Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

KADUNA

Su Aunty sun sauka lafiya, tun a daren jiyan sukayi waya da ammi data kirasu dantaji ko sun sauka lafiya. Tun da suka taho suhailat take damun Aunty da tambaya akan gidanwa sukaje, da kuma tambayar me Maryam take a gidan dan daga baya ta fuskanci maryam ba aiki take a gidanba, itama tana rayuwar yanci ne kamar kowa na gidan. se kuma ammi dataga tana mata kama da mustapha musamman ta idanunsu da yanayin yanda suke kallon mutum, dansu ba normal kamar kowa kallonsu yakeba kuma Maryam ma taga irin kallon take. shine abunda ya ƙara bata mamaki ya kuma ɗaure mata kai, Aunty dai bata kulataba da tambayoyinta balle ta bata amsa, hakama Aliya dataketa karatun Novel ɗinta a wayarta. Yau da safe bayan suhailat tagama shan baccin asararta ta tashi tayi wanka ta fito falon Aunty. Babu kowa a falon, fridge ta nufa ta buɗe ta dakko hollandia me sanyi ta nemi guri ta zauna ta fara sha a yangance. tana cikin sha Aunty ta shigo falon ta dawo daga part din abbansu aliya ne. sallama tayi suhailat ta amsa mata ciki_ciki, dan har yanzu haushin Aunty taƙi barinta a jos take. batare da Aunty ta zaunaba tace, “suhailat wai banace kidena shan abu me sanyi bane, bakisan illa bane a gareki da abunda ke cikin ba.” Zunburo baki tayi gaba tace, “To Ni fa Aunty banajin daɗin komai se abu me ɗan sanyin.” Harararta Aunty tayi bata ƙara cewa komaiba, se kwace sauran hollandia’n datayi ta shige bedroom ɗinta bayan tacewa suhailat ta shirya zasuje asibiti anjima. suhailat ta amsa mata kamar zatayi kuka saboda kwace mata hollandia’n datayi. Itafa ta gaji da wannan wahalallen cikin, ace kullum cikin shan wahala take, tun daga ranar da Dr. Ta tabbatar tana da ciki, har yau bata ƙara samun ishashshiyar lafiya ajikintaba, inda Allah ma yataimakama bata kwadayi_kwadayi, gashi cikin yayi sanadiyyar katsewar karatunta, kuma a tunaninta shiya hana Aunty tada maganar auransu da mustapha, shiyasa take ƙara tsanar cikin. Kamal ne ya faɗo mata a rai, tanason kiranshi kodan ta sanar masa tana ɗauke da cikinshi amma kuma tana tuna gargardin mommy data mata akan karta sanar masa, kuma ko yanzu ta kunna wayarta seya kirata kokuma ya mata text. kawar da tunanin kamal tayi ta faɗa na masoyinta mustapha, ita yanzu kawai neman hanyar dazata koma Jos take batare da Aunty ta saniba, dan yanda takeson kasancewa da yayannata ko’a motar haya zata iya zuwa Jos ɗin, Ita dai burinta kawai taganta kusa da masoyinta kota halin ƙaƙa….. Aunty zuciyarta babu daɗi ta ajiye guntun hollandia’n akan bedside locker. Tanajin ciwo sosai a cikin zuciyarta akan cikin dake jikin suhailat, kawai tana dannewane, ita fargabartama ta yanda zata iya sanar da daddy maganar cikin dake jikin suhailat ɗin, ita kanta suhailat ɗin tanason ta zaunar da ita ta mata tambayoyi akan cikin da kuma wanda ya mata cikin, amma taga suhailat ɗin kwata_kwata babu nutsuwa a tattare da ita, gashi wani abu dayake ƙara bawa Aunty takaici, suhailat bata da tarbiyya ko ladabi ko kaɗan. duk kwanakin datayi agidannan har yau bata san gari ya waye taje ta gaishedda Abbansu Aliya ba, kullum se Aunty ta turata take zuwa, masu aikin gidanma ta lura hakuri kawai suke da halinta, amma basajin daɗin zama da ita. shiyasa yayan Aliya kwata_kwata baya shiga sabgarta tunda canma bare kuma yanzu, duk da shi mutum ne me fara’a da barkwanci kamar Aliya, Aunty har faɗa take masa akan yanda yakewa suhailat ɗin. Ajiyar zuciya Aunty ta sauke ta bar tunanin danba mafita bane a gareta, addu’a itace kawai mafita. wayarta ta dakko ta kira likitan su ta sanar masa zasuzo asibiti anjima………


Ya ɗan jima a toilet din sannan ya fito, dakinnasa ya shiga bi da kallo ganin yanda Maryam ta gyareshi, yanda ta ɗame gadon ta jera filollika yafi komai burgeshi, gadon tamkar ba’a taɓa hawa ankwanta a kanshiba. Ashe shi da duk jagwalgwala abunsa kawai yake be iyaba, kuma shi idan zeyi gyaran dakin seya ɗauki lokaci da me tsayi kafin yagama amma ita gashi acikin lokaci kaɗan harta gyara ta fice. Karasawa yayi gaban madubi ya ɗauki lotion ɗinsa ya fara shafawa a lallausar farar fatarsa wadda ta jiku da hutu. Cikin some minutes ya gama shirinsa cikin ƙananun kaya wanda suka amshi jikinsa da matuƙar yi masa kyau sannan ya tada sallah…. Falo ya fito hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa, maryam da hankalinta yake kan kallon datakeyi batamasan ya shigo falonba.

A bayan kujerar datake ya tsaya, sunkuyo da fuskarsa yayi daidai da tata ya hura mata iska daga bakinsa a fuskarta, lumshe idona nayi da sauri a ɗan tsorace saboda bansan da zuwansa falonba, yanzu daddaɗan kamshinsane ya tabbatarmun da shine. batare daya janye fuskarsa daga kusa da tataba yace, “ya jikinnaki?” numfashi na sauke me ƙarfi saboda yanda yake gogamun sajen fuskarsa a kumatuna nace, “da sauƙi” cikin matuƙar raunin murya. kafin ya kuma magana aka fara knocking kofar falon, wayarsa ya ajiye a gefena sannan ya zagayo ya nufi kofar, da ido nabi bayanshi da kallo cikin wani irin baƙon yanayi ina sauke numfashi. Ammi ce hannunta ɗauke da basket data haɗo musu launching aciki. Murmushi suka saki a tare ita Mustapha lokacin da sukayi 4 eyes. cikin murmushin yace, “sannu da zuwa AMMINAH” itama da murmushin a fuskarta tace, “yawwa MY NOOR” tare da yin hugging ɗinshi lumshe idonsa yayi yana ƙara hugging ɗinta shima cikin tsananin so da kaunar dake tsakanin ɗa da mahaifiya. sakinsa ammi tayi ta shafa kansa tace, “ya jikin takwarata?” Da mamaki ya kalleta dan be san ta saniba. shanye mamakinsa yayi yace, “da sauƙi” ya ƙarashe zancen da karɓar basket din hannunta. Ammi tace, “Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffarane” “Ameen” ya amsa yana kama hannunta suka shiga cikin falon. kallonsu nake cike da ban sha’awa da burgewa, sunmun matuƙar kyau, kana ganinsu kaga uwa da ɗanta. sakin hannunsa ammi tayi ta ƙaraso gurin Maryam tana faɗin, “ɗiyata sannu ya jikinnaki?” da sauri na zamo daga kan kujerar danake ina daura ɗankwalina cikin girmamawa nace, “da sauƙi ammi, ina wuni” ammi cikin jin daɗin yanda taga jikin maryam tace, “lafiya kalau ɗiyata, Masha Allah haka akeso, naga jikinnakima da sauƙi bayanda nayi zaton ganinkiba, Allah ya ƙara sauƙi, ya inganta” “ameen” na’amsa ina ƙara yin ƙasa da kaina cikin jin kunya, gani nake kamar tasan meyafaru. zama ammi tayi akan kujerar danake, Ni kuma na zauna a ƙasan kujerar. Shima Mustapha zama yayi a gefen ammi ya kwantar da kanshi akan kafadarta. Kallon fuskarsa ammi tayi tace, “meke damunta ne?” yace, “zazzaɓi” atakaice. Ammi tace, “amma kuma shine bakuje asibiti anduba taba NOOR?” Yace “na kira family doctor ɗinku tazo ta dubata” da mamaki ammi tace, “Dr husnah?” Yace “ehh” ammi tace, shine bata shigo part ɗina mungaisaba” yace, “may be, tana sauri ne, danda early morning tazo, kuma daganan zata wuce aiki” ammi tace, “ehh hakane ai nasan Dr husnah akwai kirki, amma duk da haka Yakamata ku fara zuwa asibiti dan adinga duba lafiyarta dana abunda ke cikinnata” dagowa nayi da sauri na saci kallonsa, shima kallon maryam ɗin yayi sannan yayi murmushi yace “to ammi zamuje insha Allah” shafa kuncinsa ammi tayi tace, “yawwa, Allah ya ƙara lafiya, ya muku albarka ya baku ƴaƴa na gari masu albarka” “Ameen summa ameen” muka amsa a tare. tashi nayi na ɗauki basket ɗin da ammi ta shigo dashi na abinci na nufi kan dinning dashi na ajiye sannan na shiga kitchen…….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button