Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina cikin aikina naji fitinannen kamshinsa ya mamayemun hancina, nandanan naji zuciyata ta hau luguden bugu Wanda narasa na menene aduk lokacin damukayi kusanci dashi senaji hakan a tattare dani,lekawa nayi ta window ina kallonsa,yana sanye cikin manyan kaya yanzu sabanin sanda na baroshi kananane,kayan sun matukar yimasa kyau,amma ba hula akansa, dakin mahaifiyarsa ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke na dawo na cigaba da aikina,araina ina tunanin tome yahanasa zuwa gurin aiki,kodai haryaje ya dawone? Babu amsa,wata zuciyar ta fadamun hakan. Se kusan karfe 2,nagama aikin drinks din saboda nayishi da yawa ko wanima zesha. A fridge nasakasu duka. Bayan na zubawa emeka nasa, ai kuwa nasha santi a gurinsa. Nidai dariya kawai natayi masa.

Daki na koma saboda inatajiran wadanda aunty suhailat tace,zamuyi aiki tare amma shiru_shiru basu zoba,ashe ni bansaniba a part dinsu sukayi aikin,dama kayan snacks ne,sukayi mata. Wanka nayi tare da dauro alwala nayi sallah. kwanciya nayi da nufin nadan huta. banmasan sanda bacci ya daukeniba…..

Tunda ta fice daga falon ya bita da kallo ta gefen ido,besan sanda murmushi ya subce masaba saboda yanda takeyin komai nata a tsorace,kuma da yarinta. Kadan ya taba breakfast din ya mike ya koma dakinsa,fasa zuwa office dinma yayi gaba daya saboda lokaci ya kure,gashi yau Friday, 12 yake baro office saboda masallacin juma’a. Aiki yayi a laptop dinsa,sannan ya mike yayi wanka yayi shirin zuwa masallaci. Seya fara zuwa ya gaida mommy sannan zewuce masallacin. Lokacin dayashiga part din mommy,yana kallonta ta gefen ido tana lekensa ta window, wani murmushi yayi Wanda shikadai yasan ma’anarsa,ya shige dakin mahaifiyarsa…….

Suhailat se da 2 ta wuce,ta dawo gida. A matukar gajiye ta dawo dama ita langwaice batason aikin wahala,zaman lectures ma wahala ne agurinta. wanka tayi ta shirya cikin wani hadadden Dubai less.dinkin Riga da skirt ne,yamata dass a jikinta. Ta kafa daurinta tayi kyau sosai,tamkar ka saceta. Suhailat irin matannanne dakana ganinsu zakaga tsantsar kyawunsu. Taci turaruka kala_kala setashin kamshi takeyi. Waya sukayi da kamal yasanar mata yana kan hanya. Abinci taci kadan kafin yakaraso. Amma zuciyartarfa cike take da tsoron yayanta. A kan zuwan kamal Tasan dai idan tace masa abokin karatuntane,ze yarda. Dakin mommy ta nufa tasanar mata kamal yanakan hanya. Mommy macece me son ra’ayin yayanta dabin abunda sukeso. Hakan yasa batayi yunkurin hana kamal zuwaba, koda yakema hakan bakomai bane agurinsu,dan abokin yarka yakawo mata ziyara gida.kuma tayarda da abunda suhailat tace mata akan,kamal abokin karatuntane…..

Kamal shikadai yazo gidan su suhailat,kuma wannan shine zuwansa na farko gidan. Bin gidan yakeyi da kallo yana jinjina yanda aka kashewa gidan kudi, tabbas dolene, yabi shawarar abokinsa, yasan yanda yayi ya auri suhailat kodan yaci kudin babanta. Sema yanzu dayazo gidannasu,yakara jin kwadayin aurannata. Murmushi yayi yana kissima abubuwa da yawa aransa,kafin yafara Neman auran suhailat dolene yafara kawar da almustapha sulaiman menasara daga doron duniya,domin idan har yana raye suhailat baza tataba auransaba. Yadade da sanin tarihin soyayyar mustapha azuciyar suhailat, wani murmushin yakara saki,akaro na biyu……..

Tarba sosai kamal yasamu daga gurin suhailat,babban falon bakin daddy suhailat ta kaishi bayan ta taryoshi da kanta.

Ina cikin baccina naji andakamun duka abaya,da sauri na bude idona saboda dukan ya shigeni. Tozali nayi da aunty suhailat dataketa zabgamun uwar harara. “Sannu hamshakiya kinzo kin kwanta kina bacci,ina abunda nace miki kihadamun?.” “Kiyi hakuri aunty suhailat banmasan baccin yadaukeniba,nahada miki drinks din yana fridge.” Wani banzan kallo ta jefeni dashi,tace, “to kina nufin dakaina zan dakko drinks din nakaimasa koyaya?.” Sakkowa nayi daga kan gadon ina girgizamata kai,hijabina na dauka nasaka nabi bayanta zuwa kitchen. Acikin wasu hadaddun jug na zuzzuba masa drinks din. Bayan su salame tace nabi zuwa inda ta saukeshi,sukuma suna dauke da kayan abincine zasu kaimasa,suna gaba ina binsu abaya. Da nisa gaskiya daga part dinmu zuwa part din da’aka saukeshi. Nidai har yanzu mamakin girman gidannan nake, gida kamar unguwa,gashi part part din gidan yayi yawa. Kamal yana zaune yana latsa wayarsa suka shiga suka ajiye masa kayan abincin,nice ta karshen shiga. araina nace,ji uban kayan da’aka shiryamasa shikadai, kuma idan yatashidai kadan zeci iya cikinsa. wani talakan kuwa yanacan abunda zecima bashi dashi.Tunda na shiga naga yadago ya kuramun ido, yana kallona. Tsaki naja kasa_kasa domin ni natsani kallo arayuwata. Gaishesa nayi ina ajiye masa kayan akan center table din gabansa, amsawa yayi yana bina da wani mayen kallo. Harna juya zanfita yatsayar dani da fadin, “Yan mata baki karasa ladankiba,baki zubamun drinks dinba.” Dawowa nayi zan zuba masa, amma bance komaiba, Karamin Kofi nadauka nafara tsiyaya masa,raina yafara baci da kallon dayake bina dashi,duk nabi na tsargu. Shiko kamal se lasar lips dinsa yake tundaga ta shigo falon yaganta yajita masa,aransa yanacewa ina suhailat ta samo wannan yarinyar kyakkyawa, danya shakaf da ita,duk da acikin hijabi take amma daga gani tana da manyan kayan aiki. Yanzu kuwa data tsugunna seya kurawa fuskarta ido,yana ganin yanda taturo dan karamin pink lips dinta gaba, aijiyayi tamkar ya janyota jikinsa ya tsotseshi,daga gani zeyi taushi da dadi. Tundazu nake mika masa cup din,bayan na tsiyaya masa lemon kwakwar amma naji yaki karba,dago kaina nayi dannaga meyahanashi karba,senaga kallona kawai yakeyi sekace ze cinyeni. Kara bata rai nayi nace, “Karbi” adakile nayi maganar. Kamar Wanda ya firgita ya miko hannu da niyyar karba, kawai jinayi ya hada da hannuna ya damke da cup din. Kokarin kwace hannuna nayi amma yaki sakarmun se wani murmushi yake jifana dashi. Kawai jinayi kwalla ta cikamun idona,saboda bakin ciki da takaici,na bude baki zanyi magana aunty suhailat ta shigo falon…………..✍️

Kuyi hakurifa 2 days kunjini shiru,nayi busy ne.amma yanzu komai ya daidaita zaku dinga jina yanda yakamata insha Allah

BY
zeey kumurya

https://chat.whatsapp.com/Fjc94fL7wBLAM29Wl7L1FB
Masu bina p.c, in’sasu a group din abunda kashuka….yacikane. Amma ga sabonan na bude sekuyi joining. Amma dan Allah,dan girmansa badanniba banda maza mata zallah, kuma idan kinsan ba comment zakiyiba karkishigomun,idan kina group din REAL ZEEY KUMURYA KO ABUNDA KASHUKA..1 shima karki shiga pls and pls.????????

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

BANI DA BAKIN GODIYA, A GAREKU MASOYANA,SABODA YANDA KUKA NUNAMUN KAUNAR BOOK DINNAN,ALLAH YABAR KAUNA A TSAKANINMU ME DOREWA,ALKHAIRIN ALLAH YAKAIMUKU A DUK INDA KUKE,A FADIN DUNIYA????????.KAMAR YADDA NA MUKU ALKAWARI FARKON WATANNAN ZANCIGABA,GASHINAN NA CIKA ALKAWARINA, SEDAIFA BA KULLUM ZAKU DINGA JINABA.????

TUKWICI AGAREKI AUNTY ZAINAB ALIYU JIGAWA, NAGODE DA KAUNARKI DA KULAWARKI AGARENI,ALLAH YA BARMU TARE HAR’ABADA????

THIS PAGE IS FOR YOU,UMMUL AMINA,KIYI YANDA KIKESO DASHI????

Bismillahirrahmanirrahim

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button