, duk abunda mustapha yayiwa maryam akan idonta. mikewa tayi fuu cikin bacin rai ta shige dakinta. Dan idan tacigaba da zama a falonnan se zuciyarta ta buga. suna haɗa ido da ammi ta hararareshi tace, “ka kyauta ka batamun ran autah” murmushi ya mata kawai bece komaiba. numfashi na jawo na fesar da kyar na buɗe idona. batare dana kalli kowaba ba mike na shiga dakin Ammi na dakko kayana. Kafin na fito har yabawa yaya sadam Abul ya fice, sallama na musu nima nabi bayansa. yana zaune a falo idanunsa a lumshe na shigo falon bakina dauke da sallama ƙasa_ƙasa. A zuciyarsa ya amsa mata. Bedroom ɗina na wuce ganin be kulaniba, da niyyata inje innuna masa kayan sallar da ammi tamun. Bayan fitar su Maryam Ammi ta shiga bedroom din Umaimah ta rarrasheta, umaimah harda kuka dan bakin ciki. misalin ƙarfe 11 na dare ina kwance akan gadon idona a lumshe amma ba bacci nakeba, tunanin heartbeat kawai nakeyi, tunda nashigo dakin na kwanta amma nakasa bacci se juyi nake, har light din dakin na kashe. a hankali naji turowar kofar dakin gami da shaƙar kamshinsa. buɗe idona nayi amma ban motsaba zuciyata na ɗan bugawa. Kunna touchlight ɗin wayarsa yayi ya haska kan gadon, yasan dama zuwa yanzu tayi bacci. Ledar daya shigo da ita ya ajiye a gaban madubi. Seda ya ɗanyi jimmm, kamar me nazarin wani abu sannan ya fice. Ajiyar zuciya nasauke, na ƙara maida idona na rufe. Inajin kamar na tashi na bishi mu kwana tare amma bazan iyaba, duk yanda nakeson hakan dole na jure na hakura…..

Washegari ranar idin sallah ƙarama, ranar da kowanne musulmi yake farinciki da fatan zuwanta, hakance ta kasance nima a gurina. Tunda asuba na tashi nayi ayyukana saboda nasamu damar zuwa sallar idi. kafin karfe bakwai nagama shirina cikin wata dakakkiyar shadda milk colour, tasha ɗinki me matuƙar kyau. feshe jikina nayi da turaruka masu sanyin kamshi. ledar dana gani tunda na tashi najanyo na shiga dubawa. Takalmane masu kyau kala biyu da jaka, da mayafai da sarka da ɗan kunne harda agogo duk a cikin ledar. murmushi nayi cikin jin daɗi. ƙarfe bakwai da rabi nanufi part din ammi cikin shirina tsaf na zuwa Masallaci. Acan na tarar da yaya sadam da Aunty zuhura suma cikin shirinsu. Gaisawa mukayi cikin fara’a. Ammi bata falon hakan yasa na wuce dakinta. bansan yana cikiba seda nashiga na ganshi zaune gefen gadon ammi da waya kare a kunnensa alamun waya yake. zama nayi akan carpet din dake gaban gado bayan mungaisa da Ammi, ina satar kallonsa ta gefen ido. yayimun kyau sosai fiye tunanin me karatu, shadda ce fara ƙal ajikinsa, kansa dauke da hula wadda ta masa kyau bakadanba. ƙasa dauke idona nayi daga kansa. Maganar ammi naji tana cewa, “NOOR kabata wayar su gaisa da UNCLE dinnaka, kullum yana tambayata ita amma basu taba gaisawaba. gyada mata kai mustapha yayi sannan ya mikawa Maryam wayar. tashi nayi a hankali naje na karbi wayar ina kallonsa shima kallonnawa yakeyi se idanunmu suka sarke cikin na juna. Runtse nawa idon nayi da sauri saboda yanda naji bugun zuciyata ya sauya. kara wayar nayi a kunnena tare da faɗin “Assalamu alaikum” cikin murya me cike da nutsuwa naji ance, “wa’alaikimussalam” “ina kwana” na furta hakan bugun zuciyata na karuwa. “Lafiya kalau, Maryama” yanda na faɗi sunannawa senaji wani iri a zuciyata dana kasa tantance menene, numfashi na jawo na fesar da kyar nace. “Dafatan anyi sallah lafiya”…. Mungaisa dashi sosai, yamun addu’oi dafatan nasara arayuwata. godiya na masa na mikawa yaya wayar. Bayan sun gama wayar mustapha ya dubi ammi yace, “yace zezo cikin watannan insha Allah” da’alamun mamaki akan fuskar ammi tace, “dakuma yacemun baze samu zuwaba, saboda ayyuka sunsha masa kai sedai wani watan.” “Hakadai yacemun yanzu” mustapha ya fadi haka yana mikewa da niyyar fita. “To Allah yakaimu lafiya.” Gaba dayanmu gidan muka dunguma zuwa masallaci. Nida ammi da umaimah muka hau motar yaya. Aunty zuhura, da mama da mama A’isha da mijinta suka hau motar yaya sadam. Anyi sallar idi lafiya antashi lafiya sedai fatan Allah ya maimaita mana. bayan antashi Aunty zuhura tayiyyi mana pictures a wayarta sannan muka dawo gida, aka cigaba da hidimar Sallah……

KADUNA

Aunty ce tafito cikin shirinta na zuwa Masallaci dakin da suhailat da aliya suke ta nufa domin takirasu ganin sunki fitowa. da sallama ta shiga amma saboda cacar bakin dasukeyi basujiba. tsayawa kawai Aunty tayi tana kallon aliya dake magana cikin tsiwa. “Wlh nidai nagaji da kazantarnan taki gaskiya, amma kome zaki faɗa sedai ki faɗa Ni… Tsawa Aunty ta daka mata da faɗin. “Aliya mene haka? wanne shashancine wannan?” Cikin bacin rai aliya tace, “Aunty kullum fa bata ɗauke ko tsinke a dakinnanan amma bana magana haka zangyara, amma baya jimawa ta ƙara batawa, yauma ina tashi na gyara shi amma daga fitowarta daga wanka harta fara batawa, danna mata magana ta fara zagina wai zan mata rashin kunya, ko dan naga gidanmu tazo.” Rai a haɗe Aunty tace mata. “Shine dan baki da kunya zaki faɗa mata haka, sa’arkice. Kuma dan bata gyara dakiba seya zama abun magana bakya ganin bata da lafiyane.” Aliya zatayi magana Aunty ta katseta da sauri. “Banason na ƙara jin bakinki anan, zoki fice kikirawomun abbanku mu wuce, karmu makara.” Aliya kamar zatayi kuka dan takaici ta fice ɗaga ɗakin. Fuska babu walwala Aunty ta dubi suhailat dake cika tana batsewa ganin bata da alamun shiryawa tace, “ke bazaki masallacin bane?” Suhailat na yamutsa fuska tace. “Banajin daɗin jikina bazan iya zuwaba.” wani kallo Aunty ta mata me kama dana tuhuma harseda suhailat ɗin ta tsargu sannan ta fita batare datace mata komaiba. Suna tafiya a mota ammi ta dubi aliya cikin ƙasa_ƙasa da murya dan kar abbanta dake gaba yaji tace mata. “Kidena kula suhailat kuna hayaniya, yar uwarkicefa Aliya, kuma gaba take dake.” aliya kamar zatayi kuka tace, “Aunty itacefa…” Cikin lallami Aunty ta katseta da faɗin, “kiyi hakuri da duk abunda zata miki, kidena kulata kinji ‘yar albarkata” gyada kai aliya tayi tana turo baki gaba. Bayan sun dawo daga masallacin sunci abinci ammi ta nufi ɗakin da suhailat take. suhailat tana kwance tana aikin kallon hoton mustapha daya zame mata jiki Aunty ta shigo dakin. zama Aunty tayi akan gado tana duban suhailat dabatasanma ta shigoba tanacan tana tunanin Mustapha tace. “Suhailat!” Firgigit suhailat ta dago ta kalli Aunty, amma tagaza cewa komai. Aunty bata damu da yanayin datake cikiba tace, “meyake damunkine wai naga bakida walwala.?” Idantane ya kawo ruwa cikin raunin murya tace. “Inason ganin yaya, nayi kewarsa” Aunty na tsareta da ido tace. “Bayan wannan fa?” tana kauda kai daga kallon Aunty tace. “Nothing” fuska babu walwala aunty tace. “Suhailat kina boyemun kina da ciki ko?” Rassss gaban suhailat ya yanke ya fadi duk tsagerancinta seda ta girgiza dajin Aunty ta gane tana ciki. Tashi zaune tayi cikin rudu tace, “Aunty ciki kuma?” Harararta Aunty tayi tana ƙara haɗe rai tace. “Karki ƙara yunkurin boyemun, tun kafin kizo duniya nake ganin mata masu ciki, kuma nake ganesu. Tun kafin azumi nagane ciki gareki ta alamomi masu yawa da suka nuna musamman yanzu da cikinnaki ya fara fitowa.” Aunty ta ƙarashe zancen tana kallon cikin suhailat daya fara dagowa dan wata huɗu da kwanaki. suhailat kasa magana tayi se kuka data fashe dashi. Tausayintane ya kama Aunty, duk da abu yana tadda hali amma suhailat mommy ce ta cuceta dabata tarbiyya tagariba. Lokacin da Aunty ta gane suhailat tanada ciki bakaramin dimuwa da damuwa tashigaba. ƴar ɗan’uwanta guda ɗaya jal daya mutu ya bari itace da wannan abun kunyar, tasan baƙaramin tashin hankali daddy ze shigaba idan yaji wannan zancen, shiyasa har yau ta kasa sanar masa……Muncigaba da shagulgulan sallah cikin kwanciyar hankali, munjejje unguwa da ammi munje gidan su Aunty zuhura har danginsu mama duk mun zazzaga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button