Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Azumi uku kawai nasha nadora aka cigaba dani. cikin kwanakin da suke shude gaba-daya wasan buya nake dashi saboda kunyarsa danake ji. bana fitowa falo sena tabbatar ya fita, kafin ya dawo kuma zan gama komai na gudu part din ammi, idan yazo kiranane kawai muke haɗuwa. yau idan munkai azumi 29 ana saka ran gobe sallah, tun safe masu kitso da jan kunshi suka zo har gida suka mana. Kananun kitso nace amun, aiko nasha zama dan munfi awa biyu a zaune. gashi andauramun lalle a ƙafata. Umaimah se hararar Maryam take cikin hassada da kyashin ganin yawan gashin maryam ɗin, ita tana fama da kanta kamar me, dan bata da gashi kokaɗan, kitsonma dana na ƙari tace ayi mata ammi ta hana. har bayan azhar ina zaune, seda aka cire lallen na samu sa’ida. Zanen lallen yayi kyau sosai a farar ƙafata, gashi lallen ya kama sosai. Bayan ansha ruwa ina kwance a falonmu a ƙasa kan carpet, jikina duk a gajiye saboda aikin da mukasha yau, sanin danayi baya dawowa se bayan sallar isha’i shiyasama nazo falon na kwanta. labarai nake kallo, saboda inji koza’ace anga wata. banji buɗewar kofarsaba, balle shigowarsa se kamshin turarensa kawai naji. kallo bakin ƙofar nayi, da sauri na tashi zaune ganinshi ina amsa sallamar yayi gabana na faɗuwa, binsa nayi da kallo ta ƙasan ido, maimakon naga ya nufi dakinshi senaga ya karaso cikin falon ya nemi guri ya zauna akan 2 seater batare daya kalli inda nakeba. “Sannu da zuwa” na furta haka cikin sanyin murya kaina na ƙasa. kamar bejiba ko motsawa beyiba da sunan amsamun sema cigaba da danna wayarsa dayayi. kusan 3 minutes sannan naji yace, “yawwa” a can ƙasan makoshi kamar wanda akawa dole, batare daya dagoba. kamar na shareshi nima amma dai na daure na ƙara ce masa, “ga abincinka can akan dinning” girgiza kai yayi srioustly yace, “banacin abincin kazamai” waro idona nayi duka waje ina kallonsa, araina nace. “Kazama kuma? nice kazamar kenan yake nufi, to menayi na kazantar?” bakina na turo gaba tare bata fuskata kamar zanyi kuka nace. ” Aini ba kazamabace?” banza yamun kamar bejiba. idona nane ya duri ruwa, naji babu daɗi sosai dayacemun kazama, gashi ina masa magana yana shareni. bansan sanda hawaye ya zubomun ba, duk da kokarin da nayi dan kar hakan ya faru. A hankali ya dago kansa ya kalleta. mamakine ya cika masa zuciya ganin tana hawaye. “To me aka mata?” Ya tambayi kansa. kallonta kawai ya tsaya yanayi yanda hawaye yaketa zuba daga idonta, kamar wadda aka daka. lumshe idonsa yayi yana fesar da numfashi. A hankali ya mike ya sauka ƙasan kujera, daf da ita ya zauna yana jifanta da wani kallo dashi kansha besan yanayiba. tafin hannunta yakama a hankali, wanda hakan yasasu jin sauyi gaba-daya ajikinsu. lallen da aka mata yakurawa ldo, kunshin ya burgeshi sosai. zamansa akusa dani yasa bugun zuciyata sauyawa, wani yarrrr naji a jikina lokacin daya kama hannuna. daurewa kawai nayi na lumshe ido. a hankali ya kai hannunsa ya fara share mata hawayen fuskarta dan yanzu yagane meyasa ta kukan. bakinsa yakai saitin kunnena cikin wani irin amon murya me narkar da zuciya yace, “what are you crying?” Batare dana buɗe idonaba na nuna shi da hannuna tsigar jikina na tashi. murmushi yayi ya kwantar da kanta akan kafadarshi. ajiyar zuciya na sauke me ƙarfi, ina ƙara lafewa ajikinsa. sosai nake tsintar kaina a wani irin yanayi a duk lokacin dana jini ajikinsa, yanayine me wuyar fassaruwa amma yanamun daɗi sosai, ina jin tamkar na dawwama ajikinnasa. kitson da aka mata ya shafa yace, “shine baki nunamun kitson sallar da lallenba ko?” cikin shagwaba nace, “bakaine kacemun kazama ba” bakinta data turo gaba ya shafa da finger dinsa yace, “bakazamar bace” kamar zan fashe da kuka nace, “Allah Ni ba kazama bace” wannan karon murde bakin yayi ganin ta ƙara turoshi gaba yace, “wacce kikamun ajikinafa” shiru nayi ina ƙara runtse idona cikin jin kunya. se yanzu nagane meyasa yacemun kazama. hannunsa yakai ya fara shafa cikina slowly, yace. “Ya jikinnaki” “na warke” na faɗa a wani irin baƙon yanayi saboda shafa cikina dayake. lips dinsa ya lasa tare da sauke numfashi ya cire hannunsa daga jikinta. raba kanta yayi da kafadarsa yana faɗin, “dagani Ni karkimun bacci a jiki” badan nasoba na bar jikinnasa. wayarsa dake gefensa ya dakko ya fara latsawa, mikomun yayi yana faɗin. “Take it” karbar nayi cikin rashin fahimta. Ganin bata ganeba yace, “Antinki keson magana dake” fadada fara’a ta nayi akan fuskata cikin jin daɗi na ƙara wayar a kunnena ina faɗin “Salamu alaikum” jin antin ta ɗaga. “Wa’alaikumussalam, Maryam ya gida.” nace “lafiya kalau, Aunty nah, ya kowa da kowa” “lafiya kalau suke, ya ibadah” “Alhamdulillah Aunty, yaushe zakizo nayi missing dinki sosai” “munanan tafe tafe cikin sallah insha Allah” murmushi nayi nace, “Allah ya kaimu lafiya, ina aliya” Aliya dake gefen Aunty tana jiran ta bata wayar tace, “ganinan matar yaya, tun dazu nake mata alama ta bani wayar taƙi bani” dungura mata wayar Aunty tayi. Dariya nayi nace, “Aliya kina jin azuminnan kuwa, naji muryarki radau da karadinta” aliya tace, “hmmm idan ana sallah ba’a magana mairo, wlh azuminnan ya garani, Allah ya karba kawai. “Ameen ya Allah, ya skull?” “Skul Alhamdulillah munma yi hutu” hira muka shigayi da Aliya, aiko Aliya ta dage tanata zuba. Mustapha daya kurawa Maryam ido yana kallonta yanda take motsa ɗan karamin lips dinta bakaramin daukar hankalinsa yayiba. kawai jinayi ya kwace wayar. kallonsa nayi cikin mamaki, a hankali nace. “Meyasa ka kwace? bamu gama hirarmubafa” yana danna wayarsa yace, “kunsamu kati ne?” girgiza kai nayi alamar A’a. ina dubansa kamar zanyi kuka. dagowa yayi yamun kallon cikin ido, da sauri na lumshe idona dan bazan juri kallon kwayar idonshiba. numfashi ya sauke a hankali ya mike tsaye. bude idona nayi na sauke akansa a hankali ganin ya nufi kofa nace. “Fita zakayi?” juyowa yayi ya kalleni ya gyadamun kai. “Zan bika” na faɗa cikin sanyin murya, batare danasan sanda maganar ta fitoba. “Masallaci zani” ya fadi haka yana ficewa daga falon. murmushi nayi bayan ya fita, zuciyata cike da tsananin farinciki ganin ya fara sakemun yanzu, ba kamar farkon aurenmu ba. Mikewa nayi nima na shiga daki jin anfara kiran sallah, zuciyata cike da nishadi. ina idar da Sallah na yafa mayafin abayar dake jikina nanufi part din ammi.
Suna zaune Dukansu matan gidan kowacce tana duba ɗinkin da tela yakawo ɗazu. da sallama nashiga. suka amsamun dukansu cikin fara’a, amma banda umaimah data haɗe rai tacigaba da duba kayanta. guri na samu na zauna ina gaishesu. Ammi ta dubeni tace, “Maryam kayanki suna dakina ki shiga dauko” cikin girmamawa nace “toh ammi, idan zan wuce zan dauka. Angode Allah yasaka da Alkhairi, yajikan mahaifa. murmusawa Ammi tayi cikin jin daɗin addu’ar Maryam tace, “Ameen ɗiyata, ina NOOR ne tun safe ban ƙara ganinshiba” ina ɗaukar Abul dake kwance a ƙasa ganin ya fara kuka nace, “dazu kuma ya fita Masallaci” tabe baki umaimah tayi cikin jin haushin Maryam, kayanta ta kwasa bayan taja tsaki ƙasa_kasa tayi dakinta. Mama da mama A’isha ma, nasu suka dauka suka fita. Aunty zuhura ta karbi Abul ta bashi nono. Bayan yagama sha na ƙara karbarsa ina masa wasa yanata bingiramun dariya. yaya sadam da mustapha ne suka shigo falon. Umaimah da fitowarta kenan daga ɗaki tace, “yaya NOOR sannu da zuwa” tana karashe maganar tana wani fari da ido. beko kalletaba ya zauna a gefen Maryam bayan sun gaisa dasu ammi, kamarma bejitaba. kallonsa nayi ya harareni ɗauke kaina nayi daga kansa nacigaba dayiwa Abul daketa bingiramun dariya wasa. kaina babu ɗankwali bansan jelar kitsona tafito ta gefen wuyanaba seda naji Abul ya riƙe mun. A Hankali nake ƙoƙarin kwacewa daga hannunsa dan kar yayi kuka, shikuma ya rikte gam yaƙi saki. Mustapha dake kallon Maryam ta gefen ido yana ganin abunda ke faruwa, murmushi yayi ganin Maryam se yatsina fuska takeyi. hannunsa ya zira ta bayanta ya zagayo dashi ya cire gashin maryam daga hannun Abul cikin dabara. Ɗaukar Abul ɗin yayi yana faɗin. “Seka cire mana gashin saboda mamanka umaimah bata dashi ko?”…✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button