Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAYAN SATI D’AYA

 Duk wata alama da zata nuna Maryam tana da shigar ciki ta bayyana, amma ita da Mustapha basu gane ba, kasancewar basu san takan abun ba, bata da aiki yanzu sai kwanciya dan ko a zaune take sai ta dinga jin jiri, ga kwadayin dare data fara, rigima da shagwaba kuwa harda na siyarwa dan yanzu har ammi yi mata take. Mustapha sun koma Kano shida ammi sun dubo jikin Mommy, wadda ke kwance rai a hannun Allah bata masan inda kanta yake ba, ta samu karaya a hannu da kafa duka na dama, sai kuma buguwa da tayi akai da ƙananun ciwuka abun dai babu kyan gani, jikin Sadik ya fara sauƙi tunda yanzu har yana gane inda kansa yake, amma dai duk da haka sai dai a kwantar a tayar. Suhailat sosai ta tada hankalinta a cikin satinnan, bata da aiki sai kuka ko abinci bata iya ci sai Aunty ta tilasta mata take dan watsawa kaɗan, tayi baƙi ta rame duk ta fice daga hayyacinta, kamar ba ita ce wannan uwar gayun ba, to ga ciki gashi tasawa kanta damuwar abunda bazata samu ba, hakan ya haifar mata da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai, Aunty tayi lallamin tayi faɗan amma duk a banza, ƙarshe ta zuba mata ido tace taje ta kashe kanta ita bazata iya ba, tunda ita bata da tawakkali.

Misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na dare, ina kwance akan gadon yaya inacin dabino, shi kuma yana ƙasa yana operating system, isata dabinon yayi na tashi na ajiyeshi akan bedside, sakkowa nayi na zauna a kusa da yaya ina kallon fuskarshi, a hankali ya dago ya zuba mata narkukkun idanunshi, na matsa jikinsa sosai na kwantar da kaina a kafaɗarsa, ya shafi fuskata yace “har kin gama cin dabinon?” Nace “ehh, ya isheni” wuyanta ya taɓa yace “jikinki da zafi fa jewel” na lumshe ido bance komai ba sai ƙara manne masa jiki da nayi, a hankali nace “yaya zanci kaza gashashshiya” yace “kaza kuma a darennan” na ɗan turo baki nace “uhm” ya shafa ɗamamman cikinta yace “baby kin koyi ci da yawa, yanzu duk abubuwan da kika ci baki k’oshi ba?” cikin shagwaba nace “nidai dan Allah yaya kasiyomun” yace “ki bari gobe idan Allah ya kaimu, yanzu kinga aiki nake kuma dare yayi” nace “a’a nidai yaya ina son ci sosai, idan banci ba bazan iya bacci ba” ya sauke numfashi yace “shikenan ɗauko hijabinki muje” na tashi da murnata na saka hijabi muka tafi, da ƙyar muka samu gurin sai da kazar tunda har yau shima ba gama sanin garin yayi ba, guda uku ya siyo mun yace inta ci, tun a Mota na fara ci dan ina ganin kazar yawuna yayi wani irin tsinkewa, baifi rabin ɗaya ba naci naji na k’oshi, adana abata nayi nace da safe zanci, ina gama ci nasha ruwa na kwanta bacci a jikin yaya, cikin dare cikina yace baisan zance ba ya dinga murdamun, tun inajin abun kaɗan_kaɗan har ya farkar dani daga bacci, juyi na shigayi akan gado ina addu’a, wani irin amai naji yana tasomun da gudu na tashi nayi toilet hakan ya farkar da yaya, amai na shiga kelawa, sai da na amayar da kazarnan tass yaya na zuba mun sannu, ya taimakamun na wanke bakina da fuskata ya dawo dani d’aki, shi kuma ya gyara toilet d’in, da nayi aman naji daɗin murdawar cikin harna samu bacci ya kuma ɗaukeni. Sai dai me kafin asuba na tashi aman ya kai sau huɗu, sai da na amayar da duk wani abu da naci kafin na kwanta, duk jikina yayi laushi ga wata kasala gami da jiri da suka lullubeni, Mustapha hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, tausayinta gaba-d’aya ya gama cikashi, gashi sai kuka take masa sannu kawai yake zuba mata kamar shima zai mata kukan, yana jin tamkar ya dawo da ciwon jikinsa, ruwa ya samu ya tofa mata addu’a ya bata tasha, Allah ya taimaka aman ya tsaya ta samu bacci ya ɗauketa da asuba.

Kafin ƙarfe takwas sun gama shirinsu na zuwa asibiti, asibitin su Dr husnah zai kaita yama kirata tace yazo asibitin ya sameta, yau banyi musun zuwa asibitin ba, danni kaɗai nasan me nake ji a jikina, yau ko aikin gida ban iya yi ba, shi yayi komai, ya sakamun hijabina ya kama hannuna muka tafi, part ɗin Ammi muka nufa, tana kitchen suna aiki, zama nayi akan kujera dan bazan juri tsaiwaba, Ammi ta fito jin sallamar su, kallo ɗaya tayiwa Maryam tasan ba lafiya ba, Mustapha ya gaisheta nima na zamo daga kan kujerar na gaisheta, ammi ta amsamun ta ƙara da faɗin “ɗiyata lafiya kike kuwa?” Mustapha ne ya bata amsa da faɗin “bata jin daɗi ne, yanzuma asibiti zamu na shigo na faɗa miki” Ammi cikin tausayawa tace “Ayya, Allah ya ƙara sauƙi, wanne asibitin zaku kuma?” yace “Asibitin su Dr, husnah dannama kirata tace insame ta ƙarfe 8” Ammi tace “kasan asibitinne?” Yace “A’a driver’n kune ze kaimu, aishi ya sani ko?” Ammi tace “ehh yasani sosaima” Mustapha ya duba tsadadden agogon hannunsa yace “zamu wuce 8 ɗin ta kusa” Ammi tace “saikun dawo, Allah yakiyaye” muka amsa da Ameen, na tashi ina taune lips ɗina, Ammi tace “sannu kinji ɗiyata, Allah ya baki lafiya” na amsa cikin sanyin murya tare da ficewa, yaya ya biyo bayana. ya kama hannuna cikin tausayawa yace “sannu baby” na gyada masa kai kawai yace “har yanzu cikin na murda miki?” nace “a’a bakina ne kawai kemun ɗaci, sai jikina da babu kwari” yace “sorry zai dena insha Allah, ko in d’aukeki nace “a’a, zan iya tafiya” muka ƙarasa parking space yana zubamun sannu, bayan ya kira direban ammi muka shiga motar, muka shiga baya nida yaya ina kwance a jikinsa. Ba nisa asibitin sosai cikin wasu yan mintuna muka ƙarasa, kiran Dr husnah Mustapha yayi ta masa kwatancen office dinta, da tambaya suka gane gurin, sai da muka ɗan jirata ta ƙaraso, dan sanda mukaje bata zoba, bayanta muka bi kamar yadda tace har cikin office dinta muka zauna a kujerun gaban table ɗinta. Dr husnah na duban Maryam tace “amarya ya jikinnaki?” kaina a ƙasa na amsa mata, suka gaisa da Mustapha nima na gaisheta, ta dube ni da kyau tace “me yake damun kine ko kuma ince ya kike jin jikinki?” a hankali nace mata “ina jin jikina babu kwari ga jiri dake damuna, sai kuma zazzaɓi kaɗan_kaɗan, jiya kuma harda amai. Mustapha kallon Maryam kawai yake, yadda take faɗar abunda ke damunta amma shi ko sau ɗaya be taɓa sani ba, kullum sai ta dinga lafiyar ƙalau take. Dr husnah yace “yaushe rabon da kiyi period ɗinki” nayi shiru dannama manta da wani abu period, batare da tunanin komai ba nace “tun azumi” Dr husnah tayi murmushi tana duban Mustapha tace “zamu ɗauki jininta da kuma sauran gwaje_gwaje sai mu gano abinda ke damunta.” yace “ok badamuwa.”

Anyiwa Maryam duk abunda ya dace, inda sakamako ya bayyana tana da shigar ciki na sati 8, Mustapha jin abun yayi tamkar a mafarki ya rungume Maryam ɗinsa cikin tsananin farin ciki da murna, yayiwa Allah godiya babu a daɗi, alheri mai yawa ya cika Dr husnah dashi sannan suka dawo gida, suna dawowa gida ya bata abinci taci tana gama ci sai bacci, su ammi duk sun shigo sun dubata. Tattalin Maryam sosai Mustapha yakeyi baya barinta tayi komai na aiki, shi yakeyin komai duk da ita batasan hakan tafiso tayi aikinta amma yaƙi barinta, ko Part ɗin Ammi baya barinta zuwa saboda wai idan taje zata iya yin aiki a can, sai dai inya fita ta samu taje. Yau juma’a wanda ya kama babbar Sallah saura sati ɗaya, yau kuma k’anin Ammi da iyalansa da mahaifiyarsu zasu zo, dama suna Dubai yana harkar kasuwancinsa kusan watansu guda kenan a can, yau kuma zasu iso naija da yardar Allah……..✍️

Allah kanunamun ranar da zan gama book ɗinnan????.

By
zeey kumurya
ABIN DA KA SHUKA….!

8️⃣1️⃣

………Kwance nake a k’irjin yaya nayi shiru ina jin yanda bugun zuciyata yake k’aruwa, tun jiya da daddare gabana yake ta fad’uwa wanda bansan dalilin hakan ba. Shafa kanta Mustapha yayi cikin tsananin tausayinta, jikinta yayi zafi zau alamar zazzaɓi, cikin tsantsar kulawa yace “princess d’ita” na dan d’ago na kalleshi amma bance komai ba, fuskarta tayi fayau ga damuwa ƙarara akan fuskartata, yace “Please tell me, what happened to you?” cikin sanyin murya ina ƙoƙarin b’oye damuwata nace “babu komai yaya, ka yarda dani” yayi shiru kawai yana kallonta, tun jiya yaga yanayinta gabad’aya ya sauya, ga damuwa a tattare da ita, ƴar girimar da take masa ma jiyan batayiba, tambayar duniya ya mata meke damunta ko inane yake mata ciwo amma tace babu, yayi fushi ya kyaleta tasa masa kuka tace ita dai kawai ya tofa mata addu’a, batajin daɗi ne, yau kuma tunda safe data tashi yaji jikinta da zazzaɓi, yace suje asibiti a dubata taƙi, wai ita kar a mata allura. Na shafi gefen fuskarshi ganin yanda yake kallona, ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannunsa ya shafi cikina yace “baby’nmu na wahalar dake ko, sorry” nayi murmushi ganin yanda yayi maganar nace “um, um yaya baya wahalar dani” yace “Allah yasa” na marairaice nace “yaya dan Allah ka barni naje na taya su ammi aiki, ko zanji k’warin jikina” yace “A’a, ki barsu suyi ai suna da yawa, yanzuma kuma sun kusa gamawa, koma ba hakaba keba cikakkiyar lafiya ba inake ina aiki” na turo baki gaba nace “wai yaya ni haka zanta zama bazan dinga aiki ba” yace “a’a amma dai sai baby’nmu yayi k’wari zaki cigaba” nace “haka akeyi dama?” Yace “mu haka zamuyi” nayi shiru ina tunanin wai nice yau da ciki, nice zan haihu nanda wasu watanni, zan zama uwa nima, wata irin soyayyar cikin da kaunarsa ce take ƙara cikamun zuciya. Bayan sallar azhar Dr husnah ta ƙaraso gidan, tun safe mustapha ya kirata akan rashin lafiyar Maryam, tace idan ta taso daga aiki zata biyo ta dubata. Ina d’akin yaya a kwance shi kuma yana falo, ya shigo yana dubana yace “bacci kike ne?” na girgiza masa kai alamar a’a, ya ƙaraso kan gadon ya zauna a baki yana faɗin “ga Doctor nan tazo zata dubaki” na tashi zaune ina kwabe fuska nace “yaya dan Allah kace mata karta mun allura, wlh tanada zafin hannu” ya shafa fuskarta yana murmushi yana tuno darun da’aka sha da ita a asibiti time ɗin da za’a dibi jininta da yi mata allura, cikin kwantar da murya yace “dubaki kawai zatayi ta baki magani” na turo baki gaba nace “nifa lafiyata k’alau” becemun komai ba ya tashi ya fita, two minutes suka dawo ɗakin tare da Dr husnah da sallamarsu, bayan na amsa musu ta dubeni tana murmushi tace “maman biyu, me raki” nayi murmushi kaina a ƙasa nace “ina yini” tace “lafiya ƙalau, ya jiki_jiki?” cike da kunya nace “da sauƙi” ta ƙaraso kan gadon ta buɗe jakar ta ta fara dubani, bayan ta gama ta dubi Mustapha tace “zazzaɓi ke damunta, amma bayan shi babu matsalar komai, yanzu zan rubuta mata magani sai ka siyo mata tasha, tunda batason allura” Mustapha yace “ai gwara ayi mata allurar, dan maganin ma basha zatayiba” na marairaice nace “nidai nafison maganin kuma zansha” yace “shima basha zakiyiba na sani” ya maida dubansa ga Dr husnah yace “kimata allurar kawai” Dr tayi murmushi ta shiga haɗa allurar, na kalli yaya kamar zanyi kuka, ya ɗauke kanshi, bayan tagama haɗa allurar tace “saifa ka riketa” ya tako ya hawo kan gadon ya janyoni jikinsa, na riƙe shi gam dan har na fara jin kamar antsikaramun allurar ajikina, jin hannun Doctor a jikina tana ɗan yin ƙasa da skirt d’in jikina na runtse idona ina ƙara ruk’unk’ume yaya, tana tsikaramun nayi wani zillo hawaye na kwaranyomun, sosai naji zafin allurar gashi dama duk a tsorace nake, yaya ya shiga mulmulamun gurin yana hura mun iska a cikin kunnena, na cizeshi a gefen wuyansa, ya shafa gashin kanta a hankali yace “sorry baby nah” nayi masa shiru ina sauke numfashi tare da ƙara lumshe idona, wani irin bacci na fizgata, cikin abun da baifi 5 minutes ba bacci ya ɗaukeni, Mustapha ya kwantar da ita a hankali jin tayi bacci ya fita falo inda Doctor take jiransa, suka ɗan ƙara tattaunawa akan jikin Maryam ɗin, tace masa babu matsalar komai sannan sukayi sallama ta tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button