Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

..Zaro idanuwana nayi waje cikin kidima nace”gwaggo wanne aikin kuma. Wata muguwar harara ta cillomun tace”aikin uwarki,gidan alh.Suleiman menasara zakije ki musu aikatau. Dasauri na dafe kirjina,saboda wata irin bugawa da zuciyata tayi.”nashiga uku gwaggo,rarrafawa nayi na karasa gareta,kafafuwanta na kama idona na zubda hawaye,nace”gwaggo dan girman Allah,Dan darajar annabi muhammadu S.A.W. gwaggo,karki kaini aikatau,kiduba maraicina gwaggo,kada ki kaini inda ba’asan mutuncinaba,zanzauna dake,zan miki duk abunda kikeso,idan wani lefin na miki kikace haka,kiyi hakuri dan Allah,bazan kuma mikiba wlh, kirufamun asiri kamar yadda Allah yarufa miki,kici gaba da rikeni gwaggo….wata hambara ta kaimu da kafarta,baya nayi ina sakin kuka me tsuma zuciya,tausayin kaina da rayuwata nakeyi. Lami data saki baki tana kallona tace”ladi! Kai amma yarinya akwai bakin ciki,wannan ba ‘yar halak bace,ba ‘yar daza’ayi arziki da ita bace.banda haka keda zakije gidan Hutu gidan dadi,mene abun damuwa.aikin dazakiyi bawani meyawa bane,gidan burjik yake da ma’aikata.kawaidai sunasan yarinyane…”bar bata bakinki wajen yimata bayani lami,dolenema taje aikinnan dan ubanta,ko yanka naman jikinta zasu dingayi,zaki tashi kije ki shirya kose nazo na tattakaki.da gudu na tashi memakon na nufi dakina kamar yadda gwaggo tace sena fice na nufi gidan su saleemat.

Umma tana tsakar gida akan kujera tana tsintar shinkafa,nafada kanta ina sakin wani marayan kuka. Dasauri ta dagoni tana tambayata “lafiya maryam,meyafaru me gwaggon ta miki? Cikin shashshekar kuka nace” umma kitaimakeni wai gwaggo aiki zata kaini gidan alh.sulaiman menasara,wlh umma banason zuwa masu kudinnan basanin darajar mutum sukayiba,umma burina Inyi ilimi me zurfi arayuwata amma gwaggo ta hanani,kuma hakanma be ishetaba seta kaini aika….kuka ne yaci karfina.rungumeni umma tayi a jikinta cikin sanyin murya ta fara mun magana”kiyi hakuri maryam,kowanne bawa da irin tasa kaddarar,haka taki kaddarar tazo miki,kiyi hakuri kije kiyi aikin zakiga ribar abun agaba.kedai kawai duk inda kika tsinci kanki ki rike mutunci,da gaskiya, kiji tsoron Allah akan duk abunda zakiyi,zaki samu nasara. “Haba umma,menayiwa gwaggo dazata kaini aikatau,aikatau dinma gidan babban mekudi.

Dagoni umma tayi Daga jikinta ta fara sharemun hawayena”kiyi hakuri maryam,ni kaina na girgiza nayi mamaki dajin gidan daza kije aiki,amma ita gwaggon ta inama tasan gidan mesanaran,harda zata kaiki aiki can. “Wlh nima umma bansaniba,kawartace lami tazo shine tace inbita muje ta kaini. Jinjina kai umma tayi tace.”nasan son kudin gwaggo ne zesa ta amince,batare da tunanin irin rayuwar dazakiyi agidanba,kokuma halin dazaki shigaba,ita dai kawai taturaki kiyi aiki duk wata abata kudinta,amma abun da mamaki ace yanzu kamar wannan gidan basu da me aiki,anya kuwa babu wani lauje cikin nadi. ” umma nima abun da nake tunani kenan,ina tunanin zuwana gidan ba alkhairi bane,dan yau gaba daya jikina asanyaye yake,tunda na tashi gabana yake ta faduwa,Ashe ga abunda zesameni. “Kidena cewa haka maryam kitashi kije kar tayi ta jiranki,Allah yana tare da me gaskiya, zamuyi ta tayaki da addu’a kema kuma kidage,domin babu abunda ya gagari ubangiji. Hawayen fuskata na share,nace. “Yanzu umma shikenan tafiya zanyi,in fuskanci wata sabuwar rayuwar,tafiya zanyi inbarku,kukadaine mutanen danake gani nakejin dadi,inajinki umma tamkar uwata dana rasa,a kullum kina nunamun rayuwa kina fadamun abunda yake na dai_dai,ga ‘yar uwata kuma saleemah me kaunata dason ganin farin cikina,yanzu idannatafi na barku,Waze dinga mun abunda kukemun gaskiya umma bazan iyaba” zaki iya umma ta katseni da sauri,kada ki damu maryam ai bamu rabuba,nahar abada,duk sanda kika samu lokaci sekidinga kawo mana ziyara.jin muryar gwaggo nayi har gidan su saleemat tana kwalamun kira.zanyi magana umma ta hanani.”tashi kije maryam Allah ya bada sa’a.kisa aranki Allah yana tare dake akoda yaushe.cikin sanyin jiki na mike,inajan kafafuwana dasukamun nauyi. Gaskiya na yadda gwaggo bata kaunata,bata daukeni a matsayin komaiba.anya kuwa zan iya zuwa aikatau dinnan,zuciyatace ta fara bani shawara in gudu kauye kawai wajen ‘yan uwan innata……..✍️

By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

0️⃣5️⃣

………..Saboda naji hankalina be kwanta da aikatau dinnan dazaniba,haka dai na daure nafice Daga gidansu saleemat. A soron gidanmu naci karo da gwaggo ina kokarin shiga tana kokarin fita.wani gigitaccen mari ta wankeni dashi. “Dan ubanki kinaji nace miki sauri akeyi shine kika fice kin tafi sanarwa kanwar ubannakiko,to dakika fada mata ta hanaki tafiya mana,zaki wuce ki tafi kose naci ubanki,gwaggo ta karashe zancen tana rankwashina.hannuna dafe da kuncina,idanuna na zubar da hawaye nake duban gwaggo.

Tsugunnawa nayi akan gwiwoyina na kama kafarta ina rokonta a karo na biyu.” Gwaggo kimun rai,karki kaini aikatau dinnan naji hankalina be kwanta dashiba inajin tamkar zuwana ba alkhairi ba…..hanbari gwaggo tayi yasani kasa karasa zancena,baya nayi ina kara volume din kukana,matsowa gwaggo tayi da nufin yimun shegen duka.lami ce tataho daga cikin gidan jin kukana ta rike gwaggo. “Haba ladi,kin manta inda zamujene da ita,sokike suki daukarta kinsan halin maryam yanzu kina dukanta seta langwabe.sakin gwaggo tayi ta kamoni,tashi kije ki shirya mu wuce,kema kece da taurin kan tsiya,banda haka ni banga abunga damuwa ananba,gidan hutufa zaki cigabane yasameki.tafiya na farayi tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki,na nufi cikin gidanmu.gwaggo tana bina da wata uwar harara.

bani yanda zanyi bani da zabi,bani da mafita banda nabi lami.jikina a sanyaye,haka na hada ‘yan tsummokarana acikin bakko.hawayene kawai yake malala a idanuwana.harna gama hada kayana.ko wanka da cin abinci gwaggo bata barni nayiba,haka nabi lami ina kuka kasharban,mutuwar innata tadawomun sabuwa tamkar yau ta mutu,nasan datananan dahaka bata faru daniba.amma gwaggo ko tausayina batajiba.sema jaddadamun takeyi nayi aiki da kyau,nayi duk abunda aka sani na bisu sauda kafa…….

Files ne da yawa agabansa yana signing ajiki,wayarsa dake gefe ta fara ruri alamar tana bukatar agaji.a hankali ya mika hannunsa ya dakko,mahaifinsane yake kiransa.Daga wayar yayi ya kara a kunnensa. ” Assalamu alaikum” ya furta cikin daddadarr muryarsa. Cikin tsananin farin cikin jin muryar dannasa,daddy ya amsa masa sallamarsa,gaisawa sukayi ya tambayesa ayyuka da komai da komai.sanar masa daddy yayi ya shirya yau da yamma,yaje a abuja zasuyi meeting da wasu abokanan kasuwancinsa,saboda shi abubuwa sun rikesa baze samu damar dawowa kasa yanzuba.fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa masa da insha Allah.ajiye wayar yayi bayan sunyi sallama. Shikam Sam zuwa abujannan bemasa dadiba,saboda bayason yayi nisa da ‘yan uwansa da mahaifiyarsa,amma babu yanda zeyi dole yaje,saboda babu jayayya tsakaninsa da mahaifansa.yarasa meyasa mahaifinsa,komai na harkar kasuwancinsa yake dorashi,duk da yanada manyan yara amintattu,amma komai shiyake sawa akan gaba,gashi shi kuma bayason Hulda da mutane.bayason hayaniya kokadan.ganin zaman zebata masa time,yasashi mikewa ya dakko white paper yayi rubutu akan tafiyar dazeyi na tsawon sati biyu.sakatariyarsa ya kira ya bata takarda dayayi rubutu takaiwa manager na company……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button