Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mommy ce zaune a dakinta ita da daddy da aunty suna tattunawa akan abunda malam yace. “Nifa gaskiya sam banyarda da abunda malaminnan yaceba, kawaidai yazo yafadi abunda yagadamane, amma acikin awanni biyu harya gane sihiri akawa son” cewar mommy tana tabe baki. “Aunty atika kenan, aisu irin wadannan malaman baiwace Allah yabasu, kuma ni nayarda da abunda yace, saboda wlh ciwon Muhammad yayi kama da sihiri, idan kikayi la’akari yanayin ciwonnasa. Duk ciwon dakikaga anrasa gane kansa balle gindinsa, kuma ankasa gano meke damun mutum, tobaya wuce jinnu, kokuma asiri ko mayu” cewar aunty. kara tabe baki mommy tayi tace, “to saudart shiko mustapha, waye zemasa wani asiri, me yaywa wani, shida ko harkar mutane baya shiga” “hmmmm,aunty atika kenan, bar mutum kawai yanda kika gansa,zakiga kina rayuwarki baruwanki da mutum amma shi akwai mugun nufinsa akanki, mudai kawai muyi addu’a Allah yarabamu da sharrin makiya da mahassada” “amin, amma ni banso akayiwa mustapha wani maganin hausaba, dandai kundagene shiyasa na bari, danni gaskiya banyarda da wani ingancinsaba” daddy dayake saurarensu yace, “yanzu duk wannan zancen bashi bane, addu’a kawai itace mafita,kuma mu jarraba amfani da maganin malam din muga abunda Allah zeyi. Ita ko,aunty shiru tayi kawai tana kallon mommy, yanda taga yanzu hankalinta ya kwanta ba kamar farko da mustapha yafara cutaba, duk wannan muguwar damuwar datakeyi akan ciwonnasa yanzu tadena…….

Kamar yadda malam yace adingawa mustapha amfani da magani haka ake masa, kullum babu fashi, yan dubiya kuwa kullum cikin zuwa sukeyi kota ina, duk da ba’a bari aganshi saboda bakin mutane, kowa da abunda zece. yau tsawon sati guda kenan anayiwa mustapha amfani da maganin, yaya sadiq ne yake jigilar shafa masa maganin da diga masa ruwan kodayaushe, amma jikin mustapha tamkar ba’a magani babu abunda yakaru nasauki sema karin ciwo, zuwa yanzu daddy yafara sarewa da ciwon mustapha ganin yakijin magani, mommy kuwa se masifa take tana cewa dama seda tace kar’ayi wani maganin hausa gashi babu abunda yayi sema karin ciwo. Aunty ce take kara tausarsu akan akara gwadawa zuwa nanda sati daya idan beyiba se’acanza wani malamin kokuma a fitar dashi kasar saudiyan kawai.

MARYAM

Har yau bansamu naga mustapha ba duk kuwa da matukar gwadayin ganinsa danake sonyi, yaudai nakasa hakuri seda nacewa yaya sadiq inason ganinsa dan tunda yafara ciwo banganshiba, shine yace dasafe nazo shine agurinsa sena shiga naganshi. da misalin karfe goma na safe bayan nagama aikina nanufi part dinnasa, babu kowa kuwa kamar yadda yaya sadiq yace seshi dayake kula dashi, seda najirashi a falo yagama kimtsashi sannan yafito yace nashiga naganshi. da mamaki na kalli yaya sadiq nace, “yaya nikadai zanshiga bandakai” “haba maryam,kemafa yar gidace kishiga kawai babu matsala zanyi wayane tun dazu ake kirana da ina ciki” gyada masa kai nayi. Ahankali na mike nafara tafiya zuciyata na luguden bugun datasaba aduk lokacin danayi kusanshi dashi. ahankali na murda handle din kofar dakin nashiga da sallama, dukda nasan babu me amsamun. Faduwar gaba da karuwar bugun zuciyatane suka dirarmu alokaci daya sanda nayi arba dashi kwance idanunsa a lumshe. jankafata nayi data faramun nauyi nakarasa gaban gadon ina mai kura masa ido. Jallabiyace ajikinsa wadda babu alamar datti a tattare da ita. “Ya Allah muntuba,Allah ka iya mana” nafada acikin zuciyata ina kara girmama ikon Allah, mutum me kwazo da kasaita,shine acikin wannan yanayin kwance komai sedai a masa,lallai muji tsoron Allah domin duniya abar banzace. Lumshe idona nayi ina tuno yanda yake abaya da lafayarsa amma yanzu gashi a kwance ko hannunsa baze iya dagawaba. ahankali nabude idona nasauke akan kyakkyawar fuskarsa da ita kadaice bata kumburaba ajikinsa. Hawaye ya shiga kwaranyomun a fuskata na tsananin tausayinsa, ga wani gumi dayaketa tsatstsafo masa na azabar ciwo, kawai jinayi nakai hannuna kan goshinsa ina ina share masa gumin kansa batare dana shirya yin hakanba, dukda wani zafi da huci danakeji a tafin hannunnawa amma nakasa cirewa daga goshinsa, sema kara kamasa kandanayi da danyatsuna biyu kamar yadda akeyi idan za’a kamawa me ciwon kai, kai. nafara karanto abunda ake karantawa nakamun kai acikin zuciyata, jikinane kawai yabani yanda kannannasa yake zuba uban gumi yana masa ciwo, seda na kammala karanta duk abunda ake karantawa sannan nasakar masa kannasa. Rankwafowa nayi daidai fuskarsa har ina jiyo hucin numfashinsa a fuskata,lumshe idona nayi,bugun zuciyata kuma ya karu, hannuna na rawa nakaishi daidai bakinsa naraba kananun lips dinsa nasama dana kasa, nafara karanto ayoyin rokiyya a fili yana shigarsa tacikin kunnensa kuma ina tofawa acikin bakinsa, dan idannatsaya debo ruwa nace zantofa aciki zanbatawa kaina lokacine, kuma yaya sadiq yana falo yana jirana. naji abakin aunty ciwon dake damunsa ana tunanin jinnune, duk da tsananin tsoron danakeji akan abunda nake aikatawa,amma haka na daure zuciyata, nacigaba da karanto masa domin wannan shine kadai taimakon dazan iya masa,kuma nasan bazan kara samun wata damar dazan masa irin wannanba………✍️

kuyi manage da wannan

By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

3️⃣3️⃣

……….cikin ikon Allah harna gama karanta masa yaya sadiq bezo kiranaba kuma babu wanda yashigo,abunda ya bani mamaki kenan. Ammafa naji ajikina, dan naji jikina yayi mun wani iri kuma se rawa yakeyi, gabadaya na hada gumi ga wani mahaukacin bugu da zuciyata takemun. ahankali nakai hannuna dake karkarwa na taba goshinsa,senaji zafin jikinnasa ya ragu, se ajiyoyin zuciya naji yana saukewa akai_akai cikin baccinnasa, dauke hannuna nayi daga kannasa nima ina sauke ajiyar zuciyar. badon nasoba bakuma danna gaji da kallonsa naja jiki nafito zuwa falo, abun mamaki babu yaya sadiq babu dalilinsa, zama nayi akan kujera ina maida numfashi hannuna dafe dakaina dayake mugun saramun,wani irin shauki da kaunar yaya mustapha ne, yake kara ninkuwa araina gami da tsananin tausayinsa,daga gani base anfadaba kasan yana jin jiki,dakuma azabar ciwo, dama dazan iya dana maido da ciwonnasa jikina, wasu guntayen hawayene suka silalomun wanda bansan dalilinsuba,tabbas idan Allah yabaka lafiya yagama maka komai najin dadin rayuwa. nakai ten minutes azaune ina jiran yaya sadiq amma naji shiru bedawoba, mikewa nayi zanje naduba falon kasa koyacan, a kan steps mukacikaro da mommy,datake hawowa benen cikin sauri har bangazata tayi, bayanayi dasauri harna kusa faduwa dama jikina babu kwari sekuma narike karfen benen. “Maryam!” naji mommy takira sunana da alamun mamaki. Gabanane yayanke yafadi danbansan me mommy zatamunba intaga nikadaice agurin danta. “Na’am” na’amsa mata cikin rawar murya. “Mekike anan” cikin dauriyar abunda nakeji ajikina nace mata, “mommy nazo duba yayane, shine yaya sadiq yace injirashi zeje yadawo, kuma haryanzu bedawoba” mommy batakaramun magana sebina datayi da kallo, kasa nayi da kaina cikin faduwar gaba. “Yanzu sadiq son din yabarmun shikadai shikuma yakama gabansa” mommy ta fadi haka cike da bacin rai” batajira mezanceba ta raba tagefena tahaye saman. wata nannauyar ajiyar zuciya nasauke ina bin bayanta da kallo, “yanzu da’ace ina dakin mommy tazo tasameni mezance inayiwa danta,nagodewa Allah daseda nafito ita kuma tazo. Karasa sauka nayi nafice daga part din,banga yaya sadiq ba harna karasa part dinmu. Dakina nashige na kwanta akan gado,kaina na juyamun,addu’a nashiga karantowa acikin zuciyata har baccin wahala yadaukeni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button