Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Agurguje

Su Maryam sunje Kano lafiya sundawo lafiya, gwaggo ta tarbesu faran_faran, ammi ta hadata da Mustapha a waya shima yamata yajiki, Maryam hankali ya kwanta taga jikin gwaggo da sauki sosai kuma ta hadu da aminiyarta saleemat da Ummanta… Anshiga wataran Ramadan lafiya, wata me dunbin albarka da sanya farinciki a zukatan kowanne Musulmin kwarai. komai natafiyarwa Maryam yadda yakamata a cikin wannan wata me albarka, saidaifa tsakanin ta da maigidanta babu wani sauyi na mu’amalar auratayya. kwanci tashi babu wuya a gurin Allah yau gashi har ankai azumi 10, yau ne kuma su Maryam zasu fara zana jarrabawar NECO.

Tun ƙarfe 8 tagama shirinta cikin uniform dinta. yayi das ajikinta ya mata kyau sosai. jakarta ta dakko ta dawo falo ta zauna tana jiran mustapha yafito dan shi zekaita da kansa. TV na kunna ina kallon wa’azi kafin yafito. se 8:30 yafito, nikuwa duk na zaku kafin yafito seduba time nake karna makara saboda ƙarfe 9 muke da paper. ina ganin yafito na mike nadauki jakata na rataya, sannan na dubeshi nace. “Ina kwana” be amsamunba sebina dayayi kallo, kasa nayi da kaina ina wasa da zoben azurfan hannuna da yaya Sadiq yabani. Tsawon 2 minutes yana kallonta sannan yace. “Ahala zaki makarantar?” da sauri na dago na kalleshi sannan na fara duban kaina, inason ganin menene beyi daidaiba ajikina ganin babu komai cike da confidence dina nace masa. “Ehh” fuskarsa a hade seriously yace. “Bazaki fita da wadannan kayanba” yana gama fadar haka ya juya ya fice, ya barmun kamshinsa a parlon. binsa nayi da kallo baki buɗe harya fice daga falon. dakina na koma dasauri na tsaya gaban mudumi ina karewa kaina kallo. “To me kayan jikina yayi?” nafurta haka a fili cikin raunin murya. riga da wando ne, uniform din. Rigar har kasan gwiwata kuma bata kamaniba sosai, se hijabi nasu karamine na makarantar, amma ni seda yaya sadam ya kara dinkomun wani medan girma danya rufemun duwawu ta bayana. ganin lokaci naneman kuremun sena fice nabi bayanshi nasan baze wuce part din ammiba. umaimah tana tsaye a bakin kofar falon ammi tana waya da wata kawarta tana bata labarin mustapha da irin sonda take masa. kawartata tace mata. “Kai kawata amma natayaki murna da samun masoyi zabin ranki, amma najifa kincemun shu bemasan kina yiba kuma yanada mata.” Murmushi umaimah tayi tace, “wannan ba matsalata bane kawata, tunda muna gida ɗaya, zanyi ƙoƙarin naga yajanyo hankalinshi gareni, kuma indai dan ta matarshine ai basonta yakeba itama, dan daga dukkan alamu matar cushe cefa, tunda na fuskanci Baya sonta dan baya nuna mata wata kulawa” karaf wannan maganganun da umaimah tayi a kunnen Mustapha dake ƙoƙarin shigowa falon, kofar falon a buɗe take shiyasa yaji. duk dashi bame fuskantar abubuwan mutane bane idan badashi aka kasaba, amma wannan maganar ta umaimah kam yagane dashi da Maryam take, wani muskilin murmushi yasaki yana ayyana wani abu aransa. Ko kallon inda take beyiba daya shiga falon, Umaimah kuwa ganinsa yasa ta katse wayar da sauri tare da faɗin, “yaya NOOR ina kwana” benuna yajitaba balle yajuyo harta saran ze amsa mata. binsa tayi da kallo kamar wata mayya harya shige dakin ammi. Ajiyar zuciya ta sauke wani masifaffen sonsa na kara fisgarta, ta saba dama idan ta masa magana baya kulata indai ba’agaban ammi bane, amma ita hakan baya damunta kokaɗan, dan jikinta yana bata wataran mustapha ze kaunaceta. dakinta ta shige domin tacigaba da wayarta. Ammi ta dubeshi bayan sungama gaisawa tace, “harka kaita makarantar?” Kafin yabata amsa Maryam tashigo da ɗakin da sallamarta cikin ɗari_dari. “Ina kwana ammi” ta fadi haka kanta na ƙasa. Ammi na murmushi tace, “Lafiya kalau ɗiyata ya ibadah” kamar wata munafuka na saci kallonsa sannan nace, “Alhamdulillah” maida kallonta ammi tayi garesa tace, “katashi ku tafi dan takusa latti taran ta kusa” yana wani tsare gida yace, “wai ahaka zata makarantar?” Ammi tace, “kamarya a haka zata?.. meyafaru?” shiru yayi kamar bazeyi maganaba sekuma can yace, “kayan jikinta mana” ammi tace, “A’a mesukayi to? makarantafa zata ba wani gurin ba, uniform ne ai, dole dasu zata ai” bekara cewa komaiba ya mike yayi gaba. daɗine ya lullubeni danda harna tsorata karyace a fasa zuwan. cikin girmamawa nacewa ammi. “Sena dawo” tamun fatan nasara nabi bayanshi da sauri. murmushi ammi tayi, dantagane tsantsar kishine kawai kedamun mustapha. yana gaba ina binshi a baya, seda yarufe part dinmu da key sannan muka tafi. satar kallonsa nayi damuka shiga mota naga ransa abace yake sosai senaji duk babu daɗi. A hankali nace “kayi hakuri dan Allah” banza yamun tamkar bejiba. Arayuwata banason shariya kawai senaji hawaye yacikamun ido, ina ƙoƙarin maidashi amma seda yazubo. kallonta yayi ya tabe baki yacigaba da tukinsa. Har cikin makarantar muka shiga, parking yayi yadubeni bece komaiba, niba bance masa komaiba na bude motar nafita. Binta yayi da kallo harta shige compound din makarantar, lumshe idonsa yayi yatada motar yatafi. Ina shiga natambayi wata daliba inda ake exam din, Tacemun ita canzata inzo muje. se wajen ƙarfe goma aka kawo mana paper’n jarrabawar, bamu fara da wuriba dan haka seda 12 ta wuce muka fito. Tafiya kawai nakeyi ɗan zaman da mukayi harna fara gajiya, gashi bansan a me zankoma gidaba danbecemun zezo yadaukeniba, kuma babu ko sisi a hannuna gashi rana ta kwalle. Ina cikin tafiya kamar a mafarki na hango motarsa fake a bakin gate, wani irin farinciki naji dama rana se dukana take da sauri na karasa wajen motar na bude na shiga, sallama na masa ya amsa ciki_ciki. kwantar da kaina nayi ajikin kujera ina lumshe idona tare da sakin ajiyar zuciya saboda sanyin ac dayafara ratsani gami da shaƙar daddaɗan kamshinsa. seda naji yayi parking alamun munzo gida sannan na bude idona. A hankali nace, “Nagode” be amsamunba se kallona dayayi, kallonsa nayi nima karaf muka haɗa ido, dasauri najanye nawa zuciyata na ɗan bugawa. juyawa nayi na bude murfin motar nafita. shima budewa yayi yafito bayan ya kashe motar. daidai lokacin umaimah tafito zata fita, taci uwar kwalliya a tsakar ranarnan dayake bata azumi yau shine ammi ta aikata. Kawar da kaina nayi daga tana inda take, danzuwa yanzu nagane dalilin dayasa bata kaunata saboda tanason hearbeat ɗina. shiko mustapha ganin umaimah yasashi karasawa kusa da Maryam da sauri ya kama hannunta, yana wani dubanta ƙasa_kasa, duba menuni da zallar kauna ga wanda akewa, yafara magana yanda umaimah zataji cikin taushin murya menuni da zallar kaunah. “Haba hubbynah wayace kiyi tafiya aranarnan sekin wahalarmun da kanki, ga azumi gashi kinsha wuyar school, kijira Ni mana nazo nayi aikina” yakarashe zancen yana wani kannemun ido. Niko mamakinsane ya kasheni,nama kasa motsi se kallonsa kawai nake. kamar bashine yaketa haɗe rai ɗazunba. kafin nayi wani yunkuri naji yadaukeni cak……….✍️

By
zeey kumurya
ABINDA KASHUKA…

         _*BY*_

ZEEY KUMURYA

5️⃣6️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……..Taga_taga umaimah tayi kamar zata fadi saboda tsabar firgici. da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta tsaya da kafafunta, saboda tsabar razani da abunda tagani, wani tukuku taji ya turnike mata zuciya, bayan daukar Maryam da Mustapha yayi harda wani bin fuskarta da kisses, wannan wanne irin mugan gani tayi yau da ranar Allah. wani abu taji yatokare mata a kirji, binsu tayi da kallo kawai harsuga shige cikin gidan kamar wata sakarya. wata tsanar Maryam taji takara cika mata kowanne sashe na zuciya, takasa koda motsi mustapha da Maryam kawai take hangowa a idonta manne da jikin juna. “ita kuma shegiyar yarinyar harda kara wani kwanciya ajikinsa kamar jikin ubanta” umaimah ta fadi haka afili hawaye masu zafi nazubo mata. ita tananan tana haukanta mustapha bason Maryam yakeba, bazatasha wuyar janyo hankalinsa garetaba, ashe ita bata sanina yana son maryam irin haka. kallon da Mustapha yayiwa Maryam shi kadai ma ya isa yatada mata hankali, balle kuma ganinta rungume a jikinsa. Umaimah tayi nadamar fitowar ta a wannan lokacin babu adadi, datasani tun dazu da ammi taketa cemata tatafi aiken tatafi, dabataga wannan abun dayake kokarin tarwatsa mata zuciyaba. son mustapha kullum karuwa yake acikin zuciyarta, mijin datake mafarkin ta aura taki sauraren kowa saboda shi, yau gashi ta haɗu da wanda yafi wanda take tunanin samun ma, amma wata banzar yarinya tana kokarin kawo mata cikas, ta dade a tsaye a gurin tana sake_sake da kyar ta iya jan kafarta tatafi, da ji tayima kamar ta koma ta fasa fitar……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button