Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

1️⃣4️⃣

………..Da sauri na saki cup din dake hannuna bayan yacikamun hannun, cup din ya fadi kasa ya tarwatse cikin tsananin tsorata na mike tsaye, shima mikewar yayi da sauri saboda kar lemon yabatasa. Wani mugun kallo aunty suhailat take bina dashi, cikin tsana dajin haushi. Tana karasowa gabanmu ta daga hannu da nufin ta kwadamun mari, runtse idona nayi cikin tsammanin jin saukar mari, amma har wasu sakanni suka wuce banjiba. Ahankali na bude idona, senaga Ashe bakonnatane ya rike hannunnata yana girgiza mata, kai.cikin tsananin bacin rai ta fara magana. “Haba kamal yazaka hanani hukunta wannan matsiyaciyar yarinyar, baka ganin abunda tayine, sekace mahaukaciya zata wani sakar maka cup, idan da yabata maka jikinkafa” ta karasa maganar cikin karaji da daga murya. “look baby, ai itama tsautasayine batasan hakan zata faruba, haba bakiga yarinya bace kidena mata magana haka mana” wani kallo ta watsama masa batace komaiba, Nidai ajiyar zuciya kawai nake saukewa, cikin hanzari na nufi kofar fita, saboda ganin yana kokarin janyota jikinsa. Zama kamal yayi yadora suhailat akan cinyarsa, yace. “Haba baby bagirmanki bane kidinga daga murya akan abunda bekaiyakawoba.” “Hmm, bazakaganebane kamal natsani yarinyarnan over, haushinta nakeji” murmushi kamal yayi aransa yace, “dole kitsaneta mata tunda tafiki komai da komai.” Amma a fili seyashiga lallashinta yana tattabeta…….

Da sauri nake tafiya tamkar zantashi sama, tsayawa nayi abakin kofar falo ina daidaita nutsuwata. Ahankali na bude kofar falon na shiga, mommy ce kadai zaune a falon. Sallama na mata kawai na shige dakina. kan gado na fada ina maida numfashi tunanika kala_kala araina, ga haushin wannan dan akuyar yacikamun zuciya,haka kawai ze rikemun hannu wlh, Allah ya isana. Arayuwata na tsani namiji dan iska. Agefe guda kuma ina mamakin aunty suhailat,yanda take mu’amala da dan iska, haryana tabata. Mtss naja tsaki a fili cikin takaici,nakawar da tunaninsu daga araina. Mikewa nayi na dakko rigar oga dankarna manta,nakara wani lefin dannaga ya kulu akan rigarnan. Tasss na wanke masa ita a toilet dina, natisa wankinta yakai sau biyar, sedanaga tayi kal sannan na barta. A toilet din nashanya masa.Alwalar sallar la’asar na dauro na fito, dan anyi sallar tun dazu.

Bayan na idar da sallar nafito domin zuwa part din su baaba talatu. Mommy nagani zaune afalo, da suhailat da bakonta. Bata fuska nayi sosai sabida kallon gefen idon dayake bina dashi. Aunty suhailat kuwa se uwar harara take zabgamun, kusa da mommy na durkusa nace, “mommy zanje gurin baaba talatu” kallona tayi na wasu sakanni, batacemun komaiba,harnayi tunanin bazata barniba senaji tace, “ki dauki lemon kwakwa a kitchen zaki ganshi na zuba a jug,kikaiwa my son,seki wuce daganan” “toh mommy nagode.” Na’amsa mata cikin ladabi. Kitchen din nashige na dauka, zuciyata nadan bugawa nanufi part dinnasa, harga Allah tsoron bawan Allah nan nake,tsoroma kuwa bana wasaba. A falon kasa na tarar dashi yanada aiki a system dinsa,yacanza kaya zuwa kanana. Sannu namasa, batare daya dagoba ya amsamun dakai, harzankai lemon kan dinning, sekuma naga dacewar na ajiye masa agabansa, akan center table din gabansa na ajiye masa, ina satar kallonsa. Harna juya zantafi yatsaidani da fadin, “exucuse me pls” juyowa nayi ina kallonsa, da hannunsa yanunamun wata kofa a falon yana fadin, “help me with cup” “ohk sir” na’amsa masa cikin ladabi. Kofar dayanunamun na nufa na bude, kitchen din hadadden shima, bantsaya wani kare masa kalloba na nufi inda naga kofinan, seda na daurayesu sannan na kawomasa na fice daga part din.

Ajiyar zuciya nasauke ganin yanzu mun rabu lafiya, part din da baaba talatu ta kwatantamun naje, karamin part ne, yana dauke da babban falo da se dakuna. Gasu salame nan zaune da sauran ‘yan aiki, kowa yana sabgar gabansa gaishesu nayi na tambayesu baaba talatu,wani daki suka nunamun godiya na musu nashiga da sallama. Baaba talatu zaune take akan dadduma tana lazimi, zama nayi agefen katifar dake dakin ina jiran ta karasa. “Maryama, ashedai zakizo Aida nayi tunanin bazakizoba” baaba talatu tafada bayan kammala laziminta. “tun dazu nakeson zuwa baaba sekuma nayi wani aiki danagama kuma bacci yadaukeni” “ayya sannunki, aikina da kokari ya aikin,kinadai jin dadinsa” “eh baaba, ai aikinma babu yawa nariga nasaba fiye da haka agida.” Gyara zama nayi sosai nace “baaba talatu, dan Allah kikaramun Karin haske akan abunda kikafadamun wlh kullum cikin zullumi nake, da tsoro acikin gidannan” “maryama ki kwantar da hankalinki insha Allah, babu abunda ze faru dake, kedai kawai kidage da addu’a kuma kiyi takatsantsan da kowa na gidannan.” Numfashi nasauke nace, “to baaba talatu kincemun lokacin da’akeyin wannan mummunan abun duka yaran gidan basanan towa kike zargi kenan?” “Bawai ina nufin dukansu basananbane kawata_kwata, a’a,lokacin daza’ayi idan wannan yananan to wannan bayanan, zakiga wani lokacin da’akayi mutum ukun sunanan kokuma hudu kokuma biyu,inafatan kingane.” Jinjina kai nayi nace, “eh nagane baaba amma ni abunda yafi tsoratar dani dakikace duk wadda akayiwa fyaden mutuwa takeyi” “Eh to gaskiya kuskuren danayi kenan dana fada miki haka, saboda bansan na sauranba,ammadai tabbas na jikata hakance ta kasance.” “To shi megidan baaba meyasa bazedau matakiba, kodan gudan bacin sunansa a idon jama’a, musamman dayakasance ana fadar alkhairinsa sosai agarinnan” “bansaniba gaskiya maryam, domin tabbas alh mutumin kirkine” ajiyar zuciya nasauke, nidai har ga Allah zaman gidannan a tsorace nakeyinsa. “Amma baaba da lefin hajiyama, kuma ni tana aikena part din danta ko tunanin wani Abu yafaru batayi. Murmusawa tayi tace, ” Aishi wannan gaskiya bana zarginsa saboda kafinma kiganshi a part din hajiya ana jimawa, kuma wannan abunda akeyi adakin masu aikin akeyi harnan akebinsu, shikuwa daga gurin aiki se part dinsa,befiya zuwa nanba gaskiya,amma ai bata aikenkipart din sauran yarannata?” “Ehh,baaba bata aikena.” “Yawwa” Munsha hira da baaba talatu sosai, takuma kwantarmun da hankali, Allah yanaji yana gani, kuma baya barci shize kareni,babu wayo ko dabarata. Seda nayi sallar magriba nabar part dinnasu, har kofar part din hajiya ta rakoni. Tambayarta nayi akan zan iya tambayar hajiya zuwa ganin gida, tatabbatarmun dazan iya kuma hajiya zata barni.

Babu kowa a falo yanzu, dakina nashige, rigar yaya dana wanke nadakko harta bushe, dama bata dawani nauyi. Tunda nazo gidan naga iron sabo adakina, bantaba guga dashiba seyau nace bara nagoge masa rigar. Jonawa nayi nafara gogewa, ina gugar ina tunanin maganarmu da baaba talatu, ban’ankaraba tsautsayi ya afkamun iron din yakwashe wani guri agaban rigar kuma dayawa ya kwashe. Wani gumine yafara tsatstsafomun duk da a.c da fankar dake dakin, “nashiga uku ni maryam, meyakaini goge rigarnan, tsautsayi ko karambani yanzu gashi na kona masa, nasan idan yaji lefin dana aikata masa sedai wata baniba” wata hautsinawa cikina yayi, matsanancin tsorone ya lullubeni. Ninke rigar nayi cikin rashin sanin mafita, addu’a nakeyi araina Allah yasaukakamun duk hukuncin dazemun. Adaren yau kam abincima kadan natsakura naci, saboda zullumi. Inayin serving dinsu na kwanta dama nayi sallah ta, addu’a nashigayi araina ga tsoron zaman gidannan ga tsoron gamuwata da oga kwata_kwata,baccinakam adaren ragaggene, dandaima baccin barawone,bansan sanda yasaceniba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button