Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mommy ganin har wajen 10 son dinta bezo yagaishetaba setaji hankalinta yakasa kwanciya, shida yake zuwa gaisheta tun bayan sallar asuba amma yau haryanxu shiru, gashi tanata kiran wayarsa no respond,gashi maryam yau bata kawo mata key din part dinshiba,ita kuma tamanta bata tambayetaba. Yanke shawara kawai tayi gwara taje taduba taga ko lafiya yake. wayarta kawai ta dauka ta nufi part dinnashi,tanata addu’ar Allah yasa lafiya yake, dantasan bakaramin abune zehanashi fitaba. Kamar yadda maryam tabarshi haka mommy taje tasamesa, a kwance tamkar gawa. Cikin sauri mommy takarasa kan gadon dayake, tana kiran sunansa,cikin dan daga murya. “Son,son,son” amma taji shiru,zare bargon daya lulluba dashi tayi, ganin yanda yake hada uban gumi, wani irin huci mom taji yana tashi saga jikinsa, numfashinsa na fita da sauri da sauri. Cikin tsananin firgita da yanayin data ganshi takai hannu, tataba goshinsa. Dasauri tajanye hannunta saboda zafin dataji kannasa yayi, tamkar anzuba masa garwashi,gashi babu inda yake motsi ajikinsa, numfashin dayake fitarwane kawai zesa kagane yanada rai,abunda ya kara firgita Mommy kenan. Cikin tsananin gigita dayanayin da mommy taganshi, ta kwalla kara tahau jijjigashi tana kiran sunansa da karfi,tana fadin. “My son, meke damunka haka, pls d katashi dan Allah! Son,son!” dasauri kuma ta mike tamkar wadda aka tsiraka tafice da gudu daga part din cikin tsananin tashin hankali, farfajiyar gidan tanufa tana kiran ma’aikatan gidan akan suzo dasauri su taimakamata takai mustapha asibiti. Wani daga cikin ma’aikatan gidan me suna Adam, shiyafara zuwa. “Hajiya lafiya kuwa, meke faruwa?” Yatambayi mommy cikin mamaki saboda betaba ganinta a irin wannan yanayinaba. “Inafa lafiya Adam, nazo nasami son dina cikin mawuyacin hali na rashin lafiya,kutaimakamun nakaishi asibiti karya mutu narasashi” mom takarasa zancen cikin tsananin damuwa tamkar zata fashe da kuka. “subhanallah muje hajiya,muje, muje” juyawa mommy tayi cikin sauri da tsananin tashin hankali cikin part dinnasa,Adam na biye da ita abaya. wasu ma’aikatan dasuka karaso gurin yanzu suma suka rufa musu baya cikin sauri,ganin alamun babu lafiya……….✍️

kutayani da addu’a,Allah yasa nasamu nasara akan abunda nasa gaba pls????????

BY
zeey kumurya

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

2️⃣9️⃣

………Hankali atashe mommy take nunamusu mustapha,dake kwance yanda ta barshi bayan sun isa har cikin dakinsa, babu bata lokaci suka nufeshi suka cuccuboshi kamar yadda mommy tace, suka fito dashi zuwa mota. Mommy da jikinta keta rawa saboda tsabar firgici, ta dauki wayarta data ajiye agefen gadon tun shigowarta dakin, tafara Neman number daddy domin kiransa tasanar masa halin da’ake ciki,sannan itama tabi bayansu adam da sauri. Tana tafe tana kiransa amma bedagaba harta katse, cigaba tayi da kiransa amma harta shiga mota bedagaba,driver nagaba, mommy kuma tana zaune akan kujerar mezaman banza, se mustapha da’aka kwantar abayan kujera. Cikin sauri driver yafigi motar, mommy kam gabadaya baya tajuya tana kallon mustapha,gani takeyi tamkar kafin wani lokaci kankani ze iya mutuwa, basuyi nisa da tafiyarba wayarta ta fara kara. Jikinta narawa ta dakko tadaga da sauri ganin daddy ne, sallama daddy yayiwa mommy, batare data amsa masaba, cikin tsananin rudu tace, “alhaji, my son naje natarar kwance a part dinsa babu lafiya, kuma babu Inda yake motsi ajikinsa senumfashinsa dake fita kadan_kadan,yanzuma munakan hanya zamu kaisa asibiti.” Takarashe zancen da fashewa da kuka. Abangaren daddy cikin kidima yace, “Subhanallah, dama bashi da lafiyane” cikin shashsheka mommy tace, “lafiyarsa kalau muka rabu jiya” numfashi daddy yasauke yace, “ohk, kukarasa general hospital dashi bari nakirasu nasanar musu zuwanku, kujirayi zuwana nanda dare, ganinan zantaho nima insha Allah” da “to” kawai mommy ta amsa masa ta kashe wayar, number yan’uwansa tafara laluba tana kiransu daya bayan daya tana sanarmusu,suhailat ce kawai bata kiraba. Hankalinsu gabadaya yayi matukar tashi, kowa barin inda yake yayi cikin gaggawa yanufi asibitin. Driver shima kara gudu ganin yadda mommy ta gigice tanata kuka tamkar ance mata mustaphan ya mutune. Cikin 18 minutes suka karasa asibitin, ma’aikatan asibitin harsun fito da gadon tura mara lafiya suna jiransu. Acan mommy tatarar da sadiq shi haryaje yana jiransu. Cikin sauri ma’aikatan suka karasa gaban motar su mommy da gadon daukar marasa lafiya suka kama mustapha suka dorashi akai suka fara turashi da gudu zuwa cikin asibitin. Mommy ma rufa musu baya tayi,tana tafe tana saba mayafi, ita da yaya sadiq, datashin hankalinsa ya ninku fiye dana da, dayaga halin da dan’uwansa yake ciki, beyi tunanin ciwon yayi tsanani hakaba. Emergency aka nufa da mustapha, cikin wani daki likitotin suka shiga dashi, suka dukufa dubashi domin ceto numfashinsa dake barazaranar karewa. Mommy se kaiwa da komowa take aharabar gurin,yayin da sadiq yatsaya jingine da bango dafe da kansa, cikin tsananin tashin hankali, kafin 20 minutes su haidar duk sun halla a asibitin, cikin damuwa suka hau tambayar mommy meyafaru amma mommy takasa basu amsa, ita burinta likitocin su fito suce mata danta yafarfado. Abangaren daddy kuwa suna gama waya da mommy yakira aunty yasanar mata. Nandanan aunty ta rude tafara shirin tahowa kano babu bata lokaci…..


Ina school ne,amma gabadaya hankalina yana gida. Zuciyata takasa samun nutsuwa. Karatunma yau ba fuskantarshi nakeba. zee dake hankalce da maryam tundazu ta zungureta,cikin rada_rada tace, “mairota lafiyarki kuwa,naga gaba daya bakya cikin nutsuwarki,se tagumi kikeyi” ajiyar zuciya nasauke nace, “babu komai kawata” “hmmm,kifadamun gaskiya kokunsamu matsalane da yaya sadiq” girgiza mata kai nayi alamun a’a. Shiru zee tayi batakara cewa komaiba, tamaida hankalinta ga karatun da’ake musu. nikam na matsu atashi hankalina gaba daya yayi gida……


Gwaggo ce, tsaye a gidansu su saleemat rike da kugu tazone akan dole se saleemat ta rakata gidan alh,menasara tunda tataba zuwa, ita tasan unguwar gidanne bata saniba. saleemat dai nazaune tana danna wayarta hankali kwance, dama umma batanan tafita taje asibiti ganin likita tun safe, kannenta kuma sun tafi school se ita kadai agida. Kara cokalo harbatsatstsen daurinta gwaggo tayi gaba,cikin masifa tace, “kefa dama yarinyarnan bakida kirki da mutunci kokadan, banda haka nazo tundazu ina miki magana amma kinmaidani yar iska kinki kulani, da suwaibace zaki mata haka.” Kallon gwaggo saleemat tayi tace, “amma gwaggo kina kallo dai umma batanan, nikadaice kuma maryam koda munjema batanan tana school” “Toni dama nace miki gurin wata maryam zani meruwana da wata maryam,gurin mutanen gidan zani ingaishesu” kafin saleemat tabawa gwaggo amsa wani almajiri yashigo yacewa gwaggo tazo tayi bakuwa tana kofar gida atsaye. Wani dogon tsaki gwaggo taja tana fadin, “wacce gantalalliyarce kuma tazomun ina shirin fita, amma mujedai ingani” takarashe zancen dabin bayan yaron. Itadai saleemat hamdala tayiwa Allah tasamu salama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button