Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

By
zeey kumurya
ABIN DA KA SHUKA….!

8️⃣0️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………Cikin tsananin kad’uwa Mommy ta bisu da kallo kirjinta na mahaukacin bugu, gaba-d’aya ma ta manta tuk’i take a tsakiyar babban titi, gani take tamkar mafarki take zata farka ba Mustapha’n ta gani ba, mutumin da take nemansa ruwa a jallo, horn d’in da ake ta danna mata ya dawo da ita cikin nutsuwarta, tuk’i tacigaba dayi slowly tana waigen su Mustapha, ganin anbasu hannu sunyi gaba yasata juya motarta da sauri a ƙoƙarin ta na zagayowa ta bi bayansu, wata Babbar Mota ce ta danno kai, tunda titin yana tafiya ne a hannu ɗaya, Motar baisan da motar Mommy ba, tunda yasan yuturn akeyi idan mutum zai zagayo, a guje ya taho hakan yasashi yin ciki da motar Mommy tayi tsalle ta jirkice a tsakiyar titi.

Mai motar bai tsayaba yayi gaba abinsa da mugun gudu, tsayawa mutane suka fara yi na cikin Mota suka fara fiffitowa da tsirarun masu tafiya a ƙafa, aka fara ƙoƙarin ceto ran Mommy, sai da aka ɗaga motar sannan aka samu aka zaro ta cikin mawuyacin hali, jini na zuba a jikinta, wani bawan Allah ne yayi shahada yace a sata a motarsa, aka nufi Asibin Nasarawa da ita.

Sai da suka biya ta super market suka yiwa su ammi tsara ba sannan suka koma gidan Daddy, anayin sallah azhar Mustapha yace su tafi, Maryam bata soba tayiwa Aunty sallama suka tafi, Daddy kuwa sai da ya rakasu har airport. Suhailat bata samu bacci ba a daren jiya, sai da garin Allah ya waye baccin yayi gaba da ita, har su Maryam suka tafi bata tashi ba, Aunty tanata buga mata kofa tun safe ko dan ta tashi ta karya amma taƙi tashi, sai bayan tafiyarsu Mustapha ba jimawa tatashi, Aunty tana daki tana waya da Abban su Aliya, Suhailat ta shiga ta sameta, zama tayi ta jira Aunty’n ta gama wayar, Aunty ta dubeta fuskarta babu walwala sam tace “Sai yanzu kika ga damar tashi?” Suhailat tace “Banyi bacci bane jiya, sai da safe na samu ya ɗaukeni” Aunty tace “meya hanaki baccin?” Suhailat tayi shiru, Aunty ta tab’e baki tace “kije kiyi ta sa damuwa aranki, tun kina yar ƙaramarki kijawa kanki wani ciwon” Suhailat tana hawaye tace “Aunty wlh inason yaya sosai, kuma kun sani, amma shi naga yanzu ya dena sona baya tani, ko nemanama bayayi” Aunty tace “amma tun kwanaki da kika damu danki kika ƙi ci kika ƙi sha nace miki kibar wata maganar yaya sai Allah ya saukeki lafiya ko?” Suhailat tace “Aunty wlh bazan iya ba, ni kaɗai nasan yanda nake ji a raina, dan Allah ki rokeshi ya dawo mu cigaba da rayuwar mu kamar da” ta ƙarashe zancen tana fashewa da kuka. Aunty tayi shiru cikin jin tausayinta, tana ji a ranta da zata iya da tasa Mustapha ya aure ta, amma tasan idan tayi haka tayi rashin adalci, dan Suhailat sam bata dace da kamilin namiji irin Mustapha ba, sai dai idan shi ya furta yana sonta da kansa. Aunty ta dubeta da kyau tace “Suhailat Muhammad ɗin da kika sani yanzu ba na da bane, yanzu rayuwarsa ta canza zaiyi wuya ya iya auranki, musamman idan yasan abinda kika aikata” Suhailat ta d’ago da sauri tana kallon Aunty tace “Aunty bangane rayuwarsa ta sauya ba, kuma dama baisan ina da ciki ba? to Meyasa yakemun haka? Ko akan abunda Mommy ta masa ne?” Aunty tace “ko ɗaya ba akan abinda Aunty Atika ta masa bane, Mustapha yanzu yana rayuwa ne cikin nutsuwar da kwanciyar hankalin da ya rasa a da, Muhammad yayi gamo da mahaifiyarsa, kuma da ita yake rayuwa a Jos sannan kuma a halin yanzu yana da mata wato Maryama dan haka…..” mikewa tsaye Suhailat tayi Zuciyarta na wani irin bugu, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kamar an jona mata shocking, so take tayi magana amma ta kasa, wata ƙara ta kwalla tare da zubewa ƙasa a suma, Aunty dake kallonta tayi kanta cikin tashin hankali tana kiran sunanta tare da jijjigata, Fahimtar da tayi suma tayi yasata tashi ta ɗauko ruwa mai sanyi a cikin fridge ta shiga shafa mata a fuska zuwa wuyanta, Suhailat taja wani dogon numfashi tare da buɗe idonta da suka matuƙar yi mata nauyi a hankali ta saukesu akan Aunty, Aunty cike da tsananin tausayawa tace “sannu Suhailat” Suhailat ta fashe da wani irin kuka hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata, cikin kukan tace “Aunty dan Allah dagaske kike yaya yayi aure da waccan yarinyar?” Aunty tace “Ehh, Suhailat idan zan baki shawara ki ɗauka ki cire Muhammad daga ranki tun wuri, dan yanzu ba take yake ba” Suhailat ta yunkura ta tashi zaune numfashinta na fita da kyar tace “Aunty bazan iyaba, wlh bazan iya jurar rashinsa ba a rayuwata, komai zai faru sai dai ya faru amma wlh sai na aureshi, aida yana sona sai dai in shiga tsakaninmu a kai, a yau ba a gobe ba sai na bishi har Jos ɗin” Aunty data saki baki tana kallonta tace “Tun farko Suhailat ke kika cushi kanki, da’ace baki ɓata rayuwarki da yawon banza ba, dana san tabbas Mustapha ke ze aura” Suhailat bata bi takan maganganun Aunty ba ta cigaba da maganganunta na hauka cikin ihu kamar zautacciya, Aunty ta shi zata fita ganin abunnata harda iskanci, kafin ta kai ga fita faruq ya shigo a gigice yana faɗin “Aunty! Aunty!’ a dan ruɗe Aunty tace “lafiya faruq kake mun wannan kiran, ko wani abu ne ya samu Sadiq ɗin?” Faruq cikin tashin hankali yace “yanzu wani freind ɗina likita a Nasarawa hospital ya kirani, wai an kawo Mommy sunyi accident kuma tana cikin mummunan hali” Aunty tace “Subhanallah dama Aunty Atikan tana ƙasar nanne?” Yace “ban sani ba Aunty, dannima tunda tabar gidannan rabona da ita” Aunty ta dafe kanta tana kiran “innalillahi…” Suhailat ma shiru tayi tana sauraren faruq, Aunty ta dubeshi tace “kaje asibitin yanzu da sauri, ni zan zauna gurin Sadiq kafin yaya ya dawo, sai mu taho asibitin muma, ka kira su Haidar ka sanar musu” ya amsa da toh sannan ya fice, Aunty tabi bayanshi zuwa part din Daddy domin kula da Sadiq zuciyarta cike da jimanta accident din Mommy, suka bar Suhailat nan zaune zuciyarta na mata wani irin zafi da k’una, yanda takeji a ranta a yanzu idan tayi arba da Maryam zata iya kasheta, ko kaɗan labarin accident d’in Mommy bai wani daga mata hankali ba, ita damuwarta kawai akan Mustapha ne. Aunty tana zaune a falon Daddy cikin damuwa Daddy’n ya dawo, miƙewa Aunty tayi fuskarta na nuna tsantsar damuwa tace “yaya kaji wai Aunty Atika tayi accident” Daddy cikin rashin damuwa yace “when” Aunty tace “yanzu faruq ke faɗamun yama tafi asibitin” Daddy yace “Allah ya sawwake ya kiyaye gaba” yana ƙoƙarin hayewa sama Aunty ta tsaidashi da faɗin “haba yaya, yanaga kana ƙoƙarin shigewa, kamata yayi ai ka tafi asibitin kaima, amma naga ko damuwarka baka nuna ba” Daddy yace “damuwar me kuma zan nuna akan macen data zama silar sanyani cikin tashin hankali, macen da babu Alkhairi kwata_kwata a tattare da ita sai sharri, macen da…” “Haba yaya, abinda ya faru ya riga daya wuce, kome tayi dan kanta, aiko ƴaƴanta da suka gujeta ya isheta ishara, kai kuma ko dan darajar ƴaƴan dake tsakanin ku kaje ka dubata, dan faruq bakaga yanda hankalinshi ya tashi ba, kuma kasan da yafi kowa jin takaicin abinda ta aikata yafi kowa yin burus da ita, amma dake uwa uwa ce yanajin tayi hatsari hankalinshi ya tashi bakaga ba, a gigice yazo ya faɗamun” Daddy ya sauke nannauyen numfashi yace “shikenan bari naje driver ya kaini” Aunty tace “ko kaifa, Allah ya kiyaye sai munyi waya naji jikinnata, nima inna gama abunda nake zanzo asibitin” Daddy ya amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, Aunty kuma ta shiga kitchen ta fara kiciniyar dafa abinci. Mun sauka lafiya a garin Jos, Part ɗinmu muka wuce direct muka ajiye kayanmu, kwanciya nayi akan gadon ɗakinsa ina maida numfashi, ya dubeni yace “taso muje part ɗin Ammi” na daure na tashi ba dan nasoba saboda naji daɗin kwanciyar, ya kama hannuna muka fita, muna tafiya nace masa “kuma yaya bamu biya ta kadunan ba” yace “to ba Aunty’n tana Kano ba” nace “hakane fa” ammi ta tarbemu cikin tsananin murna da farin ciki, muna munyi murnar ganinta dan munyi kewarta ba kaɗan ba, abinci kala_kala ta mana na tarbarmu, bayan mun gama cin abincin yaya ya fita ni kuma na zauna muna shan hira dasu ammi da Aunty zuhura, sai dare na koma part ɗinmu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button