Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina fitowa daga toilet natarar aunty ta kwasomun kayan dazansa daga dakina. Amma ita bata dakin. murmushi nayi nadauki kayan nafara sawa, zuciyata cike da kaunar aunty, yanda take nunamun kulawa ko yar cikinta sehaka. Tunanin yaya sadiq ne yafadomun acikin raina, haka kawai naji gabana yayanke yafadi dana tunasan. nasan yanzu yanata nemana a waya besameniba, amma idan aunty tashigo zance ta aramun wayarta na kirasa. kayan kawai nasaka nafito falo domin naje nagaishe da mommy, aunty nagani tafito daga kitchen hannunta dauke da plate da cokali. “Sannu aunty” “yawwa maryam, yajikinnaki?” “Dasauki aunty” “Allah yakara sauki, kizo kici indomie dinnan kenadafawa sekisha magani, zamuyi wata tafiyane yanzu, nakira doctorn ma yacemun gashinan zuwa” da mamaki nake kallon aunty cikin sanyin murya nace mata. “Aunty tafiya kuma, ina zamu?” “nima dai bansaniba maryam haka dai yaya yacemun, sekiyi sauri kici abincin munayin sallah zamu tafi” cewar aunty tana ajiye mun plate din akasa. “To aunty bari naje nagaida mommy, yau antofawa yaya addu’ar kuwa?” kallona aunty tayi sannan tace, “kici abincinki kawai anti atika batanan, shikuma mustapha jikinsa yayi sauki sosai, alhamdulillah” ajiyar zuciya nasauke aboye tajin dadin aunty tace, jikin heartbeat dina yayi sauki. Zama nayi akan carpet na bude
plate din da aunty takawomun nafara cusa indomien badon inajin dadintaba, saboda yanda zuciyata take bugawa inajin tamkar wani bakon al’amari nashirin faruwa dani ayau………..✍️

kuyi hakuri da typing error, yauma babu editing

By
zeey kumurya
ABUNDA KASHUKA….
(shizaka girba)

4️⃣0️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

……….Abangaren su faruq kuwa, gabadaya part dinsu suka nufa zuciyoyinsu babu dadi, kowa dakinsa yashige ya kullo kofa domin samun kadaita. sadiq da nadama gami da kunya suka masa katutu yakasa zaune yakasa tsaye zarya kawai yakeyi a dakinsa abubuwa biyu ne suke damunsa a wannan lokacin. Na farko wata zazzafar kaunar maryam ce ta mamaye masa zuciya. na biyu kuma boka tsidau yatabbatar masa da cewa matukar aiki ya lalace to ciwon da mustapha yakeyi ze dawo kansa ne. a yau kam yayi nadamar kasancewar mommy mahaifiyarsa, ta cusa masa abunda baze taba amfanesaba arayuwarsa. Fiye da shekaru goma ta cusa masa kiyayyar mustapha me tsanani acikin ransa, ta nuna masa mustapha babban makiyinsune, alhalin bahaka abun yakeba. wani zazzafan huci ya fuzgar, hannunsa yakai ya ware hiramun dake kansa gami da cire safar hannunsa, dinkin da’aka masa yabayyana na ciwon da maryam taji masa. fadawa kan gado yayi sharab, zuciyarsa na masa kuna jiyakeyi tamkar ya kashe kansa dan bakin ciki, ga wata kewar maryam data cika masa zuciya. Da farko da yaudara yafara son maryam, amma zuwa yanzu son yarikide masa yakoma nagaske wanda yake barazanar tarwatsa masa zuciyarsa. kansa yafara bubbugawa akan gadon a fili yafara magana. “Mommy, why,..! why, dakika zabarmun wannan rayuwar, meyasa nabiye miki nakai kaina ga halaka,yanzu da wanne ido zankalli maryam wadda tabani dukkan yarda da amanarta, ta dauki a amatsayin bango na rayuwarta, koyaya zataji idan taji labarin ninake kokarin rabata da mutuncinta. Tabbas ubangiji baze barniba akan cutar da bayinsa wanda basujiba basu ganiba danayi. kansa yarike dayake kokarin tarwatsewa saboda damuwa, wannan ranar besan dame zekirataba arayuwarsa……….

naci indomie fiye da rabi, sannna na rufe plate din saboda aman dana faraji yana tasomun, ahankali na mike nanufi dakin aunty domin nace ta bani aron wayarta nakira yaya sadiq dina. Da sallama nashiga dakin, aunty dake hada kaya acikin wata yar karamar jaka ta amsamun sallamar batare data dago ta kalleniba. zama nayi akasan gado cikin sanyin murya nace, “aunty dan Allah kibani aron wayarki zankira yaya sadiq nasan yanzu yanata kirana besameniba” dagowa aunty tayi tazubawa maryam ido, cikin tausayinta domin ta dade da fuskantar soyayya sukeyi, gashi harta kasa hakuri tatambayeta Aron waya takirashi, batasan shine me kokarin bata mata rayuwaba, koda daddy befadaba dama aunty ta dukurcewa ranta bazata bar takara kwana acikin wannan gidan da’ake burin cutar da itaba. kasa nayi dakaina ganin aunty tana kallona, wata kunyartace ta lullubenu wata zuciyar tawace tacemun kodai aunty tasan muna soyayya da yaya sadiq dinne. “Maryam, nakirashi ai tundazu amma wayartasa bata shiga, akashe ake cewa” aunty tafadawa maryam haka, domin batason tasan komai tunyanzu tafison sekomai ya lafa tukunna. “Shikenan aunty” nabata amsa cikin sanyin jiki. domin bugun zuciyatane yakaro akannada…

Mustapha yadau tsahon mintuna 20 a toilet kafin yaja kafa yafito saboda matsanancin jirin dake kwasarsa amma bawai dan ruwan ya isheshiba. kan gadonsa yafada Cikin mawuyacin hali, jikinsa na wata irin kyarma, dakyar ya iya jan bargo ya lullube jikinsa saboda wani sanyi sayaji yana shigar jikinsa. tunanin abubunwa dasuka faru abayane suke dawo masa kwanyarsa, tabbas biri yayi kama da mutum, mommy tasha siyo masa kayan maye domin yadingasha, wai rayuwarce seda haka. Agaban mommy suhailat take hugged dinsa kota dane kan cinyarsa amma mommy bazata kwabetaba sema ta nuna jindadinta. Mommy bata bashi tarbiyyya tagariba kokadan tayi masa abubuwa dadama domin ya lalace amatsayin soyayyar datake masane haka, Allah ne kawai yakareshi dakuma tsaiwar dakan da daddy yayi wajen ganin rayuwarsa ta inganta. wasu hawayene masu matukar dumi suka digo masa, wanda dakyar yasamu suka zubo. har yanzu yana mamakin wai mominsa datafi kaunarsa fiye da komai da kowa a duniya ita ce take furta Kalmar tsana agaresa saboda abunda duniya. har yanzu yanajin guntun kaunar mommy acikin zuciyarsa, kobabu komai ta raineshi kuma ita yataso yake kallo amatsayin uwa. zurfaffen tunani yashiga sosai akan rayuwarsa wanda hakan yakara haddasamasa matsanancin ciwon kai dana zuciya, tun yana gane meyakeyi haryafice daga hayyacinsa,komai yadauke masa dif…….

Daddy akokarinsa nason tafiyarsu takance da wuri, yadauki mota yafita dakansa domin yimusu cuku_cukun tafiyar, ga wayarsa dake Cikin aljihunsa sekiransa akeyi ga tarin damuwar dake addabar ransa. tukin kawai yakeyi amma hankalinsa baya jikinsa yanacan duniyar tunane_tunane. be’ankaraba sekawai jiyayi ya gwabzi wata mota adaidai dangi. Cikin tsananin firgici daddy yafara ambaton “subhanallah” a fili, dasauri yayi parking motar tasa yafito ko rufewa kofar beyiba. mutane harsun fara taruwa saboda motar ta jirkicene anata kokarin dago da ita. shima daddy karasawa yayi akafara kiciniyar daga motor dashi. direban dake tuka motar yafito babu wani rauni ajikinsa sedai juya dake dibansa sakamakon jirkicewar da motar tayi, dan motar ta barin dama ta jirkita. Anyi nasarar juyar da motar har’aka fito da matar da direban yake tukawa, sedai matar babu alamar numfashi atattare da ita. tashin hankali wanda ba’asamasa rana. “Ana wata ga wata” daddy yafurta hakan azuciyarsa. “Ya Allah kasa ba kisan kai nayiba” yakara furta haka lokacin da’aka dakko matar a hannu rai ahannun Allah,babu inda yake motsi ajikinta. hankalin direban idan yayi dubu yatashi. Se kiran “innalillahi’wa’inna’ilahirraji’un” yakeyi kamar yadda daukacin mutanen wajen keyi. Cikin sauri daddy yayi gaba zuwa wajen motarsa aka Sanya matar abayan motar. Kasancewar daddy ba boyayyen mutum bane, mutane se fadin. “Yallabai Allah yakiyaye gaba sukeyi” driver seat daddy yashiga direban motar kuma yashiga front seat daddy yaja motar yanufi asibitin aminu kano. wayarsa yazaro yakira bakanikensa yasanarmasa yazo ya dauki motar dayabugedin yatafi da ita, tare da kiran asibitin yasanar musu da zuwansu. Cikin mintuna kalilan suka karasa asibitin abakin emergency yayi parking motar yafito dasauri yabude bayan, ma’akaitan asibin suka kama matad suka sanyata akan abun tura marasa lafiya suka nufi ciki da ita dasaurinsu, suma su daddy rufa musu baya sukayi………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button