Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

AYI HAKURI DA TYPING ERROW BA EDITING NE

By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

3️⃣1️⃣

………..Nidai gaskiya doctor dana bazan masa maganin hausaba,kawai Ku sallamemu yanzu mucanza asibiti kafin safiya muyi shirin fita dashi waje,tunda Ku kunkasa gano abunda kedamunsa.” Mommy ta fadi haka tana batarai. Kallonta aunty tayi yanda take hakikancewa tana magana tamkar ba ita tagama lagwai_lagwai dazuba. Daddy da tunda aka fara maganar bece komaiba seyanzu ya numfasa yana duban doctor yace, “amma doctor mekake tunanin yana damunshi,kokuma yake kawo irin wannan ciwon haka.” “Agaskiya alh,a yanzu dai bazance gashiba amma su masu maganin idan kukaje gurinsu zasu sanar muku da yardar Allah,yanzudai Ku barshi anan zuwa safiya mukara ganin abunda Allah zeyi akansa, semusan abunyi.” “Toh shikenan doctor mungode yanzu zamu iya zuwa muganshi” “ehh,zaku iya zuwa ba matsala,amma se’akiyaye,danma naga kundamune shiyasa nabarku kuje kuganshi,amma aka’ida babu meshiga gurinsa,ayanzu. “ohk,insha Allah zamu kiyaye Dr.” musabaha daddy sukayi da doctor yamusu sallama ya fice. Babu bata lokaci suma su daddy suka mike dukansu suka nufi dakin da mustapha yake. Yanayin dasuka ganshi bakaramin kara firgita daddy yayiba,gashinandai akwance shiba rayuwaba shiba mutuwaba, tambayoyi daddy yafara yiwa mommy akan ko abu yasamesa jiya kafin ya kwanta,kokuma yace mata wani guri najikinsa na masa ciwo, mommy tace babu komai lafiya kalau suka rabu. jikin daddy gabadaya yayi sanyi da ciwon mustapha, harya fara tunanin ko ciwon ajali ne yakama mustaphan dan haka yake shima arasa meke damun mutum. Addu’a kawai daddy yashiga yimasa acikin ransa akan Allah yabashi lafiya….

Yinin yau gabadaya cikin rashin nutsuwa nakarasashi, nayi tunanin duk hanyar dazanbi dazan iya zuwa naga yaya mustapha a yau amma bansamuba. Gashi banason na kira yaya sadiq akan inason zuwa, yayi tunanin wani abu daban,zama nayi naita tunane_tunane har akayi sallar magriba. Dakyar na iya tashi nayi sallah, sannan na dafa indomie guda daya,na watsawa cikina dan kar yunwa tamun illa. Ganin duhun dare yayi se tsoro yakamani ni kadai a part din. kamar daga sama naji tunanin abunda yafaru dani ranarnan yadawo cikin kwanyata, tiryen tiryen kamar yanzu abun yake faruwa. wani matsanancin tsorone yakamani, cikin sauri na mike na dauki wayata nafice daga part din gabadaya bayan na janyo duka kofofin part din na rufe. Part din su baba talatu nanufa,ina tafe ina tunanin abunda yafarun a kokarina nasan tuno wanene yazo da niyyar ketamun haddi, duka dai yayan gidan nasan muryoyinsu harma da megidan, kuma Wanda yazomun dindai yayi magana, “tokodai yaya faruq ne?” natambayi kaina, domin shine tunda nazo gidannan, jin muryarsa danayi befi a kirgaba. zato zunubi hakan yasani yin istigfari tare dayin addu’ar koma waye Allah yakareni daga mugun nufinsa. koda naje part din su baba talatu naji sunata zancen ciwon mustaphan, dayake drivern dayakai su mommy asibiti akwai matarsa acikin ma’aikatan gidan agurinsa ta jiyo musu. Nidai dakin baaba talatu nashige na kwanta bayan mungaisa dasu. zuciyata sam babu dadi, namarasa meyake damuna ahalin yanzu. Karatun kur’ani me girma na kunna awayata inaji ko zuciyata zata samu sukuni…….

Acan asibiti kuwa tuburewa mommy tayi ita se’ancanzawa mustapha asibiti tunda nandin sunkasa aiwatar da komai. Hakuri daddy da aunty suka shiga bata tare da nuna mata, itafa lafiya ba likitoci ke bada itaba, Allah ne yake badawa a lokacin dayaso. Dakyar mommy ta hakura akan su kwana a asibitin zuwa safiya se’asan abunyi kamar yadda doctor yafada. Bayan sallar isha’i daddy yacewa dasu sadiq sukoma gida hakannan dasafe sazo, mommy kam dama anan zata kwana, suhailat ma daddy yace tabiyo su yaya sadiq amma tace, Sam itama a asibitin zata kwana, haka daddy yace abarta ta kwanan. Aunty kuwa harta mike zata tafi, daddy yace ta zauna itama ta Kwana,tace masa ai anyi yawa amma yace ta kwanandai danyaga tafi mommy hayyaci. shima zuwa anjima ze koma gida idan sungama tattaunawa da doctor. Adakin baba talatu nayi sallar isha’i, abinci ta zubo ta kawomun nace mata nakoshi naci abinci kafin na fito. Takuramun tayi naci kadan danma naji dadin zuciyata danaji karatun. Harna kwanta yaya sadiq yakirani, yacemun ina ina, nacemasa ina part din su baaba talatu, yacemun meyasa bazan kwana a part dinmuba, nace masa tsoro nakeji nikadai. Wai ni raguwace banda haka mene abun tsoro nadawo nan na kwanta, nace masa wlh bazan iyaba. Badan yasoba ayanda na fuskanta ya hakura ya barni na kwanan anan. sanarmun yayi yadawo gida zedebarwa su mommy kayane yakaimusu seya dawo, kamar nace masa zan bisa sekuma naji becemunba nima senayi shiru, amma yasha tambaya aguna akan yajikin yaya mustapha. nikadai adaki su baaba talatu suna falo suna hira, se juye_juye nakeyi akan katifa amma nakasa bacci. Mikewa nayi dama da alwalata nashiga jero nafilfili akan Allah yabawa heartbeat lafiya……….

Washegari,tunda sassafe daddy da sadiq suka koma asibiti, inda suka tarar da wani mummunan tashin hankalin,domin jikin mustapha yafi yanda suka barshi jiya rikicewa, dansu mommy kam yanda sukaga rana haka sukaga dare, dakyar likitocin suka samu suka shawo kan matsalar numfashinsa ya daidaita. Babban tashin hankalin su mommy rashin farfadowarsa. ganin haka yasa daddy babu bata lokaci yafara kiciniyar fitar dashi kasa me tsarki domin aduba lafiyarsa. Kafin karfe goma nasafe yan dubiya sunfara zarya a asibitin, danma ba’abari ashiga aganshi sedai ayiwa su mommy yame jiki. Abokanan daddy da iyalansu gamida makota da mutanen da’ake mutunci se tittidowa suke ta ko’ina. rashin lafiyarsa ta barbazune a daren jiya da yan’uwansa suka dora a social media. Yan’uwansu daddyma sunzo ba lefi,hakama na mommy………
Baccin dana samu yau bawani ishashshe bane, danbefi na awa biyu da rabiba, nadade ina sallar tawa duk dan akan Allah yabawa heartbeat lafiya, dannalura addu’a kawai yake bukata ahalin yanzu. Tunda duku_duku nakoma part dinmu saboda zanwa su mommy breakfast tun da aka idar da sallar asuba yaya sadiq yakirani yasanarmun. Tare muka koma da baaba talatu danta tayani aikin, munayi muna hira akan ciwon mustapha, duk ni hankalina gabadaya yana gurinsa jinakeyi kamar nayi tsuntsuwa naje nagansa. wajen 8:20 mungama komai munshirya tsaf yaya sadiq yazo yadauka, yauma senaji kamar ince zanbisa amma senakasa fada masa. dole haka nahakura nakoma nayi wanka nashirya na tafi islamiyya batare danaci koda abinciba. Su aliyama kafin 11 sunzo kano itada abbansu da yayanta, direct asibitin suka wuce. Koda akatashi daga islamiyya nadawo gida, senatarar gidan da baki yan dubiya.

uniform kawai nacire mukahau aikin abinci dasu baaba talatu, nikam dauriya kawai nakeyi dan har wani jiri_jiri nakeji da zazzabi, kuma nasan yunwace da damuwa, dan tun jiya babu wani abincin kirki acikina. Tea nahada me kauri nasha sannan nafarajin yar nutsuwa. Muna cikin aikin, su aliya da aunty suka dawo gidan, yau aliya babu bakin surutu idanuntama sunyi luhu_luhu alamun taci kuka ta koshi, aunty cema yau me dauriyar yiwa mutane magana. Duk wanda yazo daga asibiti jiki asanyaye yake dawowa dan jikin mustapha kam sedai addu’a. Hankalina bakaramin kara tashi yakeba idan akayi zancen jikinnasa da yanda yake. kasa karasa aikinma nayi sebarmusu nayi nakoma daki nasha maganin ciwon kai saboda saramundin dayakeyi, kwanciya nayi wani wahalallen bacci yadaukeni. Acan asibiti kuwa mommy tatadawa daddy hankali akan ita sedai akai danta India ba saudiyaba,saboda tasan ciwonsa bana Islamic bane na asibitine. dole daddy badan yasoba yacanza akalar shirin tafiyar daga saudiya zuwa India. nadade ina baccin se bayan la’asar na tashi, bayan nayi sallah nakira yaya sadiq dan yau gabadaya bamuyi wayaba, yanzu kam banyi kasa a gwiwaba nasanar masa inason naje nadubu yaya mustapha yacemun idan yadawo da wuri semuje tare……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button