Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Harna nufi dakin hajiya zan gyara naji muryar suhailat. “Ke!” Tsayawa nayi amma banjuyoba. “Kutmar, lallaima yarinyarnan wuyanki yayi kauri. ina miki magana kinki juyowa saboda tsabar raini ko? Juyowa nayi ina bata hakuri saboda banason tashin hankali. “Dalla ni,rufemun wani rubabben bakinki,nonsense kawai.zanyi bako anjima,kafin na dawo daga school ki hada masa drinks,sannan kuma zakuyi aikin delicious dinsa tare dasu salame.amsa mata nayi cikin girmamawa nashige dakin Hajiya.

Seda nagama aikina tsaf,nima na karya. sannan na koma nayi wanka. Shiryawa nayi cikin wata atamfa dinkin doguwar Riga.yay mun dass ajikina.turaruka masu sanyin kamshi na fesa wadanda yaasadiq ya kawomun.hijabina iya gwiwa nasaka Wanda ya shiga da kalar kayan. Tsayawa nayi agaban mudubi ina karewa kaina kallo. Nikaina nasan na canza,a yan kwanakin danayi a gidannan. To zanci me kyau,insha mekyau, sabulun wanka me kyau,man shafawa me kyau.makwanci me kyau gashi tunda nazo banga ranaba. Falo na fito da niyyar tambayar mommy, zan fita. a kitchen na tarar da ita tana shirya kaya a wani katon kwando. (Da’alama dai na dan lelentane.)”Sannu da aiki mommy” “yawwa,am maryam dan kaiwa son breakfast dinsa,idan kika dawo sekiyi aikin da daughter tasakaki. atunaninta aikin suhailat na taho yi. dammmm!! Zuciyata ta buga,yaseen ni nama manta dashi kwata_kwata agidan,dazu da safe agurin break bangansaba shiyasa bantuna dashiba. Karba nayi ina amsa mata. “Kiyi sauri maryam,yana saurine ze fita. Akwai plates a kitchen dinsa,ki duba ki dakko seki zuba masa. “Toh mommy na’amsa cikin ladabi.

Tunda na nufi part dinnasa zuciyata take luguden bugu, tundaga falon kasa sihirtaccen kamshinsa ya ziyarci hancina lumshe idanuwanayi saboda dadinsa.sama nahau,shima dai kamshinnasane yamun sannu da zuwa.kan dinning na ajiye kwandon. Kofar dake kusa dakinshi na bude cikin sa’a kuwa nanne kitchen. Tsayawa nayi ina kallon kitchen din,Wanda ko wata amaryar albarka.sekace mace komai kwai a kitchen din. Ba karya ya hadu shima.Plates din na dakko seda nadaurayesu sannan na dawo falo.rasss,gabana yayanke ya fadi ganinshi zaune akan dinning yana latsa wayarsa. Karasawa nayi cikin matukar tsoronsa na ajiye plates din,gaishesa nayi amma ko kallona beyiba.tambayarsa nayi mezan saka masa nanma shiru kamar besan ina gurinba.tsayawa nayi ina kare masa kallo.kananun kayane ajikinsa,rigar farace Tass, se bakin wando.kayan sun masa kyau sosai,se yanzu naga tsananin kamarsa da mommy.gajiya nayi da tsaiwa nafara serving dinshi,ina kunkuni kasa_kasa. Komai zuba masa nake acikin plate ina tura masa gabansa. Na dakko farfesu zan zuba masa,nadan saci kallonsa. Idanuwansa tsam akaina yana jifana da wani irin kallo.nandanan jikina yafara rawa. Allah yagani tsoron idanuwansa nakeyi,saboda suna saukarmun da wani yanayi ajikina.ban Ankara kawai gani nayi spoon din yafadi daga hannuna,ferfesunne ya zube akan table din.cikin matukar tsoro na dago ina kallon gefen dayake. Gaba daya roman farfesun ya tsatstsallu a gaban farar rigarsa……..✍️

yauma ba editing,am sorry????????

By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

1️⃣3️⃣

……………Kallonta kawai ya tsaya yanayi cike da takaici da bakin ciki,bayan ta shigo ta samesa bata masa sallamaba, sannan tana ta masa surutun banza,yanzu kuma yana sauri zeje office tazo ta bata masa Riga,dolene ya hukunta yarinyarnan yau. Nikuwa jikina rawa yakamayi saboda matsanancin tsoro da razana,wlh bansan ya’akayi ludayin ya subce daga hannunaba.batare dana bari na kallesaba,na tsugunna akasa akan gwiwata idona tab da kwalla na fara magna. “Dan Allah Dan annabi,kayi hakuri wlh bansanib”…. “Shut up!” Yadakamun wata uwar tsawa,wadda najita har tsakiyar kaina,hawayen dake makale a idonane yafara zuba,akan fuskata jikina yacigaba da rawa tamkar mazari. Kallonta kawai yakeyi,gata yarinya karama amma se shegen rashin jin tsiya,ga dan banzan tsoro. Inajin yanda idanuwamsa suke yawo ajikina,amma nakasa dago kaina na kallesa. Mikewa yayi bekaracemun komaiba,ajiyar zuciya na sauke,ina bin bayansa da kallo. Tashi nayi, nafara goge inda na zubar da romon,amma fa bandena kukaba. Yayi kusan 5 minutes sannan ya fito sanye da wasu kayan ajikinsa,hannunsa dauke da rigar dana bata masa.dafe kansa yayi aransa yace. “Ko a ina mommy ta samo wannan yarinyar, ita kam Sam kuka baya mata wahala,yanzu meyamata datake ta kuka,yana zaman zamansa zatasa masa ciwon kai. Ina rakubu tamkar almajira naji ya cillomun rigartasa a jikina, yayi hanyar fita batare dayace mun komaiba. Fahimtar danayi fita zeyi kuma ko break din beyiba, senaji ba dadi saboda nice sanadiyyar hakan. Cikin marairaicewa nace masa. “Dan Allah karka fita bakaci abincinnanba,idan ka tafi haka bazanji dadiba wlh.” ni kaina seda na furta hakan naji wani iri. Kamar daga sama yaji muryarta tana rokonsa,tsayawa yayi cak, zuciyarsa na masa kuna shifa bayason mutum me yawan takura, dolene yasanar da mommy karta kara aiko masa yarinyarnan. Juyowa yayi karaf muka hada ido,da sauri nayi kasa da nawa idon saboda wata uwar harara daya wurgomun. Ahankali ya fara takowa zuwa dinning din,da hannu ya nunamun kofa alamun na fice masa. Sum_sum nafara tafiya rungume da rigarsa,duk da befadamunba amma nagane nufinsa na wanke masa. A falon kasa na tsaya ina maida numfashi,tare da daidaita nutsuwata. Saboda ina fita a haka kallo daya mutum zemun yagano zallar firgici da tsoro a tattare dani. Ninke rigarsa nayi wadda sassanyan kamshinta ya mamaye ni,a hijab dina na boyeta na nufi hanyar fita daga part dinnasa……..

Kamar amafarki na hangi baaba talatu da’alamun fita zatayi saboda naga ta nufi get din tsakiya.wani sanyi naji araina, tafiya na farayi cikin sauri_sauri saboda na cimmata. “Baaba talatu” nakira sunanta bayan na matso kusa da ita. Juyowa tayi itama cikin mamaki tace, “maryam!” “Na’am baaba talatu ina kwana, kamo hannuna tayi batare data amsamun gaisuwataba,fara’a fal fuskarta. Tace, “maryam dake nake kwana nake tashi araina,kullum,inaso naganki amma badama.” “Baaba to meyasa yanzu kikadena zuwa part din hajiya,nima inason ganinki amma bansan inda zansamekiba. “Hmmm,maryam,kenan ai se hajiya ta kiramu muke da damar shiga part dinta,amma ke kina da ikon dazaki iya fitowa kije ko’ina agidannan, kinga wancan dan karamin part din idan kika wuce na hajiya,to nanne part dinmu na yan’aiki idan kikazo zaki ganni.” “Kai amma naji dadin ganinki baaba,insha Allah idannagama aikina zanzo anjima,nifa nayi tunanin ma bakya gidannan.” Murmushi baaba talatu tayi tace, “banda abunki maryam,ina zani ai nanne gurin Neman abincina,yanzudai sauri nakeyi zanje dubiya, wata yar garinmuce datayi aure anan jiya tayi bari,shine zanje na dubota banason a shiga masallaci bandawoba. “Toh,shikenan baaba,sekin dawo,ki mata sannu,Allah yakiyaye.” “Ameen maryam sena dawo” part dinmu nanufa zuciyata cike da murnar ganin baaba talatu dama akwai tambayoyin danakeson nayi mata.

Mommy bata falo,may be tana dakin ta. abunda yake kara dauremun kai da gidannan tunda nazo banga bako ko daya yazoba,kodayake bandade da zuwaba kila shiyasaka. Dakina nashiga na’ajiye masa rigarsa acikin cover da nufin idannaga aikin dazanyi sena wanke masa. Kitchen na shiga, kuku na tarar yana kokarin Dora lunch tun yanzu,dariya nayi masa nace, “kai emeka tun yanzu zaka Dora girki?” Cikin hausarsa yacemun madam karamace tasakashi aiki kafin ta fita. Jinjina kaina nayi,dannagane aunty suhailat yake nufi. Tsayawa nayi ina karewa kitchen din kallo narasama wanne kalan drinks zan hada, na iya drinks kala_kala,tunda shine sana’ar innata. amma bansaniba koze musu dadi. Yanke shawara nayi bari kawai na mata zobo,da kunun aya da lemon kwakwa. tunda na kware wajen yinsu,dan da azumi munayi a gidan umma nida saleemat. Cikin freezer na duba,naga akwai duk abunda zan bukata. Sedai banga aya da zobo ba a kitchen din,amma naga kwakwa da dabino da madara da sugar, dasu flavour. Tambayar emeka nayi amma yakasa gane me nake nufi, dole se dakin hajiya na shiga na tambayeta. Tacemun inje kitchen injirata zata saka akawomun,godiya na mata na koma kitchen na fara gogo kwakwar da zanyi lemo da ita. Mintuna kadan wata mata ta kawomun aya da zobon dayawa, wanke ayar nayi na jikata…… ( typing da wahala danayi muku yanda tayi lemon,da kunun ayar.)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button