Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Part dinmu na nufa na faɗa kan kujera ina sakin kuka, wani irin zafi da daci nakeji a cikin zuciyata, duk murna da farincikin zuwansu Aunty danake ya gushe. Banmasan haka nake da kishiba seyau, idona yarufe gani nake yayan shima ya rungume suhailat ɗin, kifa kaina nayi a hannun kujera ina sakin kuka mara sauti dana tuno yanda suhailat ta kwanta a kirjinsa. Yayi 3 minutes tsaye yana kallon Maryam da batasan yana tsayenba, a hankali ya tsugunna zuciyarsa babu daɗi ganin tana kuka ya dagota tare da janyota a hankali ta faɗa jikinsa. Rikesa nayi sosai ina ƙara volume din kukana, tare da sakin ajiyar zuciya. Lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa jinta ajikinsa. A hankali yasa tattausan hannunsa ya dago fuskarta. Narkarkkun idanunsa ya zuba acikinnata idon dake cike da hawaye. dif na hadiye kukannawa ina kallonsa nima, duk yanda naso nadauke idona daga cikinnasa amma nakasa. Kallon cikin ido mukewa juna, sosai bugun zuciyata yake ƙara ninkuwa, ganin bashi da niyyar dena kallona na runtse idona, wani abu naji yana yawo ajikina a sanadiyyar wannan kallonnasa dana kasa gane masa. Mustapha kallon Maryam yake with out control, batare daya saniba. Komai ya kwance masa daga kwanyarsa fuskarta ya matso daf da tasa har sunajin hucin numfashin juna, tare da bugun zuciyoyinsu. hawayene suka cigaba da shatata daga idona, ga tsoro da fargaba danaji sun lullubeni saboda betamun irin hakaba tunda muke, bamu taɓa kusanci me taɓa zuciya irin wannan ba, duk da idona a rufe yake amma nasan be dauke idonsa daga kainaba, saboda yanda nakejin wani abu kamar tsinkewar jini ajikina. Lumshe idonsa yayi tare da fesar da numfashi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. A hankali yake ƙara kusanto da fuskokinsu, bakinsa ya dora akan lips din Maryam batare daya shiryawa hakanba. zabura nayi cikin tsananin tsorata na fara kokawa da numfashina dake ƙoƙarin daukemun saboda dimuwa, kuka na saki ina ƙoƙarin raba jikina da nasa. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi yana ƙara manneta da jikinsa karon farko a rayuwarsa ya fara sucking lips ɗinta cikin tsananin zaƙuwa……..✍️

BARKANMU DA JUMA’ATU BABBAN RANA????

By
Zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….

BY
ZEEY KUMURYA

6️⃣1️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………..Jikinane ya kama kyarma jin yanda yake tsotsar lips ɗina kamar ze ciremun. yanda jikin Maryam yake rawa haka shima Mustapha jikinsa yakeyi, se numfashi yake fitarwa da sauri da sauri yana ƙara manneta da jikinsa kamar ze maidata ciki. Yakai 7 minutes yana kissing ɗinta cikin nutsuwa da salo me wuyar mantawa da tsayawa arai. a hankali ya zare bakinsa daga nata yana maida numfashi badon ya gaji da kissing ɗinnataba sedan kawai ya barta ta sarara. lumshe idonsa yayi cikin mawuyacin hali na bukatuwa da ita. Ni kuwa boye kaina nayi a kirjinsa ina maida numfashi kamar wacce nayi tseren gudu, har yanzun hawaye be bar zuba daga idonaba. A hankali cikin dauriya ya dagota daga jikinsa domin zamanta ajikinsa yana ƙara masa feeling. fuskarta ya dago da tafin hannunsa a karo na biyu ya zuba mata tsumammun idanunsa da suka rine sukayi ja, wanda suke ƙara rikitata. Idanunsa cikinnata yasa tafin hannun damunsa a hankali ya fara share mata hawayen fuskarta. rufe idona nayi ina turo baki gaba nace, “kadena kallo na haka” murmushi ne ya subuce masa dabe shirya masaba. cikin wata irin murya kamar me rada yace, “why?” a shawabe nace, “ina jin wani iri a jikina” be ƙara cewa komaiba ya sakeni. A hankali na mike da kyar jikina kamar anmun duka saboda kasala, ban ƙara dubansaba na nufi ɗakina na nashige domin na wanke fuskata. Binta yayi da kallo har ta shige, ajiyar zuciya ya sauke yana maida numfashi, harna fito yana zaune a falon yanda na barsa, sena ganshi kamar mara lafiya kokuma wanda wani abu ke damunsa, senaji duk babu daɗi ganinsa a haka, kamar na tambayesa abunda ke damunsa,tunawa da nayi su Aunty sun jima da zuwa, sena ja ƙafata na fice daga falon cikin sanyin jiki. seda nazo zan shiga falon kuma naji wani iri na abunda danayi sanda naga suhailat a jikin yaya, wata kunyar su naji ta lullubeni, musammanma ammi. Daurewa nayi na shiga falon da sallama. suna falon gaba-ɗaya sunata shan hirarsu, su ammi sun cikawa su Aunty gabansu da kayan ciye_ciye da drinks. suka amsamun sallamata atare amma banda umaimah da suhailat data dago da sauri jin Muryar Maryam. Da gudu Aliya tataso ta rungume maryam cikin tsananin murna. Nima rungumeta nayi ajikina cikin farin ciki. Suhailat kallon Maryam kawai take da matuƙar mamaki. ” kamar maryam me aikin mommy ?” suhailat ta furta hakan aranta cikin tantama, tana tunanin ba Maryam din bace, kamace kawai, dan wannan tafi Maryam ɗin data sani fari da kyau gami da wayewa. sakin juna mukayi da aliya cikin murmushi, ƙasa_ƙasa tayi da murya yanda ni kaɗai zanji tace, “matar yaya, mene sirrinne? Irin wannan kyau haka, ga abubuwa se juyawa suke duk kiwon yayannawane haka?” Harararta nayi nace, “daga zuwanki zaki fara, Ni matsamun inje gurin auntynah” dariya aliya tayi, Ni kuma na wuce gurin Aunty daketa sakin murmushi tun shigowar Maryam, daga yanda taga Maryam ɗin tasan tana cikin kwanciyar hankali. Suhailat Binta tayi da ido kamar wata doluwa. Rungume Aunty nayi ina faɗin “oyoyo Aunty nah, dafatan kunzo lafiya” aunty na ƙara faɗaɗa fara’arta tace. “Lafiya kalau Maryam dita, dafatan kina lafiya?” “Lafiya lau Aunty” na faɗi haka ina sakinta da murmushi dauke a fuskata. Suhailat ta haɗiye wani yawu tana duban Aunty tace. “Aunty wai wannan Maryam ɗin dana sanice house girl dinmu?” cikin rashin jin dadin house girl da suhailat ta kira Maryam Aunty tace, “ehh” maida kallonta tayi ga Maryam cikin tsananin mamakin yanda taga yarinyar ta sauya mata. Ba yabo ba fallasa nace, “ina wuni Aunty suhailat” tana ɗauke idonta daga kallon Maryam ɗin tace. “Fine” zuciyarta cike da mamakin wai gidan waye sukazo? da taga Maryam da yayanta. Tasan dai Aunty tace mata yaya yayi tafiya ne, to kenan nan garin shine inda yazo, to ita kuma Maryam ɗin metake a gidan? “May be nan ɗin ma aikatau tazoyi” suhailat tabawa kanta a cikin zuciyarta. (Ke kaɗai dai????) ƙara kallon kofar falon tayi a karo na ba adadi sannan ta juyo ta dubi Aunty tace, “wai ina yayanne Aunty, naga haryanzu be ƙara shigowa ba?” Harararta kawai Aunty tayi, bata bata amsaba cikin takaicin yanda take nuna rashin kunyarta a fili a gaban kowa, tun daya fita take ta maganarsa ita tayi missing ɗinsa kaza_kaza. Aliya ta dubi Maryam tace, kawata zo innuna miki wani abu” ta faɗi haka tana latsa wayarta. tashi nayi fuskata dauke da murmushi na koma kusa da aliya. tana cigaba da latsa wayartata tace, “Ina yayan wai?” “yana part dinmu” na bata amsa. wayartata ta mikomun tana faɗin “kalli hotunan kayan nan” karba nayi nafara kalla, waro idona nayi waje saboda ganin hotunan wasu ƴan’iskan kaya wanda idan mutum yasasu basu da maraba da tsirara. kallonta nayi so surprise nace, “wannan kayanfa ina kika samosu aliya?” wani murmushin tayi tace, “kike wani zaro mun ido dankinga wannan kayan, to sune tsarabar dana kawo miki” ƙara waro idona nayi waje nace, “inye me dasu Aliya?” Hararata tayi tace, “bangane kiyi me dasu ba, kiyiwa yayana kwalliya mana” nima harartata nayi nace, “kwalliyo mata, to ba daniba wannan tambaɗar, a inama kika samo kayanma tukunna?” “Bansabiba ke, tunda na miki gwanintama ban burgekiba kinsan wahalar danasha kafin nasamosu?” ganin yanda tayi da fuska senayi murmushi nace, “haba kawas, kema kinsan ba haka bane, kinsan babu ta yanda za’ayi in iyasa wadannan kayan ajikina” “to cewa nayi kisa kifita dasu, mijinki kawai zakisawa ya gani ai” kallon aliya nayi baki buɗe, araina ina faɗin. “Abunda baze taɓa yiyubama kenan” kafin wani acikinmu ya ƙara magana, Ammi ta katse mana muhawarar tamu da faɗin, “yata kizo kuci abinmana karyayi sanyi, tun dazu ankawo muku amma kunki ci kamar wasu baƙi” tana kallon Aliya tayi maganar. cikin girmamawa aliya amsa mata da “to” sannan tatashi ta nufi gun dinning, ta barni da wayarta a hannu. Suhailat ma seda ammi ta mata magana sannan ta mike itama. Umaimah ta rakata da harara, tunda suka zo ƙala bata haɗasu da suhailat ɗin ba, ta lura yarinyar nada jin kai da dagawa ga kuma fuskanta datayi itama tanason abunda takeso wato Mustapha….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button